Ina isa dakin Haidar ya mika wa Safra ita, shi kuma ya yo wurina.
"Baby girl..."
Ya furta a hankali, idanuwansa a cikin nawa.
Kafin ya ci gaba da magana Safra ta mika masa yarinyar, su kuma suka fita hade da tura mana kofar.
Ya sumbaci yarinyar cike da soyayya a idanuwansa, sannan ya sake duba na ya ce
"Sannu da kokari kin ji. Allah Ya yi miki albarka."
"Amin baby boy. Tare da kai."
Muka rungume juna tare da yarinyar a tsakiyar mu.

Bayan ya sake ni, ya miko min ita sai wawure-wawure take,
"Da alama da yunwa ta fito fa yarinyar nan. Tun da aka kawo ta take laluben hannu."
Ya fadi yana dariya.
"Na yi surprising dinki fa. Na yi mata huduba da UMMULKHAIRI, ba wai don ke mahaifiyarta ba, na saka mata hakan ne saboda Mamanta marigayiya Ummu. Ina fatan hakan zai faranta ranki, za ki ji cewa na yi miki gwaninta kamar yadda nake buri kodayaushe."

Shigewa na yi cikin jikinsa, wani irin mayafin farinciki na lullube ni. Tabbas Haidar ya faranta raina, ya yi min abin da ba zan taba manta shi ba har duniya ta nade. Na dade ina mafarkin yi wa Ummu takwara, sai dai ganin mahaifiyarsa ta dauki soyayyar duk duniya ta dora a kan wannan cikin nawa, ya sanya na cire rai, a tunanina Radiya zai saka sunan Mamin, sai ga shi ya shayar da ni mamaki, ya cika min burina duk da ban taba furta hakan a wurinsa ba.

Rasa ma kalaman gode masa na yi, sai wani irin girmansa da na kara gani a cikin zuciyata, na kalle shi ina jin saukar hawaye,
"Na gode, na gode sosai Sweat heart. Allah Ya saka maka da alkhairi, Ya raya mana UmmulKhairi. Allah Ya sa ta yi halayen kwarai na takwararta."

Jin an kwankwasa kofar ya sanya na janye jikina daga nashi.
Mami ce a gaba sai Umma da Sadiya biye da su. Dukkaninsu fuskokinsu dauke suke da annuri. Mami ta fara karbar diyar ta duba ta hade da yi mata addu'a, sannan ta mika ta ga Umma.

"An yi mata huduba da UmmulKhairi."
Haidar ya fadi hade da mikewa ya fita daga dakin bayan ya amsa addu'ar da su Mami ke ma yarinyar. Yana fita sai ga Safra da Nusaiba ma sun shigo. Shi kenan sai dakin ya dauki harama, aka dinga daukar ta hotuna.
Mami ta miko ta gare ni ta ce,
"Ungo wannan 'yar acici ce, in ban da wawurar mutane ba abin da take yi. Maza ba ta ta sha ko za a dace da ruwan nono a kusa.
Cike da kunya na karbe ta amma na kasa yi mata komai. Fahimtar kunyar da nake ji ya sanya Mamin mikewa ta ce
"Bari in zauna a waje Maman Safra. Nan din mun yi yawa."
Ta fice. Umma da kanta ta zaro nonon ta manna shi ga bakin Little Ummu, aikuwa sai ta cafke shi. Duk suka dauki dariya yayin da Umma ke maimaita abin da Mami ta ce wai da yunwa ta zo duniya.

Kwana biyu muka yi aka sallame mu daga asibitin, mun ga soyayya daga masoya, mutane, wasu ma ban san su ba dangin su Haidar ne, sannan an ci sa'a har dagin Babanmu ma wasu sun zo. Haka bayan mun dawo gida ma aka dinga dafifin zuwa ganin UmmulKhairi.
Mama ba karamin dadi ta ji ba da aka shaida mata Ummu na yi wa takwara. Wadanda suka san mu da ita suka kara jinjina wa girman amincinmu.

Ranar suna taro na musamman aka yi, har da su decoration na baloon irin wanda ake yayi hade da hoton babyn ta yi kyau sosai.
A farfajiyar gidana aka yi komai, da maghriba duk aka watse aka bar mu da tarin gajiya.
Haidar baki har kunne, shi ma din har walima ya yi shi da abokai da 'yan'uwansa. Sannan an sha hotuna ma.

Ko da dare ya yi akwai gajiya, Ummu ta dinga kuka sai da aka ba ta panda sannan muka samu ta yi bacci.
Da Haidar ya shigo yana tambayar ba'asin kukanta, na ce,
"Rigima ce fa kawai wallahi."
Ya harare ni bayan ya zauna, ya kalle ta cikin net dinta tana ta baccinta hankali kwance, ya ce,
"Ba wata rigima fa, kun tashi kun tara mata gajiya, waccan ta dauka ta ba waccan ba dole yarinya ta sha kuka ba."
Na tabe baki na ce
"Ba wani fa, kukan banza ne da ita. Kai don ba kai ke kwana da ita ba shi ya sa har yanzu ba ka yarda tana kukan banza ba. Da rana ne kake ganin ta ta sha bacci sai dare ya yi ta ce sam ba ta san wannan ba."
Na kama hannunsa na rike, na dan saukar da murya na ce,
"Baby boy ya zancen tafiya gidan gobe?"
Nan take ya daure fuska hade da mikewa tsaye.
"Babu ita."
Ya fada hade da juyawa zai tafi. Na yi saurin mikewa na kamo hannunsa na shige cikin jikinsa. Sai da na ba shi kyakkyawar sumba sannan na ce
"Please baby boy, Daddyn UmmulKhairi kuma mijin UmmulKhairi, ka taimaka ka bari mu tafi. Wallahi idan ma ka ce ba sai mun cika kwana arba'in din ba na yarda sai mu dawo. I can't face Umma in ce mata wai ka hana ni komawa wanka. Please my darling husband."
Ya saki murmushi,
"Wannan dai dadin baki ne kawai. Na ji, na yarda. Amma duk ranar da na ji sha'awar matata dole ne ki dawo."
"Na amince wallahi."
Na ba shi amsa ni ma ina murmushin.
"Shi kenan. Kuma kullum sai kin gan ni na zo ganin babies dina, uwa da 'ya."
Nan ma dai cewa na yi na yarda, sannan ya tafi.

Tun da sassafe muka hau harhada kayan tafiya gida wanka, da taimakon Nusaiba na hada komai. Ana gama aikin suyar nama, rabawa kawai aka yi muka wuce gida. Har a cikin mota Haidar cewa yake shi dai wallahi ba ya son tafiyar nan, wai haka kawai a raba shi da 'yarshi bayan ko guminsa ba ta sani ba. Ni dai kawai nake ba shi har muka isa gida.

Kamar yadda ya fada din kullum sai ya zo. Wani lokacin ma sau biyu ya zo safe ya zo da daddare musamman cikin weekend. Umma sosai hakan yake yi mata dadi, ta ce ai abun alfahari ne wannan, alamun mijina yana kaunata da 'yarmu kenan.
An ci sa'a ya yi hakurin har na cika arba'in. Sai da na sha gyara sosai na ciki da na waje, na yi lalle na je saloon, Anti Maryam ta jika ni da kayan mata. Kwana biyu kadai muka kara ya zo ya kwashe mu da kayanmu muka tafi.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUजहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें