Ni dai ina jin su sai murna suke yi. Can kuma sai ga Umma ta shigo, wuri ta nema ta zauna, sannan ta dube ni da alama magana mai muhimmanci take son ta yi da ni.
Na sunkuyar da kaina da idanuwana da ke min radadin kuka. Ta ce
"Aliyu ya yi min magana yanzun a tsakar gida kafin ya fita. Ya shaida min yana son aurenki idan har ba a yi miki miji ba, ni kuma na amsa masa a kan ya nemi soyayya daga wurinki, ni dai don ta ni babu matsala. Sannan na shaida masa zan fada wa Kanin mahaifinki a waya, sai ya ba shi lokacin da zai je ya nemi izini a wurinsa tunda ni mace ce, kuma bai kamata a soka mace cikin lamarin neman aure ba."
Ta yi shiru hade da kama hannuna, sannan ta dora da
"Ban ga aibunsa ba UmmulKhairi. Tunda ke da kanki kike yabon kyawawan halayensa tun farko fara aikinki a garin nan. Sannan duk wanda zai girmama naka to babu tamkarsa. Ni dai Aliyu ya yi min dari bisa dari, amma ba zan yi miki tilas ba, sai dai zan iya ba ki shawara a matsayina na mahaifiyarki, uwar da take son farincikin diyarta. Ki tuna kaddarar da ta hau rayuwarki, ya sani amma duk da haka ya zabe ki a matsayin wadda yake son aure. Sannan ko ba komai ya taba aure, mutuwa ce ta raba shi da matarsa, kin ga ya san ciwon kansa, ina ji a jikina ba zai wulakanta ki a gaba saboda kaddararki ba."

Na saki kuka da karfi bayan na fada jikinta, na ce
"Umma ba wai shi din nake ji ba, kar a je sai na saki jiki komai lafiya kuma a samu masu goranta min daga gefe. Kin san an ce ba a mugun sarki sai mugun bafade."
Umma ta ci gaba da shafa bayana a hankali,
"Haka ne Khairi. Sai dai ki sani shi ne mai auren ba kowa ba, kuma shi din dai ne ya ce ya ji ya gani zai iya. Don haka kar ki dauki wannan a matsayin matsala. Sai dai abu daya da nake so ki kwana da saninsa shi ne; ba kowa ba ne zai kaunace ki ba daga danginsa, ba wai shi din ba ma, duk wanda za ki aura  ba za ki iya tsallake wadannan surutan daga bakin mutane ba. Dole ne sai kin toshe kunnuwanki, ki ji ki hakura, farincikin mijinki kawai kike so ba na kowa ba."

Sosai kalaman nata suka sanyaya zuciyata. Ta fahimci hakan kuwa sai ta ci gaba da amfani da kalaman da ta san za su kwantar min da hankali har sai da ta samu galaba a kaina.

***
Ina kwance dadaddare sai ga kiran sa ya shigo wayata. Kura wa wayar ido na yi ina tunanin a wanne matsayi zan dauki kiran, ya ce idan ba a Office muke ba shi ba Oga Ahmad ba ne, sunansa Aliyu Haidar Turaki. To daga Aliyun ma kuma ya koma matsayin mai neman aurena. Har yanzu zuciyata ta gaza tantance muhallin da yake. Tabbas ba na jin kiyayyarsa, haka kuma ba na jin sa can cikin zuciyata saboda dalilan nan guda biyu da na fada wa Umma. Sai dai kuma maganganunta sun shige ni; da ma ba lallai ba ne in samu karbuwa a wurin kowa, dole in yi facing different challenges na rayuwa tunda na shiga halin da ba lallai in iya ketare challenges din ba. Ita mace da ma ko babu raping ba lallai ba ne kowa ya so ta a cikin dangin miji, to ballantana kuma mace irina, wacce ta hadu da mummunan tsautsayin nan.

Har wayar ta tsinke ban dauka ba ina ta tunane-tunane, can kuma sai ga kiran nashi ya sake shigowa. Na dauka cikin sanyin murya na masa sallama, a maimakon ya amsa sai ajiyar zuciya da ya sauke, can ya nisa hade da fadin,
"A cikin dictionary dina Khairi, babu wani abu wai shi hakuri, musamman kuma hakuri irin wanda zai cutar da ni. Naci gare ni sosai. Don haka ki sa a ranki ba zan daina damun ki ba har sai sadda kika aminta da batun aurena."
"Ina wuni."
Na bude baki na gaishe shi ba tare da ba shi martanin maganar da ya yi min din ba."
"Kina lafiya?"
"Alhamdulillah."
Na ba shi amsa cikin sanyin murya.
"Ya Ummanmu take? Ina kannena kuma?"
"Duk suna lafiya alhamdulillah."
"To ma shaa Allah. Ni kullum ina tambayar ki tamu Umman amma ke ba ki taba tambaya ta tawa ba, ko?"
Dafe baki na yi ina jin kunya sosai don da gasken ban taba tambayarsa ba, sau daya ya taba yi min zancen ya ba ta labarin namijin kokarin da na yi a wurin aikina amma daga nan ban sake jin sunanta ba a bakinsa.
"Ka yi hakuri Sir..."
"Buttercup..."
Ya yi gaggawar dakatar da ni.
"Don Allah ki daina kira na da Sir din nan, ni dai har a office din ma na yafe, please ki dinga kira na da Haidar idan ma sunan soyayyar ba zai samu ba."

Bayyananniyar dariya na yi saboda yadda ya yi maganar cikin wani yanayi. Sai kuwa ya sauke ajiyar zuciya tare da sakin hamdala.
"Ba ki ji yadda dariyarkin nan ta sanyaya zuciyata ba wallahi. Dan Allah Khairi ba sai mun je da nisa ba ki aminta da ni don tuni zuciyata ta fada min kina so na, sai dai kin kasa karbar gaskiyarta ne. Kuma ni dai zuciyata ba za ta yi min karya ba tunda ba ta taba yin karyar ba. So nake gobe idan na je gaishe da Mamina weekend, in ba ta kyakkyawan albishirin na samu matar aure kamar yadda take ta min fata tun bayan rasuwar Maryam."

A daidai wannan lokacin ba zan iya ci gaba da yi masa shiru ba bayan shawarwarin da Umma ta ba ni da kuma yadda zuciyar tawa ta aminta da batun aurensa duk da ba na jin digin soyayyarsa a cikinta. Don haka sai na ce masa
"Idan ka je gidan Mami gobe ka gaishe ta, sannan ka fada mata ta shirya tarbar UmmulKhairi a matsayin matar danta Oga Haidar."
Daga nan na yanke wayar cike da kunya ina jin cewa hakan da na yi shi ne daidai, duk da ba zan fasa yi wa kaina addu'ar tabbatuwar alkhairi ba. Idan har aurena da Haidar ya kasance, na sani shi ne alkhairi gare ni. Idan kuma bai yiwu ba to babu alkhairi a ciki, saboda koyaushe cikin neman zabin alkhairi a rayuwata nake, haka mahaifiyata ma.
Allah Sarki Ummu! Sai kuma tunaninta ya zo min. Da tana raye da na tabbata a wurinta Haidar zai yi kamun kafa saboda muhimmancinta gare ni. Da tana nan da tuni ta fara batun shirye-shiryen aure tunda kullum burinmu shi ne mu ga auren junanmu bayan mun zama likitocin da muke mafarkin zama.
Amma ga shi a lokacin da na samu mijin aure babu ita, babu Ummu a duniyar ta tafi ta bar ni.
Na saki wani irin kasallallen kuka, ina jin cewa tabbas aikina bai kare ba, har sai na tabbatar da wadanda suka kashe Ummu sun shiga hannun hukuma kamar yadda na yi silar kama wadanda suka yi min fyade a hasashen su suka kashe ta.

Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now