Page 15- Kudin Fansa

Start from the beginning
                                    

"Ko kwanakin can an dauke min yaro, suka bukaci in ba su kaji guda hamsin tare da kudi naira dubu dari biyu; mun hada an kai din fa amma sun kashe shi har lahira."
Na yi saurin tarar numfashinsa,
"To amma Baba, me ya sa har yanzu kuke zaune a garin? Me ya sa ba za ku tashi ku bar musu shi ba can su karata?"

Irin murmushin da bai da alaka da nishadi ya yi, ya amsa min da
"Tashin ne ba zai yiwu ba diyata. A baya tun ma kafin abun ya yi ta'azzarar haka mun taba yunkurin tashi mu koma can cikin garin Meshe, amma sai ga sako sun aiko mana wai duk muka kuskura muka tashi sai sun sake bin mu har inda muke. Don haka dole muka zauna, sai dai a kullum cikin dar-dar muke, babu kwanciyar hankali ko kadan."
"Kenan idan na fahimta Baba, daga cikin kauyen nan akwai mai kai musu labarai game da abubuwan da kuke aiwatarwa?"

Ya jinjina kansa yana ba ni tabbaci.
"Fadi ki kara diyata, tabbas daga cikinmu akwai mai kai musu rahoto, sai dai har yau din nan mun gaza gane ko waye. Duk iya hasashen mai hasashe kuwa an kasa hasasho wanda yake kwasar zantukanmu idan mun yi yake isar musu. Tuni mun hakura tare da fawwala wa Allah. Mu dai mun san idan sun fi karfinmu ai ba su fi karfin mahalaccinmu ba, wanda su din ma shi ne Ya halicce su kuma yake ba su talala a kan abin da suke aiwatarwa. Dole kuma akwai ranar kin dillanci, ranar da komai zai yamutse musu."

"Tabbas wannan zance haka yake Baba. Babu wanda ya fi karfin hukunci daga wurinSa AzzawaJalla. Kuma da sannu kunkuru zai kai inda barewa ta je."
Da a ce da ne kafin in shiga aikin DSS, da na tabbata yanzu ina nan sharar hawaye, amma a yanzu da zuciyata ta dake da komai, na dai tausaya musu, sannan na yi alwashin da yardar Allah komai ya kusan zuwa karshe, karshe din da nake fatan zuwansa da gaggawa. Ina ji a jikina zuwa na tamkar mabudi ne na samun sassaucinsu.

"Ki samu ki je ki kwanta kafin zuwa safe sai a gwada miki makarantar da za ki koyar din, duk da fiye da rabin iyaye sun hana yaransu zuwa makarantar. Amma na tabbata zuwan nan naki zai kara janyo su musamman idan kika dage sosai."

Na mike ina masa sai da safe, a zuciyata kuwa fal tunani ne, sannan na danna malatsin tura wa Oga recording din duk da na dauka, kafin safe in fita neman service tunda an ce akwai dutsen da ake zuwa a samu.

Shimfida mai kyau na tarar mai dakin da aka kai ni da na ji ana kira da amarya ta yi min. Ko da na koma na tarar duk sun yi bacci daga ita har yaranta. Na kwanta kan shimfidar tawa hade da shiga wurin sunan Oga, na rubuta masa;

"Sir, ko dai za a turo mini Aysha ne mu yi aikin nan tare? Akwai babban hatsari a garin nan, kamar ba zan iya ni kadai ba. Ko kuma wani namijin da ake ganin zai iya mu yi tare."

Daga nan na ajiye wayar na rufe idona, sai dai ko kadan baccin ya gagara zuwa, tunani fal a raina, tunanin rayuwa da komai, kamar wasa kuwa, wannan tunanin sai ya dauke ni ya kai ni can wani lokaci, lokacin da muke cikin kasurgumin dajin nan da 'yan garkuwa da mutane suka kai mu.

TUNA BAYA

A lokacin da muka cika sati daya hannunsu, aka saki wannan dattijuwar matar wacce muke daki daya da ita, kasantuwar an biya kudin fansarta naira miliyan biyu. Ta yi mana fatan alkhairi kafin ta tafi, sannan ta gargade mu da mu rage taurin kai, musamman ma ni. Da an umurce ni da abu in kokarta yi don mutanen nan ba imani ne gare su ba.
Muka yi mata godiya tare da fatan alkhairi. Tana kuka ni da Ummu ma muna yi har aka fice da ita, ya zamanto daga mu sai budurwar nan da aka kashe mahaifinta, sai 'yar yarinyar da muke jin ta tamkar kanwarmu ta jini.

Sai da muka cika sati biyu cif sannan aka karbi lambar Baba a wurin Ummu. A lokacin na tabbata sun gama jigata da rashinmu. Saboda rashin ji daga gare su ma ba karamin tashin hankali ba ne, don sai a gwammaci mutuwar mutum ma fiye da ya bace bat babu labarinsa, musamman kuma diya mace.

A gabanmu aka kira shi, cikin rawar murya ya amsa, da alama abin da ya jima yana saurare kenan.

"Kana ji na? Idan kana cikin mutane ka mike ka fita, kar ka bayar da wata alama da za ta sanya a fahimci da waye kake waya."

A hands free wayar take, muna jin yadda yake in'inar fadin
"To...to, zan fita...na fita ma."

Dan tsurut din Ogan nasu mai zubin balbela ya kwashe da dariya, sannan ya daure fuskarsa ya ce
"Ka yi kyan kai. Yaranka, ga su nan a hannunmu fiye da kwana goma. Kuma ba za mu sake su ba har sai kun biya kudin fansarsu, kowacce naira miliyan uku, su duka zai kama miliyan shida. Na yi muku ragi ne saboda ku matsiyata ne ba ku gaji komai ba sai talauci."
Sannan ya juyo gare mu ya ce
"Ga su nan ka ji muryoyinsu don ka tabbatar da suna hannun namu."

Da kyarmar hannu Ummu ta karbi wayar, a tare muka kira sunan Baba hade da fashewa da wani irin kuka mai cike da rauni.
Bai bari mun kara fadan komai ba ya kwace wayar yana wannan dariyar tashi ta mugunta.

"Idan an kawo kudi, mu saki yara babu bata lokaci, amma idan ba a kawo ba, hakan daidai yake da sadaukar da su gare mu. Za mu yi yadda muke so da su tunda kun bar mana su.
Sannan ka sani, fitar da wannan zancen ga hukuma daidai yake da riskar gawawwakinsu a wulakance. Idan kunne ya ji, gangar jiki ta tsira."

Ya kashe wayar hade da zare layin ya tattaune shi ya zubar. Bayan ya mayar da wani layin ya karbi lambar Umma a wurina. Ita ma iri daya abin da ya fada wa Baba shi ya fada mata. Har ma ta fi Baban rikicewa saboda shi namiji ne ya dan fi ta karfin hali. In ban da kuka babu abin da take yi. Ya miko mana wayar, tsananin rauni da tausayin mahaifiyata ya sanya na kasa fadan komai sai kuka, Ummu ce ta dan yi mata magana tare da rokon duk yadda za a yi a yi don ganin an hada kudin nan an ba su.

"Ku daina kuka...ku yi hakuri Ummu, ki ba 'yar'uwarki hakuri kar kukan ya haddasa muku wani ciwo. In shaa Allahu za a hada, za a kawo, za su sallame ku cikin aminci."

Fizge wayar ya yi sannan ya zare layin shi ma ya taune kamar yadda ya yi wa na farkon.


Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now