Page 18- Tarko

Começar do início
                                    

Yau da na isa makaranta an samu karin Malamai biyu, su din ma dai duk sammakal, tamkar ba malaman makaranta ba, babu tsafta, ilimin ma ya yi musu karanci, sai zaman gulma da ciye-ciye kamar wasu mata. A bangaren headmaster shi din ma dai hakan take, na karbi aji biyar zan koyar da su darasin IRK, tunda shi ne wanda na iya ko da ban karance shi ba saboda ina zuwa islamiyya. A lokacin da na je karban sai da ya fara ja na da hira, wai ni kyakkyawa ce me ya kawo ni wannan kauyen mai cike da ruguntsumi da tashin hankali?
Ban ba shi amsa ba sai fita kawai da na yi ina ayyana ta inda zan fara koyarwa tunda ban karance ta ba. Saukin ma daya a Islamiyya ina koyar da yara, don haka abun zai zo min da sauki. Sai dai matsalar, cike su lesson plan da sauransu. Kodayake ba ma lallai ba ne idan duk wannan din ya dame su a makarantar don ni kam ban ga alama ba.

Ina zaune ina karatu na tsinci wata hira da malaman ke yi wadda ta dauki hankalina.
Wannan Malamin na jiya ne ya ce
"Wallahi da a ce yadda na dauko talauci a baya, har yanzu ina cikin yanayin da tuni na bar garin nan, kai ina ganin da Ikko ma zan wuce in nemi kudin a can. Dan ni wlh ko mene ne zan iya yi in dai har zan samu kudi. Allah ma Ya san ban iya zaman talauci."

Suka tafa hannu suna masa dariya.
"Kenan dai yanzu ba ka tattare da talauci mutumina."
Wani ya fada bai daina dariya ba.
"Allah Ya yafe maka Malan Shamsu. Wato da Ikko za ka wuce kenan."
"Kwarai kuwa, ko a karkashin gada ne in dinga kwana ba."
Suka ci gaba da dariya.

"To wai kai me ya sa albashinka bai ishe ka ba? Duka-duka mata daya da yara biyu ai sai in ga dubu arba'in da biyu ta ishe ku rayuwa a kauyen nan dai ba wani babban birni ba."

Tabe baki Mallam Shamsun ya yi tare da fadin,
"Ba za ka gane ba Malan Abu. Ai su wadannan kudaden na iyali ne kawai. To kuma ai muna da bukatar wanda za mu dan kashe wa zawarawa da 'yan matanmu ko? Ko so kake mu dinga zuwa zance wurinsu kememe babu kudin zance? Idan haka ne kuwa ba za suke fitowa ba idan mun je."

Sosai daga cikin kalamansa na tsinci wasu abubuwan da ya kamata in yi bitarsu har sai na gano bakin zaren. Ina jin wani daga cikinsu ya ce
"To wai ma a ina kake samunsu din yanzu bayan albashinka?"
Exactly tambayar da ke cikin zuciyata, don da a ce da ni suke hirar babu abin da zai hana ni jefa masa ita ni ma. Sai na kasa kunne domin jiyo amsar da zai bayar.

"Ka dai san ai na fada maka zan iya yin komai domin samun kudi ko? To wallahi hanyar da nake samun kudi ta fi wannan wahalallen koyarwar sauki nesa ba kusa ba?"
Ya ba su amsa yana gaftar katon raken da ke hannunsa.

"To ka dora mu a kai mana mu ma mu samu?"
"A'a Malan Kamilu. Ba lallai ba ne idan za ku iya. Amma idan har kana ganin za ka iya din shi kenan, sai mu sa labule."

Mamakin mutumin nake ta yadda gaba-gadi yake fadin abin da ke cikin zuciyarsa. Wani abu da na lura shi ne bai iya boye-boye ba, tun zuwa na jiya na fahimci hakan.
Don haka ina tsammanin zan samu wasu bayanai daga gare shi, sannu a hankali ba sai na yi gaggawa ba.
Na fara tunanin ta inda zan fara, sai na tuna na ji zawara da 'yan mata a bakinsa, kenan ba zai yi wuyar shiga tafin hannuna ba. Na saki murmushi kawai tare da danna send, na tura wa Oga Ahmad hirar daga inda na fahimci akwai alamar tambaya game da mutumin.

Bayan lokacin tashi ya yi na matsa wurinsu, wannan shi ne right time da ya kamata in fara aiwatar da aikina na Mallam Shamsu, sai kuwa na je daidai inda yake zaune, na dan russuna na ce
"Mallam don Allah ko za ka ba ni aron lesson plan dinka? In ya so anjima sai ka same ni can gidan maigari ka karba."
Da annuri a fuskarsa ya ce
"Ok can gidan Maigari ne masaukinki. Babu matsala ki tafi da shi din, zan zo ko zuwa dare ne in ansa."
Godiya na masa, ina ganin yadda bakinsa ke annuri na san tabbas tarkona ya kama kurciya.

Ina isa na tarar Aysha ta iso ita ma, muka makalkale juna cike da farinciki. Abinci ne a gabanta amma ba ta ci ba ko kadan sai ruwan roba da take sha da cookies.
Na kalli jakar kayanta, hakan ya ba ni tabbacin ita ma a dakin Amarya aka sauke ta, na kuwa washe baki, hakan ya yi kyau, wai an sayar da gonar raggo an sayo masa fura.
Za mu fi jin dadin aiwatar da aikinmu idan muna tare.
Sai dai na tuna kalamin Oganmu dazu da muke waya, ya ce
"You have to be extra careful idan Aysha ta zo, saboda team work yana da dadi amma kuma ya fi komai hatsari, sosai yake son a bi komai a hankali wajen yinsa. Don ba wuya ta magana ma za ku iya bata lissafin."

Tabbas kuwa haka ne, dole mu kula da kyau gudun kar a samu matsala.

Ni ma nawa abincin na ciro daga jaka, ina ci muna hira sama-sama da Aysha har muka kammala.

Wuraren bayan la'asar aka ce ana sallama da ni, jikina ya ba ni Mallam Shamsu ne don babu wanda zai neme ni idan ba shi ba. Lesson plan din nashi na fitar daga cikin jaka, sai a lokacin ma na duba na ga abin da yake ciki. Ko ni da ban taba karantar fannin Education ba ina gani na san tarin shirme ne. Sannan jiya da yau din da na je makarantar ko sau daya ban ga ya shiga wani aji ba, amma ga shi nan duk da plan a cikin littafin. Na gyada kai kawai a zuciyata ina tunanin ta ina yara za su samu ilimi mai kyau alhali su kansu malaman ba masu nagarta ba ne?
Na zira hijabi a kan doguwar rigar da ke jikina na fita.

Shi din ne kuwa kamar yadda na yi tsammani, bayan mun gaisa na mika masa littafin, da annuri ya ce
"Idan dai kin san ba ki kammala ba ki bar shi kawai a wurinki har zuwa sadda za ki gama."

Na gyada kai,
"Na gama duka, na gode sosai."
"To madalla. Yaya yanayin garin namu? Fatan dai kina jin dadinsa?"
Na dan murmusa,
"Ba laifi."
Na ba shi amsa don ina dan son tsawaita hirar tamu ne.
"Ba laifi fa kika ce. Kenan dai babu dadi ko?"
"A'a da dadi fa. Kawai dai ka san ba lallai in ji dadinsa ba kamar namu garin. Tunda ban san kowa ba."

Ya gyara zaman hularsa da duk ta gama jin duniya, da alama saboda ni ya sanya ta. Ya ce
"Haka ne kuma. Ni bari in wuce, may be zuwa dare in dawo mu sake gaisawa sosai ko?"

Tsaki na yi a cikin zuciyata don har ga Allah ba na son shisshigi. Na amsa da to sannan na juya ban ko jira na karasa jin sallamar da yake yi min ba.




Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUOnde as histórias ganham vida. Descobre agora