Page 27- Dare Dubu

Start from the beginning
                                    

Na kama hanya na fita.
Ko da na je Mama har rungume ni ta yi saboda farincikin gani na, ta kuma taya ni farincikin nasarar da muka samu.
Baba ma baki har kunne, yana kara jinjina min musamman da na fada masa ta hanyar da aka samu kama kidnappers din nan da suka jima suna addabar mutane kuma gwamnati ta kasa aikata komai a kansu.

Tambayar nan da nake son yi wa Baba na yi masa, ya dan yi shiru jim, kafin ya ce
"Ashe ba mu taba yin maganar nan da ke ba Khairi."

Mama ta gyada kai,
"Ina fa ta ba mu damar yin duk wata magana ma da ta shafi mutuwar Ummu? Tun lokacin na so mu tattauna a kai amma na lura da ko zancen ma ba ta so. Shi ya sa kawai na rabu da ita, na tabbata akwai ranar da za ta so ta ji, tunda ba nan za ta dawwama da danyen raunin mutuwar ba."

Baba ya yi gajeren murmushi, irin wanda bai da alaka da nishadi, ya ce
"Tabbas bayan na ajiye kudin sun dauka a inda suka sanya ni ajiyewa, da ranta muka bar wurin, ina ta jin dadin ganin ta cikin aminci, ita kuwa maganar farko da ta fara hada mu ita ce
"Baba, a taimaka a karbo min Khairi, Baba wallahi zama a wurin nan babu dadi, muna mu biyun ma babu dadi ballantana kuma da babu ni. Ban san yaya za ta ci gaba da rayuwa ita daya a wurin nan ba."
Na dinga tausarta ina ba ta tabbacin ke ma za a karbo ki da izinin Allah.

Ban san hawa ba ban san sauka ba, ban san daga ina harsashin bindiga ya dirar mata a kirji ba, sai kawai zubewarta na gani. Ban koma ta kan neman wanda ya harbetan ba sai ta kanta, na dinga jijjiga ta ina kiran sunanta amma shiru, na daga hannunta ya koma ya langabe, na saita kunnuwana saitin zuciyarta amma sai na tsinci bugun numfashinta tsaye cak! Ba ya tafiya. Da karfi ta sauke wani irin ajiyar zuciya, wanda ya yi daidai da fitar dukkanin numfashinta.
Babu wanda ya san abin da ya faru har sai da asuba, ko mahaifiyarta ga ta nan ba ta sani ba, saboda ban iso nan gidan ba sai asubar. Ban dauki gawarta ni kadai ba sai da na kira mutum biyu daga cikin 'yan'uwana, daya Yayana sai Kawuna suka zo muka dauke ta, daga nan kuma gidan Kawun nawa muka nufa tunda duk mazauna garin Sassanya ne, kuma ya fiye mana kusa daga dajin a kan mu taho nan Katsina.
Sai da asuba ne muka iso nan din.
Wasu daga cikin dangi da mutanen arziki sun nemi mu sanar da hukuma amma sai na dage a kan lallai a bar zancen kawai, ai lokaci ya riga ya kure, kafin a tafi ake sallama ba sai an dawo ba. Kuma akwai wadanda suka fi mu kudi da mukami, ba su sanar da hukuma ba, ko kuma sun sanar din amma an kasa yi musu komai. To mu su waye da za a iya yi mana wani abu?
Da wannan hujjar muka share batun. Wai kuma da rana sai ga labarin ke ma wani mutumi ya tsince ki, da ya kai ki wurin hukumar garinsu shi ne su kuma suka kawo ki nan Katsina, a asibiti General. Wata kawarki ta je dubiya a dakin ne ta gan ki ta gane ki duk da ba a cikin hayyacinki kike ba, daga nan ne aka sanar da Fatima da 'yan'uwanki fa.
An samu kin dan farfado har kika tambayi Ummu aka shaida miki tana asibiti, sai kuma lum! Kika sake somewa.

Wannan shi ne ainahin abin da ya faru, ba wai tsintar gawar Ummu na yi ba kamar yadda da yawan mutane suka dauka. Da ranta na karbe ta, har magana mun yi, kafin kuma aka kashe ta murus har lahira."

Na sharce gumi hade da hawayen da ke kwance saman kumcina. Mun jima muna alhinin komai kafin na mike na yi musu sallama na tafi. Zuciyata cike da wasi-wasin ba kidnappers din nan suka kashe Ummu ba.
To idan su ne, da wace hujjar za su kashe ta?
Me ya sa za su kashe ta bayan an ba su kudi, kuma sun tabbatar da kudin sun kai adadin da Baba ya fada musu?
Sannan sun tabbatar babu dan sanda ko wani jami'in tsaro tattare da baba. Wadannan dai ai su ne dalilan da ke janyo su kashe mutum bayan an yi yarjejeniyar karbarsa.

Da wannan na isa gida zuciyata fal da tunani. Ina ganin dole sai Oga ya tsaya min na ga su Zaki, ta yiwu su fada min gaskiya. Idan ba su fada ba kuma zan roko Oga a kan a kai case din kotu, watakila za su bayar da tabbacin kisan Ummu, idan har sun rike ta din, don adadin mutanen da suke kamawa ba ma lallai ba ne su rike kowa.

Washegari na shirya na tafi asibiti dubo Aysha tunda an kwantar da ita ne saboda malaria da ta kama ta sosai. Ban wani jima ba saboda danginta sun zo daga Dutse idan ta ji sauki za su wuce da ita har ta dan dawo da kuzarinta.
Daga asibitin kai tsaye gidan Anti Maryam na je. Ta yi farincikin gani na ba kadan ba, ta ce
"Wallahi yanzun nan muka gama zancenki da Abban Rukayya, ya ce zancen scholarship din nan akwai yiwuwar ya taso. Na fada masa ai ko ya tashin ma ba za ki je ba saboda kina aiki yanzu, kuma kina kaunar aikinki."
Na yi shiru kawai sai murmushi da na yi.
"Sannu sannu da zuwa kanwata. Na yi kewarki sosai wallahi. Ina fatan an samu nasarar abin da aka je nema."
Duk da ba ta san inda na je da kuma aikin da na yi ba.
Da annuri a fuskata na ce
"Mun yi nasara sosai Anti Maryam, an kama wadanda suka yi garkuwa da ni, kuma suka yi min fyade."

Ta kwalalo ido tana kasa fadin komai saboda zallan mamaki ta ce
"Shin da gaske kike ko da wasa?"
"Da gaske Anti Maryam."
Na ba ta amsa ina dorawa da
"Aikin da na je yi kenan a kaiyen Kanya da ke cikin kauyukan Meshe. An kama su, har da informers din da suke garin duk an tafi da su, yanzu haka suna can kulle."

Tsabar farinciki har da rungume ni ta yi, da guntuwar kwallarta ta ce
"Wannan lamari ya yi min dadi Khairi. Hakika DARE DUBU na barawo ne, amma DARE GUDA daya tak sai ya kasance na mai kaya. Yau ga dubun azzalumai ta cika, watakila mu samu sassauci a yanzu, mutum ya yi tafiya a tsanake cikin kwanciyar hankali."

Muka ci gaba da hira har bayan la'asar sannan na mata sallama na tafi. Ina kara jinjina yadda matar ke kaunata da zuciyarta guda.
Haka Allah Yake lamarinSa, a lokaci guda sai Ya hada ka da wanda ba ka taba tsammani ba a rayuwarka, kurum don ya zama wani tsani na ginuwar farincikin duniyarka.


Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now