Page 14- Assignment

Start from the beginning
                                    

Gajeren tsaki ya yi cikin takaici ya ce
"Tun dazu fa muke nan muna jiran mai Office din ya zo amma shiru. Kuma ya kamata a ce ya zo din tunda lokaci tuni ya yi, ga shi dole shi din ne za mu gani kafin komai. Kin san wasu idan Allah Ya daukaka su shi kenan kuma sai abin da mutane suka gani."

Ni ma tsakin na yi ina duban sa,
"Gaskiya dai kam ya taushe hannu. Ga shi sai kara yawa muke..."
Dif bakina ya dinke sakamakon mutumin da na gani a ujilce yana tinkaro inda muke. Na murza idanuwana da kyau, shi din dai ne kuma da alama wurinmu zai karaso. Ban gama shan mamaki ba sai da na ga yana neman bude office din da muke tsaye gabansa tun dazu muna jiran mai shi, wannan ya ba ni tabbacin kenan office din nashi ne...wait, kar dai...
Sai kuma na yi shiru jin ana gaishe shi. Bai kalli fuskar kowa ba ya amsa gaisuwar hade da dan hada hannuwansa guda biyu alamun bayar da hakuri.

Na sha mamaki kwarai ganin yadda yake sakin fuska da mutane, duk wanda ya shiga ya fito sai in ga fuskarsa da annuri. Haka ni ma sadda aka zo kaina na shiga, ko da na gaishe shi cikin sakin fuska ya amsa. A raina na ce shin ko dai ba shi ba ne wanda nake tunanin? Lumshe idonsa da ya yi ya bude a hankali ne ya ba ni tabbacin shi din dai ne wanda na yi wa lakabi da mijin novel, kuma shi ne wanda ya nemi kade ni da mota ya fi ni bala'i, sannan shi ne mutumin da ya dinga zagin mai keke napep din da ya dauke ni a lokacin da ya dan taba masa mota ba da gangan ba.
Amma a yau komai ya sha bamban, wannan wani mijin novel ne mai fara'a da barkwanci, fuskarsa fadade take da annuri sabanin wadancan ranakun da babu digon rahama a cikinta.
'To ko dai akwai abin da yake damun sa ne lokacin?'
Na tambayi kaina.

"UmmulKhair yaya?"
Ya fada bayan ya duba takardata.
Cikin girmamawa na amsa da
"Lafiya lau Sir."
Sannan na kai duba ga kafadar rigarsa. Lieutenant Ahmad Aliyu Turaki ke rubuce, sai na kara shan jinin jikina. Ashe kadan ya hana in yi wa babban Ogana rashin kunya a lokacin da ya kusan kade ni da mota. Amma shi da alama ma bai gane ni ba, don ko kadan babu alamun ya taba gani na ma a fuskarsa.

"You can go."
Ya furta bayan ya yi signing a takardar tawa. Har na mike zan tafi sai kuma na ji ya ce
"Wait..."
Na juyo hade da rusunawa
"Sir?"
Na fada cikin dan tsoro-tsoro gami da shakkun me zai biyo baya. Sai ji na yi ya ce
"Ranar farko, a gaggauce nake saboda matata da aka kai asibiti amma aka ki komawa ta kansu har sai da yaron cikinta ya rasu ita ma kuma ta fara jigata shi ne aka kira ni a waya aka fada min, na tafi a gaggauce zan tafi ke kuma kawai kika afko wa titin ba tare da kin tsaya kin duba ba.
Sannan rana ta biyu, a Kaduna ko?"
Ban ce komai ba face zallar mamakin da ya cika ni, ya ci gaba da cewa
"Wani assignment ne har mun yi nisa da yinsa sai kawai muka yi failing, komai ya tashi a iska, sannan abun haushin aka raunata mana yaron da ya yi shigar mahaukaci a bakin wani Banki. Raina ya baci sosai, kuma na tsaya ina amsa waya kawai mai napep ya zo har inda nake ya kawo min karo. Na tabbata a zuciyarki kina yi min daukan wani mutumi mara mutunci, mai nuna isa da kasaita ko? To ba haka nake ba. Am very simple as you can see."

