Page 22- A Week To Go

Start from the beginning
                                    

"To kuma Yaya ai ba zai yiwu ba mu tafi mu bar ki cikin wannan halin. Ko kuwa dai?"
"A'a ku je kawai Barira, ba matsala ai, ga yara nan idan ma ina da bukatar wani taimakon."

Cikin boye murmushina na ce
"Ga ni ni ma, zan iya taimaka miki idan kina da bukata, zan ma zauna a nan tare da ke."

Idanuwa ta watsa min cike da tsoro ta ce
"Ba ma sai kin zauna ba wlh, kawai ki je ki kwanta abunki ki huta, ai ga su Hadiza nan, za su taimaka min na tabbata."

Ban kara cewa komai ba kawai na mike na shige daki abina. Na samu yadda nake so, kuma ina fatan ta kiyaye sharuddan nawa har zuwa sadda komai zai kammala.

Har na kwanta kuma na ji ina son jin muryar mahaifiyata, ina son ta yi min addu'ar nan tata kamar yadda ta saba.
Na kuwa mike na zira hijabi na nufi neman service.

Na latsa kiran Umma babu jimawa ta dauka,
"Yanzun nan muke cikin maganarki ni da Mamanku ga ta nan, kwana biyu ta ce ta ji ki shiru na ce ni ma ba ki kira ni ba ina ta neman ki kuma ba a samu."
"Wallahi kuwa Umma kin san da ma na fada miki sai an je inda network yake sannan ake samu, ko za ki shekara nema na ba za ku same ni ba har sai idan ni ce na neme ku, ko kuma aka yi katari na gitta ta inda service mai kyau yake."

Ta amsa da
"Haka ne. To ya aikin naku?"
"Alhamdulillahi Umma. In shaa Allahu mun kusa gamawa a nan inda muke."
"To ma shaa Allah, ina miki fatan alkhairi. Allah Ya sa a yi lafiya a gama lafiya."
"Amin Ummana. Ina Mama take? Na huta sai na kira ta daban, ba ta wayar in gaishe ta ita ma."

Ta mika wa Mama wayar, bayan mun gaisa ta yi min addu'a sosai kamar yadda ta saba, sannan ta mayar wa Mama da wayar, ina jin tana mata bankwana ta tafi, cikin hikima ta ba mu wuri ne don mu tattauna ni da mahaifiyata. Ba ta san ba ni da wannan lokacin ba, a yanzun ma karya maganar Oga Ahmad ce na yi tunda ya hana ni zuwa neman service gudun zargi daga mutane.

"Jiyan nan kuwa Antinki Maryam ta zo, ta ce in gaishe ki sosai idan mun yi waya."
"Ina amsawa Umma, ai idan na samu lokaci ita ma nakan kira ta mu gaisa."
"Kin kyauta kwarai."
"Bari in je Umma, sai mun sake magana."
"Allah Ya yi albarka Ya sa ku gama da duniya lafiya. Allah Ya ba ku nasara Ya sa ku gama da aikin nan lami lafiya."
"Amin Ummana, a gaishe da su Safra. Idan na samu lokaci sosai zan kira a ba su mu gaisa."
"Shi kenan ba damuwa. Sai an jima."

Kamar an ce in kunna Data sai ga sakon Oga ya shigo, voice note ne, na yi gaggawar budewa, can na jiyo muryar Bafulatani yana fadin

"Ta ba ni wannan lambar ne a matsayin ta mahaifinta. Muna neman naira miliyan goma daga hannunka, na ba ka nan da sati guda, idan ba a kawo ba za mu jefar muku da gawarta."
Sai ga muryar Oga ya ce
"Za mu bayar, don Allah kar ku kashe ta. Kafin nan da sati dayan zan kawo muku. Amma ku taimaka ku ba ni ita in ji muryarta."
Can na ji muryar Aysha tana kuka tana rokon sa
"Daddy, ka taimaka a ba su kudin nan..."

Na kashe kawai. Na fahimci komai, na gane sun nemi lambar wayar mahaifinta, shi ne ta bayar da ta Oga Ahmad, sun kira sun nemi miliyan goma, ya kuma amsa musu da za a bayar kafin wa'adin sati dayan da suka yanka.
Na saki murmushi kawai, wannan wani irin puzzle ne da babu wanda zai iya daidaita shi idan ba mu da muka tsara shi ba.

Na latsa kiran Oga, bai dauka ba sai ya kashe ya kira ni da Kansa.
"Ina wuni Oga? Ya aiki kuma?"
"Lafiya kalau Khairi. Au, Safina. Ke za a tambaya aiki ai, ke ce a tsakiyarsa ko?"
Ya yi murmushin da har sai da ya bayyana.

"Lafiya lau Sir, na ji voice din da ka tura min. Da ma ni ma ina son sanar da kai mutanen nan fa ba su gane matsayin Aysha ba. Ta bagarar da su cewa mahaifinta ya ba ta kayan tsaron lafiyarta, kuma sun yarda, da alama ba su fahimci komai ba a Id card dinta.
Sannan batun matar nan, ashe uwargidan maigari ce."
Na yi masa bayanin duk yadda muka yi da ita.

"Weldone Khairi, kina da brain wallahi. Sosai nake son yin aiki da irinki masu kwazo da tsananin sanin makamar aikinsu. Ki shirya, kafin nan da sati daya za ki kammala assignment dinki. Sai kuma next one, wanda nake tsammanin ki yi shi a..."
Sai kuma ya yi shiru, ya gyara zancen da fadin
"Just get ready, the game is about to start."
"Yes Sir."
"Take care."
Ya fada yana yanke wayar.

Yanzu abin da ya rage min kawai shi ne na karasa aikin bangaren Shamsu, kuma shi ma din a gobe nake son kammala komai, zuwa jibi in shaida wa Oga na gama da nawa saura nasu.

Washegari ko da na isa makaranta babu Malamin da ya zo, na dan yi karatu sama-sama, sai ga Oga Headmaster ya iso. Na gaishe shi ya washe hakoran nan nashi masu cike da gansakuka.

"Malama Safina, gaskiya kina kokarin zuwa da wuri. Dalibanki ma suna yaba miki sosai."
Na dukar da kaina ina fadin
"Na gode Yallabai."
"Ah no, ai ba sai kin yi godiya ba kin cancanta ne."
Yana dariya hade da kokarin zama daf da ni.
Na yi saurin janye jikina,
"Yallabai ka yi hakuri kar ka zauna a nan, ka ga dalibai suna zuwa kar su zargi wani abu, tunda bai dace headmaster ya zauna da Malama haka ba."
Ko a jikinsa ya daga kafada,
"Kar ki wani damu, in don dalibai ne su ma suna da damar yin yadda suke so. Ke ni fa nan gaba ina ganin ma fara hada auratayya zan yi tsakanin dalibi da daliba, kin ga shi kenan na samu lada ko?"

Na gyada kai kawai ina dariya, har cikin raina mutumin yana saka ni nishadi fiye ma da Mallam Shamsu.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now