Page 28- Next Assignment

Start from the beginning
                                    

***
Da ya iso daidai layinmu ya kira na ce ya shigo cikin layin, zan turo Sadiya ta jira shi kofar gida.
Ba a wani dauki dogon lokaci ba sai ga su sun shigo, Sadiya ta yi masa iso zuwa parlor, da ma kuwa ya sha gyara ga kamshi sai tashi yake.
Bayan an ba shi masauki, sai ga Sadiya ta zo ta fada wa Umma, ta sanya hijabi suka isa tare.

Ina daga daki ina jin shi ya gaishe ta ta amsa masa. Daga nan ya ci gaba da jinjina wa kokarina tare da nata ita kanta ta yadda har ta iya jurewa diyarta mace take aikin tsaro, sabanin iyaye da yawa wadanda suke daukar hakan a matsayin wani abu da bai dace ba.

Safra ce ta shigo ta gaishe shi ya amsa mata har da 'yar tsokana, ita kuma ta wuce ta same ni cikin dakin ina kwance da waya rike a hannuna, na raba hankalina ga latsar waya ga kuma sauraren hirar da Oga Ahmad da Umma ke yi.

Da karfi Safra ta fado jikina, cikin farinciki ta ce
"Yaya Khairi, tsakani da Allah ba karamin dace kika yi ba. Irin fa mazan nan ne masu zubin Indiyawa, wanda 'yan mata da yawa ke harin samu...kai...wannan yaya zan ga 'ya'yanku idan kuka haihu? Ke kyau shi kyau ai abun sai ya yi yawa."

Pillow na dauka na jefa mata ta yi saurin kaucewa tana dariya.
"Wai gidan uwar wa aka fada miki saurayina ne? Ina ce godiya kika ji yana yi wa Umma a kan aikina?"
Ta tabe baki bayan ta tsagaita da dariyar,
"Allah ban yarda ba son ki yake ba Yaya. Idan ka ga kare na sunsuna takalmi fa..."
Ta kasa karasawa tana dariya.
Banza na yi mata, can sai na ji Umma tana yi masa sallama ta tashi ta koma dayan dakin da yake tsakar gida.
Na ji ya ce Sadiya ta kira ni, sai ga ta kuwa ta shigo tana fada min sakonsa.

Ban san yadda aka yi ba na tsinci kaina da wata irin kunya, da kyar na iya mikewa kawai na sanya jilbaab tare da daukan wayata na tafi parlor.

Tun daga nesa yake bi na da wani irin kallo, kallon da duk ya sanya ni tsarguwa. Daga can nesa na zauna da shi tunda babu kujeru a dakin sai tafkeken carpet da ke shimfide a kan ledar tsakar dakin.
Na rusuna na gaishe shi cikin girmamawa ya amsa. Ban zauna ba har sai da ya ba ni izinin zama.

"Ba Office muke ba Khairi, a gida muke please ba na son girmamawan nan, kin sa na ji kunya."
Murmushi kawai na yi ina sadda kaina kasa.

"By the way, sunana Aliyu Haidar Turaki..."
Na daga kaina na dube shi, caraf muka hada ido na yi saurin sunkuyar da kaina.
"Yes Khairi, am not Ahmad, Ahmad yana existing ne kawai a Ofishin DSS. Amma da zarar an bar can na tashi daga Ahmad Aliyu Turaki, na dawo Aliyu Haidar Turaki, ko kuma Aliyu Turaki, a saukake kenan."

Na yi murmushi don na gane inda ya dosa, yana nufin dai abin da ke wakana a office daban, wanda kuma yake yi a wajen office daban.

"Ummanmu tana da kirki..."
Ya fadi a hankali yana kokarin sanya idanuwansa cikin nawa amma na ki ba shi dama.
"Ashe a wurinta kika gaji kyawawan halayenki."
Na ci gaba da murza zoben hannuna.
"Da nutsuwarki..."
Na dago kai na dube shi, ya saki sassanyan murmushi yana lumshe idanuwa, ya karasa,
"Da kuma kyanki."
A daidai wannan gabar rasa abin da zan yi ma na yi, zuciyata na dinga jin tana fadada, tana wani irin girman da na rasa mene ne sanadinsa.

Cikin sassanyar muryar nan tashi ya ce
"Dalilai biyu ne zuwa uku suka kawo ni gidanku UmmulKhair. Na farko shi ne wanda na riga na yi, na gaisa da Umma, na fada mata kokarin diyarta. Sannan na biyu..."
Ya dakata hade da karbar wayar hannuna da nake kokarin cire password tsabar rasa abun yi. Ya ci gaba,
"Please look at me..."
Na kasa kallon nashi kuwa.
"Dan Allah fa na hada ki. Ki cire duk wani tunanin ni Oganki ne a wurin aiki. Shi ya sa na fada miki sunana na gama-gari duk don ki saki jikinki da ni."
Da kyar na iya dago kan nawa na kalle shi, sai dai jin idanuwansa a cikin nawa duk sai jikina ma ya dauki rawa, na daburce tare da rasa abun yi.

"Abu na biyu shi ne ina son next Assignment dinki ya kasance ni da ke ne."
Kamar na so in gane nufinsa, sai dai tsantsar mamaki ya hana ni gasgata abin da nake tunanin yana nufin da kalaman nashi.

"I mean, ki yi next assignment dinki a gidana."
Da wani irin mamaki na daga kai na kalle shi, ya daga min kai alamun hakan dai yake nufi.
"Tun daga day one da na fara ganin ki ban taba daina tunaninki ba, musamman da wani mutum ya ce an yi kidnapping dinki kin yi wata hudu a hannun kidnappers. Da tausayinki na tafi, duk da wani tashin hankalin da na tarar a asibiti. Sannan rana ta biyu, rokona da kika yi a kan in rabu da mai keken nan da ya taba min mota, na tafi da tunaninki a zuciyata. Uwa-uba kuma ranar da kika fara zuwa office dina, na ji dadi kwarai da kika kasance a karkashina kike."
Ya yi shiru daga nan na kimanin minti biyu, daga ni har shi babu wanda ya furta komai, kafin ya ci gaba da cewa
"Ban taba zaton ko nan da shekara biyar zan so wata mace bayan Maryam ba, Allah Ya ji kanta da rahma. Sai da na ji ni na tsunduma tsundum a cikin tafkin kaunarki Khairi."

Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now