Tunda ya fara maganar nake bin sa da kallo ina cike da mamaki, don lamari nashi ne sai ido, wai bebiya ta auri makadi.
Sai da ya dire zancensa sannan ya ce
"Ina ta neman ranar da zan gan ki in ba ki hakuri, kwatsam sai ga shi Yayana ya tura min passport da sunanki a kan yana so a yi posting dinki nan Katsina. Sai na gode wa Allah da ban mutu ba ba tare da na bambance miki gaskiya ba, kar in mutu a bi ni da shaidar banza ta rashin mutunci."
Ya karasa maganar yana murmushi.

Gumin fuskata na share duk da dakin cike yake da ni'imtaccen sanyin AC. Wani irin bargon kunya ne na ji ya lullube ni, na dan rusuna ina yi masa godiya sannan ya ba ni izinin fita.

Ban san yadda aka yi ba na dinga jin nishadi, shi ya sa ba a so ka yi judging din mutum ba tare da bincike ba. Ni dai a zuciyata daukar wani mutum dan wulakanci nake yi masa, ashe ko kadan lamarin ba haka yake ba, mutum ne mai saukin hali tare da sanin darajar dan'Adam.
Hakan ya tabbatar min da zai yi min abin da nake so cikin sauki ba ma sai na nemi taimakon Oga Kamaluddeeni ba.

Na dauki akalla wata uku ina zuwa wurin aikin, kafin in bijiro wa Oga Ahmad bukatata, da kuma zargin da nake yi wasu boyayyun al'amurra. Babu bata lokaci kuwa ya aminta, ya goyi bayana tare da tsara duk yadda aikin zai kasance.
Sannan ya dora da
"Kamar yadda kika riga kika sani tun a wurin training, bakidaya aikinmu taking risks ne. Kuma akwai win akwai lost. Sometimes ma sai kina ganin ga ki ga nasara, sai kuma komai ya cabe. Amma duk da haka bai cika cabewar ba kamar sauran ayyuka, tunda mu komai namu na sirri ne; shi ya sa ake kiranmu da 'yan sandan farin kaya. Komai zai faru yana zo mana da sauki saboda kiyayewa irin tamu. Don haka, za ki yi takatsantsan sosai yayin aikinki.
Da farko na tsara za ki tafi ne a matsayin mai larurin mantau, za a tsince ki a can. To kuma ganin yadda komai ya juye a yanzu, ba kowa ne yake saurin taimako ba, ya sanya muka canja shawara. Don haka, za ki je kauyen ne a matsayin 'yar bautar kasa."

***

Kauyen Kanya, karkashin Meshe, ta jihar Katsina.

Tun da na sauka garin na Meshe nake jin faduwar gaba, duk da kokarin da nake yi na ganin na dake, na zama jaruma amma hakan ya gagara, ji nake tamkar ba zan yi nasara ba; har sai da na kira Oga Ahmad, shi ya ba ni kwarin guiwa sosai sannan na samu babur na hau, na shiga kauyen na Kanya da confidence dina.

Da na isa, kai tsaye gidan maigari na ce a nufa da ni. Saboda khakin NYSC da suke jikina ya sa cikin farinciki aka tarbe ni, da alama ba a kaina aka fara zuwa bautar kasa kauyen ba.
Maigari ya sa aka kawo min ruwa da abinci da fura. Ban ci komai ba saboda ina da guzurin lemo da biskit a cikin akwatina. Sai dai ganin ban ci komai din ba ya sanya matar da yaran da aka sauke ni dakinsu, suka dinga bi na da wani irin kallo. Gudun zargi ya sanya na dauki kwanon furar na sha kamar rabinta sannan na yi godiya na dan kishingida ina jin takaicin rashin service din kauyen.



Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now