Page 36- I Love You

Start from the beginning
                                    

Ina kiran Haidar ya dauka, wani abu da ya ba ni mamaki saboda duk sadda zan kira shi sai dai ya latse, ya kira ni. Amma yanzu ina kira ya dauka. Tun kafin in ce komai ya ce,
"Ga mu nan asibiti Buttercup, Nusaiba ce ba ta da lafiya yanzu Mami ta kira ta shaida min, an shiga emergency da ita."
Ta yanayin muryarsa kawai za a tsinci zallar tashin hankali a cikinta.

"Subhanallahi! Me ya same ta? Ko jiya fa mun yi waya da ita ba ta fada min ba ta da lafiya ba."
"Asthma ce ta yi attacking dinta."
Ya ba ni amsa cike da alhini.
"Allah Sarki! Allah Ya ba ta lafiya Ya sa kaffara ne. Zuwa an jima zan zo sai in duba ta. Nusaiba na da kirki sosai."
"Ba sai kin zo ba Buttercup, don ko kin zo din a yanzu ba barin ki za a yi ki gan ta ba, saboda mu ma ga mu nan a reception tsaye tun da muka kawo ta, sai dai tambayar update a kan halin da take ciki muke yi. Ko me kenan zan kira ki in shaa Allah, ko zuwa gobe ne sai in zo in dauke ki ki duba tan ko?"

Cikin damuwa na amsa masa da to, har ya yi min sallama sai kuma na ga bai kamata in kyale shi haka ba tare da na kwantar masa da hankali ba a matsayina na matarsa. Na ce
"Baby boy..."
A hankali ya amsa.
"Everything is going to be alright ka ji?"
Ya maimaita
"In shaa Allah."
"Ka kwantar da hankalinka. Za ta ji sauki, za ta ga bikinmu ni da kai, da yardar Allah."
"In shaa Allahu." Din dai ya sake maimaitawa.
"Ka yi ta ambaton Allah kana yi wa Annabi SAW kirari, kana istighfaari, tare da nema mata sauki a wurin Allah. Da izinin Allah daga nan zuwa anjima kadan za ta wartsake."

Sosai na fahimci ya ji dadin kalamaina. Sai da na ji ya dan samu nutsuwa sannan na yi masa sallama na yanke kiran.
Wata irin shakuwa ce tsakanin Haidar Turaki da 'yar'uwarsa Nusaiba Turaki, wacce ban taba ganin Yaya da kanwa sun yi irinta ba. A yadda take fada min, ko sirrinsa bai cika boye mata ba. Haka ita ma, idan sabon saurayi ko sabuwar kawa ta yi shi ne mutum na farko da zai sani. Duk wata bukata tata ba ta taba kwana da ita ba ba tare da ya cika mata ita ba, matukar dai ta fada masa. Wannan dalilin ne ya sa ni ma ta dauki soyayyar duk duniya ta dora a kaina. Take kyautata min tamkar jininmu daya. Ni ma kuma ganin hakan ya sa ta shiga raina sosai, zuciya tana son mai kyautata mata.

Jiki sabule haka na kasance har sai da Umma ta fahimta, tana tambaya ta na shaida mata Nusaiba ce ba lafiya, asthma ta tasar mata tana ma asibiti kwance. Ita kanta ta shiga alhini don Nusaiba kowa nata ne. Daga lokacin da ta fara zuwa gidanmu, zuwa yanzu ta yi zuwa ya kai biyar, kuma duk zuwan da za ta yi akwai abin da za ta riko wa Umma wai na gaisuwa ne.
Haka dai muka kwana daga ni har kannena cike da tunanin halin da take ciki. Mun yi waya da Haidar fiye da bakwai ina tambayarsa update amma sai ya ce har yanzu dai tana emergency ba a bari sun shiga ba.

Washegari da safe bayan na yi wanka, ko karyawa ban yi ba na kira Haidar na fada masa ga ni nan zuwa asibitin.
"Kin yi breakfast?"
Ya tambaye ni cikin sanyin murya. Na amsa masa da a'a sai na dawo tukunna.
"Duka-duka karfe tara da rabi yanzu Buttercup, ki samu ki nutsu ko ruwan zafi ne ki sha, in ya so ko zuwa sha biyu zan zo in dauke ki sai ki duba ta."
Ba don na so ba na amsa masa da to. Don ni kam burina in duba ta, an ce ka kula da mai kula da kai.

Sha biyu da kusan rabi ya zo. Har ciki ya shigo ya gaishe da Umma ta yi masa ya mai jiki, ya shaida mata da ta ji sauki sosai don an mayar da ita ma amenity. Umma ta ji dadi sosai ta yi mata addu'a sannan muka tafi, na so tafiya da daya daga cikin su Sadiya amma ba su nan duk suna makaranta.
Riga da skirt ne na saka na maroon din leshin da ya yi daidai da kalar farar fatata. Sannan na yafa golden din medium mayafin da ya tafi da kalar adon golden da ke jikin leshin. Mayafin bai wani kare surar jikina sosai ba, duk shape dina ya bayyana, ga kuma heel shoe da na sa wanda ya sanya tafiyata komawa tamkar 'yar wasan fashion.
Ya riga ni fitowa ya jira ni a mota, tunda na fita idonsa yake a kaina, fuskarsa daure babu annuri har na karaso na shiga motar.
Gaishe shi na yi amma sai bai amsa ba, ya ci gaba da tukinsa har zuwa sadda muka hau kan babban titi.

"Kar ki kara yafa irin wannan mayafin."
Ya furta ba tare da ya kalle ni ba, idanuwansa na saitin titi kamar ba shi ba ne ya yi maganar.
Shiru na yi ina jin wani iri don ba mu saba irin haka da shi ba, ban saba ganin sa a irin wannan yanayin ba. Sai na mayar ko saboda jikin Nusaiba ne ya sanya bai sakar min fuska ba, duk da ya sakar wa Umma sosai.

"Kin ji ni ba? Wallahi duk ranar da kika kara sanya irinsu sai kin koma kin sauya shi da dogon hijabi, ko kuma ma ki fasa fitar duka."
Sai yanzu na gane. Wato kishi ne ke dawainiya da shi ashe. Haka nan ake cewa kishi kumallon mata, Hausa ce kurum, amma kishi kumallon maza shi ya fi cancanta a fadi.

"Am sorry."
Na ce ina dukar da kaina.
"It's Okay."
Ya fadi amma bai yi min murmushin ba ballantana in sa ran zai amsa gaisuwata. Duk sai na sha jinin jikina don bai saba daure min fuska irin haka ba.




Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now