Muka ci gaba da hirarmu ta masoya. Jin jikina babu dadi ne ya sanya na ce bari in watsa ruwa zan kira shi.

***

Tamkar wata daya haka shekara guda ta zagayo, na kammala da Law School dina. A tsayin lokacin nan Haidar ya yi zuwan da ko ni ban san adadinsa ba. A wasu lokutan shi da Ummu da Afreen, Kuluwa, sai kuma Sadiya, haka suke zuwa. Wani lokacin kuwa shi kadai zai zo, ya yi kwana daya ko biyu sannan ya juya ya tafi. Duk sadda zai zo hotel din da ya sauka nake tafiya in kwana a can. Idan tare da su Ummu ya zo kuwa haka muke rabuwa da su suna kuka, musamman ma Ummun da ta yi wayo, ita Afreen saukin rarrashi gare ta, kuma ba ta wani mugun sanin zak'in uwa ba kamar yadda ita Ummu ta sani.

Ranar da na koma, cike na tarar da gidanmu. Yan'uwa duk an zo tarba ta sai murna ake yi. Ummu da Afreen gayu aka ci musu cikin hadaddun dogayen riguna da alama domin wannan ranar kawai Daddynsu ya saya musu.
Gida ya sha gyara, an canja min sababbin kujeru da dining table.

Sai da na yi kwana biyu ina baccin gajiya kafin na wartsake, muka fara nuna wa juna kewar junanmu da muka yi, ni da Haidar. A kwana na uku sai ga dalleliyar mota kirar venza ya canja min. Murna a wurina ba a magana. Da ita na dinga yawata gidajen dangi ina gaishe su saboda jimawar da na yi ba na nan. Afreen tunda na dawo kullum sai ta yi kukan dare saboda rashin sabo. Da kyar dai na shawo kanta ta fara sabawa da ni har ta daina kukan daren.

Bayan sati hudu aka yi posting dinmu NYSC, Allah Ya taimaka na cika married certificate aka bar ni a nan cikin Katsina. Don haka sai lamarin ya yi min dadi don ko camping ma ban yi ba sai da aka gama sannan na fara zuwa wurin bautar Kasata.

Ko da Haidar ya ce min zai sa Ummu makaranta cewa na yi kawai ya hada ya sanya su, a lokacin farkon fara Law School dina ne, sai ita Afreen aka ajiye ta crèche. Shi ya sa a yanzu da na dawo ba ni da haufin tafiya wurin aikina don ta riga ta saba da zuwa makaranta. Sai idan na tashi nake biyawa in dauke su saboda karfe sha biyu kullum nake gamawa.

Wani alwashi da na dauka wanda ko Haidar ban fada wa ba shi ne; zan yi aiki da Human Rights, ba don komai ba sai don raped victims. Su nake son dinga kwato wa fansa gwargwadon iyawa ta.

Na fara duk wani kokarina wajen tinkarar Haidar da batun, duk da na san zai yi wuya ya musa min musamman da ya san ra'ayina ne shige wa raped victims a gaba.

Ranar da muka kammala bautar kasa na tinkare shi da zancen. Ya nuna farincikinsa sosai ya kuma aminta.
"Sai dai ina jiye miki tsoro Baby girl, wallahi rayuwar nan ta zama abin da ta zama, mutane ba sa son gaskiya sam, ba wuya ki ga an illata mutum, daga kokarin bayyanar da gaskiya."
Ya dan yi jim, sannan ya ci gaba da cewa,
"Ko kuma yadda kike da raunin nan, abu kadan zai iya rikita min ke."

Na saki murmushi ina shafar lallausar kasumbarsa,
"Ai ba ka sani ba Daddy, tun da na yi aiki a DSS zuciyata ta zama mai karfi. Ba na jin akwai wani tashin hankalin da zai karya min zuciya."
Ya harare ni yana murmushin shi ma, ya ce,
"Ke din nan da abu kadan kin zubar da hawaye shi ne kike wannan batun? Allah dai Ya kyauta kawai."
"Amin."
Na ce ina kokarin mikewa. Ya sanya hannu ya dawo da ni.
"Allah ba ki isa ba Buttercup. Zo nan ki ba ni tukuicin kammala NYSC. Kin san dai ni ne na farko da na taya ki murna ai ko? To dole a ba ni wani abu..."
Tun bai rufe baki ba na hada bakina da na shi.

***

BAYAN WANI LOKACI.

A cikin ministry of justice, a karkashin  Sexual Assault Referral Centre (SARC), jere lauyoyin da ke bi wa raped victims hakkinsu suke, daga ciki har da ni, watana biyu kenan da na fara aiki, inda na yi shari'a guda biyu. Daya na yi nasara, inda dayar kuma ban samu nasara ba saboda rashin karfafan hujjoji.

Telephone din cikin Office din ne ya yi kara, Barrister Fa'iz ya dauka. Ya dan yi magana sannan ya miko min.
Wanda ke kan telephone din ya ce,
"Barrister UmmulKhairi, akwai wani file da ya iso wurina yanzun nan, case din ya yi tsanani gaskiya, idan kina da ra'ayi, na san ki da tausayi; sai ki zo ki duba."
"Okay Sir."
Na furta cikin sanyin murya. Na ajiye telephone din hade da mikewa na nufi office din na babban lauyan da ke kula da division din, Barrister Nuruddeen.

Ina isa ya miko min file din, ya ce,
"Duba ki gani. Aikin lada ne. Idan za ki iya sai ki samu mataimaki."
Na karba din na fara dubawa. Hannatu Abdulkadir sunan raped victim din. Shekararta goma sha takwas da haihuwa. An yi raping dinta ne a dajin da ke hanyar Polytechnic bayan ta tashi daga makaranta za ta dawo gida.

Dafe kaina na yi cike da alhini ina karantawa. Da na gama na rufe file din, na dubi Barrister Nuru na ce,
"Sir, zan yi in shaa Allah."
Ya saki murmushi hade da fadin,
"I know you can do it. So please try your best, tunda akwai suspects, ki bi mata hakkinta."
Na jinjina kai ina sake duba address da lambar wayar da ke jikin file din wanda za a samu victim din da su.

"You can go with the file. Ki samu ko Barrister Fa'iz ya taimaka miki. A yi duk abin da ya dace, in shaa Allahu nasara tana tare da ku."
"In shaa Allah."
Na maimaita hade da tafiya.

Ko da na ba Barrister Fa'iz file din ya duba, babu tababa ya ce zai taya ni mu yi aikin tare, na ji dadi sosai, muka kuma yanke shawarar daga an tashi aiki kai tsaye gidan su yarinyar za mu tafi.

Muna cikin tattauna maganar ne wayata ta yi kara, cikin shauki na dauki wayar.
"Daddy, good afternoon."
Na fadi da farincikin jin muryarsa.
"Afternoon my Baby girl. Yaya aikin?"
"Alhamdulillahi. Ga shi nan muna ta fama."

Cikin sautin alhini ya ce,
"Wai kin san wani abu? Shekaranjiya ba na fada miki na kai Mami gidan Anti Khadija dubiya ba sai muka tarar wai an tafi asibiti da yarinyar sai Anti Khadijan kawai muka tarar?
Na amsa da
"E haka ka ce.  Jiya kuma da kuka je asibiti ba ku samu ganin Hannatun ba wai likita ne a dakin ko?"
Ya amsa kai tsaye,
"Wai ashe boye-boyen nan da Anti Khadija ke ta faman yi, raping din Hannatun ne aka yi."
Ido bude nake maimaita innalillahi. Na dafe kaina ina tuna halin kirkin Hannatu, da kuma yadda mace ke ji a lokacin da aka haike mata.




Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now