Page 49- Court

Comincia dall'inizio
                                    

Daga haka na juya cike da takaicin maganganunsa.
Can sai ga masu laifin sun shigo, suka nemi wurin zama suka zauna su duka hudun. Na waiwaya na dubi Hannatu da bakidaya tsoro ya bayyana a saman fuskarta, ta kwanta a kan kafadar mahaifiyarta.

Shigowar alkali ce ya sanya kowa ya mike bisa dokar kotu, har sai da ya zauna sannan kowa ma ya zauna.
Registrer ya fara gabatar da kara, kafin Alkali ya dubi inda muke jere ya ce,
"Lauya mai kara, you can proceed."
Mikewa na yi na ce
"My Lord!"
Hade da matsawa kusa.
"Zan so kotu ta ba ni dama domin gabatar da victim dita, akwai tambayoyin da nake son yi mata."
Alkali ya jinjina kai,
"Kotu ta ba ki dama."
Na dubi inda Hannatu take, na ce,
"Hannatu Abdulkadir."

Cikin rashin kuzari ta tako, hawaye na wanke fuskarta ta iso. Witnessbox na gwada mata, sannan aka sanya ta rantsuwa a kan za ta fadi gaskiya.

Na matsa daf da ita na ce,
"Hannatu, zan so ki gabatar wa kotu kanki, da kuma abin da ya faru da ke ranar ashirin ga watan tara, shekara ta dubu biyu da ashirin da uku."
Jikinta ne ya fara rawa, ta fara kokarin yin magana amma sai kuka,
"Na san akwai zafi da ciwo Hannatu, amma ina so ki jure ki yi wa kotu bayani."
Ta daga kanta, cikin sanyin murya  ta ce,
"Sunana Hannatu Abdulkadir. Ranar ne daga makaranta..."
Cikin kuka ta maimaita wa kotu duk abubuwan da ta fada min ranar da na tambaye ta.
"Wancan, shi ne ya fara. Daga nan sai wancan ya karba..."
Ta dinga nuna su da hannu tana kuka.

Alkali ya yi gyaran murya ya ce,
"Kafin kotu ta ba Hannatu izinin komawa ta zauna, ko lauya mai kare wadanda ake kara yana da tambayar da zai yi mata?"

Barrista Rafiq ya mike, cikin girmamawa ya amsa da
"Ina da ita ya mai shari'a."
Sannan ya koma kusa da ita ya ce,
"Hannatu, ki nutsu. Shi mai gaskiya ai bai da haufin komai. Idan har kin san ba kirkirar zancen kika yi ba mene ne zai tsorata ki?"

"Objection my lord! Barrister Rafiq yana kokarin karyata Hannatu a kan gaskiyarta. Bayan kuma kowa ya san duk inda raped victims suke ba a rasa su da shiga tashin hankali. Wannan dalilin ne ya sanya take rawar jiki ba wani abu ba."

Alkali ya dubi barrister Rafiq ya ce
"Objection sustained. Barrister Rafiq a kiyaye."
Ya dan rusuna, sannan ya ci gaba,
"Ke da ke cikin wani hali, ta yaya har kika iya gane wannan ya yi ya ba wannan Hannatu?"

Shiru ta yi in ban da sautin kukanta babu abin da yake fita.
"Tambaya ta biyu, my lord, ta yaya wadanda suka san ta ta san su za su yarda su yi mata wannan aika-aikar kuma su gudu bayan sun san za ta iya tona musu asiri?"
Ya dubi Hannatu, ya ci gaba
"Kina tunanin hakan mai yiwuwa ne?"

Cikin takaici na mike na ce
"Objection my lord! A cikin bayanan Hannatu, mun ji inda ta ambaci sun ce kashe ta za su yi, shi ne sai suka zabi hanyar da za su ji dadi kafin kasheta din. Sannan ba su gama aiwatar da aikinsu ba Allah Ya jeho wasu kauyawa, wadanda dalilin ganin su ne ya sanya su guduwa ba tare da sun kammala aikin nasu ba."

Alkali ya jinjina kai.
"Ta riga ta bayar da wannan labarin, Barrista Rafiq. Babu amfanin maimaita abin da aka riga aka fade shi."
Ya dan rusuna,
"Iyakar tambayar kenan ya mai shari'a."
Alkali ya ce
"Kina da damar komawa ki zauna, har zuwa sadda kotu za ta iya bukatar sake ganin ki."

A hankali ta taka ta nufi wurin zaman ta.

Na sake mikewa, cikin girmamawa na ce,
"My lord, zan so kotu ta ba ni dama domin gabatar da shaidata ta farko."

Ya dago kansa ya ce
"Kotu ta ba ki dama."

Na koma kan kujerata na dauko medical reports dinta har guda biyu, da na asibitin farko, da kuma na SARC division.
"Ya mai girma mai shari'a, wannan su ne results din Hannatu na asibiti, wanda ke bayar da tabbacin fyaden da aka yi mata. Wannan na farkon na asibitin da aka fara kai ta ne, sannan sai wannan, na SARC Division ne. Ina fatan za su gamsar da kotu."

Registrer ne ya karba, ya karanta a bayyane har da tulin raunukan da aka samu a jikinta, da kuma dinkin da aka yi mata har zuwa dawo da ita asibitinmu.

"My lord, ina fatan wadannan takardun za su gamsar da kotu bisa ga haike wa Hannatu Abdulkadir da aka yi."

Barrister Rafiq ya mike, ya ce,
"My lord, don Barrister UmmulKhairi ta gabatar da takardun raping victim dinta da aka yi hakan doesn't mean clients dina ne suka aikata, don duk a jikin takardun babu inda suka bayyana ga wanda ya yi wannan aiki. Ina fatan kotu za ta yi watsi da wannan hujjar tata wacce ba ta da tushe ballantana makama."

Alkali ya dan shafi fuskarsa, hade da duba na ya ce
"Kotu za ta so ki gabatar mata da hujjarki, tare da dalilin da ya sanya kuke zargin clients din barrister Rafiq a kan cewa su ne suka haike wa Hannatu Abdulkadir."

Wani irin gumi ne na ji yana tsattsafo min. Na sauke gajerar ajiyar zuciya hade da fadin,
"Zan so wannan kotu mai adalci da ta daga wannan shari'a zuwa wani lokacin, ina fatan kafin nan zan tattaro duk wasu hujjoji wadanda za su gamsar da kotu. Sannan ina rokon wannan kotu da ta ci gaba da rikon su Saminu har zuwa lokacin da gaskiya za ta yi halinta."

Barrista Rafiq ya mike,
"My lord, har yanzu babu wata hujja da ta nunar da clients dina su suka haike wa Hannatu. Ina fatan wannan kotu mai adalci za ta watsar da rokon da Barrista UmmulKhairi ta yi, a sake su don ba su da laifi ko kwara guda."

Alkali ya yi guntun rubutu, sannan ya dago fuskarsa ya ce,
"Idan har babu mai shari'a cikinku nan da sati biyu, za mu daga shari'ar zuwa wannan lokacin."

A lokaci guda duk muka amsa da babu. Ya ce,
"Kotu ta daga wannan shari'a zuwa nan da sati biyu masu zuwa. Sannan ba za a rike wadanda ake zargi da laifin ba kamar yadda Barrista UmmulKhairi ta nema."
Ya buga guduma hade da mikewa bayan ya furta
"Kotu!"
Ya fice.




Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUDove le storie prendono vita. Scoprilo ora