Page 16- Daren Farko

Start from the beginning
                                    

"Yawwa, haka nake son ji. Watakila idan matsiyatan iyayen naku suka ji yadda sautin kukanku ke fita za su yi hobbasa su kawo mana kudin garkuwarku. Haba! Na gaji haka nan. An kusa zuwa gabar da zan yanke hukunci a kanku."
Yana fadin haka yana latsa kira, bugu biyu kuwa aka daga.
Muryar Baba ce, da sallama a bakinsa don bai gane lambar ba da alama, har sai da Ogan ya yi magana sannan ya gane.
"Ina fatan ita ma waccan komadaddiyar matar tana ji na! Don ba zan sake wahalar kiran ka ba ita ma in kira ta. Tunda dai duk tafiyar guda ce, idan ma ba ta kusa sai ka isar da sakon gare ta."
Ya fada hade da kara wayar tsakanin fuskokinmu, kuka muke yi dukkanmu. Ina jin sadda Baba ya kira sunayenmu, kafin ya dora da
"Ku yi hakuri kun ji, muna nan muna ta bakin kokarinmu wajen ganin mun hada kan kudaden nan, amma abun ya faskara. Kudin ne da yawa, ga shi kuma babu su wallahi sai dai godiyar Allah. Amma da izinin Allah ko rabin abin da aka bukata na mutum daya ne za mu hada mu kawo ko za su ji kanmu su sake ku. Kuna ji na?"
Ya tambaya, jin babu wacce ta yi magana a cikinmu.

Ummu ce ta yi karfin halin cewa
"Baba a taimaka a fitar da mu, wallahi babu dadi a nan din, ga Khairi ba ta da wadatacciyar lafiya, ciwon kan nan nata yana damun ta. Babu abincin kirki Baba, babu sutura, babu bacci mai dadi, komai babu dadi. Ga kewarku, Baba don Allah duk yadda za a yi ku hada kan kudaden nan, na san ba abu ba ne mai sauki, tunda babu."

Fizge wayar Oga ya yi da karfi, sannan ya ce
"Ina fatan ka ji abin da nake son ka ji din. Don haka kuna da wa'adin sati daya, idan har ya cika babu kudin nan, zan fada muku inda za ku dauki gawarsu."
Daga haka ya yanke wayar hade da tattaune layin kamar yadda ya saba.

Na runtse ido ina jin tausayin rayuwarmu da ta iyayenmu, wannan wace irin rayuwa ce? Wane irin zamani muke ciki wanda ake farautar rayuwar mutum tamkar ta dabbobin daji? Sai yaushe ne dan Nigeria zai zama mai 'yancin kansa kamar yadda ake fadin kowa yana da freedom a kasar? Sunan dai Nigeria ta samu 'yancin kanta ne a 1960, amma wannan 'yancin babu shi. Idan kuwa har tana da shi, to lallai 'ya'yan cikinta ba su da shi.
Shin ina shugabanninmu na siyasa suke?
Ina Sarakuna?
Ina manyan Malamai?
Ina sojoji da 'yan sanda?
Ina Mopol da sauran jami'an tsaro?
Duk mene ne amfaninsu idan har za a dinga cinikin fansar mutum a cikin kasarsa?

Da wannan tunane-tunanen aka kore mu zuwa dakunanmu. Zuciyata cike da tunanin ta inda Umma za ta iya samun wadannan kudaden da ba na jin ko a mafarki ta taba mallakarsu. Har gara ma Ummu tunda babanta yana raye, sannan suna da dangi masu yi musu. Ni kuwa fa? Umma ita ce karfin komai namu, sai kuwa taimako da ga Baban Ummu. To kuma an zo gabar da kowa tasa ta fisshe sa ne, don ba zai yi wahalar Neman kudin fansar Ummu ba ya yi tawa.

Kuka sosai na yi a wannan daren, duk kokarin Ummu na ganin na yi shiru amma na kasa, ita gudunta kar ciwon kaina ya taso don ba abu ne mai sauki ba idan ya tasar min har da zazzabi yake hadewa.
Abin da na fahimta shi ne, ita ba ta ma tausayin kanta kamar yadda take tausayina.
Shin waye ya taba ganin zallar soyayya irin wannan?

***
Na sharce hawayena bayana na gama da tunane-tunanen duniya.
To ni kuwa me zai tsorata ni da ba zan iya tsayuwa wajen ganin asirin azzaluman ya tonu ba?
Na shirya, ko da a ce zan rasa numfashina ne in dai a wajen tonuwar asirinsu ne zan yi, kamar yadda na daukar wa kasata alkawari.

Kamar da wasa har karfe ukun dare ta yi bacci bai dauke ni ba, a hankali na dinga jiyo motsi daga waje, na kasa kunnuwana da kyau ina son sanin ta inda motsin nan yake amma na kasa ganewa. Da rashin tsoro irin nawa sai na tashi zaune, na hau takawa a hankali har na isa bakin 'yar kankanuwar tagar da ke cikin dakin, na janye labulen gararar da ke jiki na dan leka, sai na ga wata mata ce ke bin bango cikin sanda za ta fita waje, na darara ido da kyau amma ban gane ko wace ce ba, tunda zuwana duk na ga matan gidan har ma da yara sai da amarya ta yi min bayaninsu.
Kallabin da ke kanta ta sanya ya sauko har saman fuskarta ta yadda ba za a iya gane wace ce ba. Cikin sandan har ta karasa zauren gidan, daga nan kuma ban kara sanin abin da ya faru ba. Na duba wayata, karfe uku da kusan rabi. Mamaki bai bar ni ba na ci gaba da jiran tsammanin dawowar ta amma shiru, sai da ta dauki kusan minti ashirin sannan na yanke wa kaina shawara.
Na lalubi kuguna na daidaita zaman 'yar karamar bindigata wadda ake kira da pocket pistol, sannan cellular phone dita ma ta aiki tana jikina. Kawai sai na samu kwarin guiwar fita, domin ina jin a jikina lokacin fara aikina ya yi, watakila a daren nan zan fara aiwatar da abin da ya kawo ni kauyen.

A hankali nake takawa don kar in tashi amarya da yaranta, na isa bakin kofa har na kusa yin tuntube da fo din da ta ajiye domin fitsari idan sun ji, don an ce a garin ba a fita ko fitsarin dare gudun kar a sace ka tunda bandakunansu a filin tsakar gida suke wasu ma can bayan gida.
A hankali na bude kofar, na janyo ta na rufe ta yadda ba za ta tashe su ba.
Kamar yadda waccan matar ta dinga bin bango ni ma hakan na yi, ban kuma tinkari zaure ba kai tsaye sai na labe daf da kofar.
Kasa-kasa na dinga jiyo muryoyi, duk maza ne sai na mace daya, kuma babbar mace da alama don yanayin m sautin muryar ya bayyana hakan. Na zura kaina ta kofar ko zan iya jiyo wani abu amma shiru ban iya jin komai din ba.
Kusan minti goma ina tsaye, sai can na jiyo suna sallama, kafin kuma na ji ta ce

"Na manta in fada muku, muna da sabon kamu a garin nan, a nan gidan ma. 'Yar bautar kasa ce ta zo."




Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now