Gani na da kalar wannan shigar ya sanya su duk kallo na fuskokinsu na nuna alamun mamaki. Na dauke kaina daga duban Amarya da ta gama cika da al'ajabi, na karasa daf da Azumi.
Bindigata na saita a daidai fuskarta, tamkar ban taba murmushi ba a duniya nake bin ta da kallo, yayin da duk su kuma iyalan gidan suke bi na da kallo, yaran gida kuwa wasu kuka suka fasa da alama sun san bindiga sun kuma san amfaninta ko da a talabijin ne. Cikin daurewar fuska na ce
"Kar ki kuskura ki motsa daga nan wurin, motsawarki daidai take da motsawar rayuwarki. You are under arrest."

Ta dora hannuwanta bisa kai tana fashewa da wani irin kuka,
"Don Allah ki yi min rai diyar nan. Ina ce da kika hana ni fita ba ki ga na sake fita ba? Me kuma na yi da za ki saita mini bindiga. Na roke ki da Allah kar ki kashe ni..."
Na zaro cellular phone dita na latsa kira,
"Gidan maigari Mati Amadu, copy. Azumi matar maigari Mati, copy."
Sannan na mayar da wayar a ma'ajiyarta, still bindigar tana saitin fuskar Azumi.
"Muna zarginki ne da hada baki da 'yan garkuwa da mutane kina ba su boyayyun bayanai game da wannan garin. Number two, muna zargin an hada baki da ke wajen sace d'an mijinki wanda kike riko, har aka kashe shi."

Ta zaro ido cike da tsoro ta ce
"Wallahi diyar nan ba ni na ce su kashe shi ba, ban kashe shi ba, na dai san na ce su sace shi don mu samu kudi daga wajen maigari, amma babu ni a batun kisan sa, hasali ma sai da na fada musu ban so su kashe..."

"Duk wadannan bayanan ba muhallin yinsu ba ne nan, kina iya tattara su watakila za su yi miki amfani a gaba."
Na juya kaina jin motsin mutane daga bakin kofa, sai ga maigari da tawagarsa ta fada, da Oga Sagir da Oga Usman biye da su.

Oga Sagir ya jinjina min tare da fadin
"Weldone UmmulKhairi. You did a good job."
Ya juya ga Azumi sannan ya dube ni,
"Handcuff her."
Na karbi ankwa daga hannun Oga Usman na zarga mata.

Maigari sai kuka, matansa kuka, yara kanana kowa kuka. A cikin kukan maigari ke fadin
"Kin cuci kanki Azumi, don ba zan ce kin cuce ni ba, kanki kika cuta. Kin ga yanzu za ki je ki kare rayuwarki ne a gidan yari, yayin da mu kuma za mu ci gaba da rayuwarmu cikin kwanciyar hankali.
Na jima ina rokon Allah a kan Ya kawo mana dauki, ya toni asirin duk wasu azzaluman da suke kewaye da mu, ashe wannan ranar tana nan zuwa, ashe kina daya daga cikin azzaluman nan da nake addu'a a kansu."
Ya juyo gare ni bayan ya share hawayensa, ya ce
"Kin yi kokari sosai diyar nan, ta yadda kika yi aiki ba tare da ko alamar fahimtar wani abu ba game da ke. Kin cancanci lambar yabo. Allah Ya ci gaba da dafa miki, Ya kare ku a duk inda kuke."

Kaina sunkuye nake amsawa da amin.
Na juya na sara wa su Oga Sagir, kafin muka fice waje aka sanya ta cikin mota tare da sauran ma'aikatanmu da ke jan motar da gadinta.

Sauran gidajen wadanda Oga Sagir ya zayyane wa maigari muka nufa, duk babu wani bata lokaci aka kama su. Mutum daya ne dai ba mu samu a gida ba, ashe wai ya ji labarin abin da ke faruwa shi ne ya gaggauta guduwa. Matarsa da ta ji muna neman hadawa da ita sai ta tona masa asirin ya yi shigar mata ne ya tafi, idan an gaggauta za a same shi a hanya.
Mun kuwa same shi din har ya tsayar da babur zai hau, aka shako shi sannan Oga Usman ya cire masa hijabin jikinsa, daga nan muka karasa kofar gidan maigari.

Mutane da yawa kofar gidan maigarin, mata da maza; manya da yara sai alhinin wannan abu ake. Babu wanda ake zato a cikin duk wadanda aka kama, saboda a fuska mutanen kwarai ake musu kallo, sai dai hakan ba shi ba ne halayen da ke lullube da zukatansu.

Shiga cikin gidan na yi na dauko akwati da jakar goyona na fito, na je har inda Amarya take na yi mata godiya sosai, na jinjina wa karamcinta da na yaranta, sannan na koma wurin motarmu, daga nan kawai muka wuce.

Oga Sagir ya kira waya, bayan ya gama ya ce a yanzu haka ana can daji ana fafatawa, ba a dai cafke kowa ba tunda ba su gano ainahin wurin zaman kidnappers din ba, sai dai suna jin harbe-harbe daga nesa, su ma kuma suna yin nasu harbin.
Babu hadin guiwar police ko army, mu ne kadai muke kidinmu muke kuma rawarmu, muna fatan dacewa a cikin kankanin lokaci. Da ma kuma tafe suke da map, shi suke bi domin ya isar da su ainahin mazaunar kidnappers din.

Mun kuwa dace din, don babu mutum daya da aka kashe daga cikin ma'aikatanmu, sai dai harbi, an samu har mutum biyu amma an ci sa'a babu wanda bullet ya zauna a jikinsa. An samu nasarar kama kaf kidnappers din da suke cikin dajin, sannan an kubutar da mutum sama da ashirin da suka sace.
Babu wata tazara a tsakanin isarmu da isarsu.
Aka kulle informers wurinsu daban, sannan kidnappers ma wurinsu daban.
Sauran victims din kuwa, aka sallame su, Oga Ahmad ya sanya a kai su tasha, tare da kudaden mota ga kowannensu. Ni da Aysha rungume juna muka yi sadda muka hadu. Daga nan aka wuce asibiti da ita domin auna lafiyarta saboda zazzabi da take ta fama da shi.

A lokacin da na shiga office din Oga Ahmad waya yake yi, na ci gaba da tsayuwa har sai da ya gama ya ba ni izinin motsawa, ya ce in zauna a kan kujera.
Tun kafin in ce komai ya riga ni,
"Weldone, Weldone UmmulKhairi. Kin yi aiki mai kyau wanda kika cancanci babbar kyauta."
Ya saki murmushi.
"Sai dai duk kin yi baki, kin rame. Duk zaman kauyen ne, ko kuwa rasuwar saurayinki ne har yanzu a ranki?"
Na sunkuyar da kaina ban ce komai ba. Ya ci gaba da fadin
"Hakika wannan aikin namu ba iya na maza kawai ba ne kamar yadda mutane ke daukan bai dace ga mata ba. Tunda idan da aikin maza ne kawai ta yaya za ki shiga jikin Shamsu har ki samu muhimman bayanan da muka samu? Ga Azumi ita ma, da namiji ne watakila da corper's lodge za su sauke shi, da ba za mu samu komai dangane da ita ba.
Kina da kwazo sosai, ina son aiki da mutum mai kwazo irinki. Don haka na jinjina miki, and you deserve to be awarded."
"Thank you Sir."
Na furta a hankali ina jin dadin kalaman nashi.
"Your award will be ready in few days in shaa Allah. Za a yi taron karrama ki idan mun gama da wadancan mugayen mun tura su court."
Na sake yi masa godiya. Ya ce
"Ki samu ki je gida ki huta sosai. Ki ga Umma don na san kina cike da kewarta ko?"
Na yi murmushin jin dadi.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now