Page 07- Tushiya...

Začať od začiatku
                                    

Ba zan iya sake yi wa Baba musu ba, don haka na sanya ido kawai aka cike min shi din, ina jin a raina ina nan kan bakana ba zan fasa zama jami'ar tsaro ba, ko ba don fansar abin da aka yi mana ba, ko don dakile yawaitar 'yan ta'adda.

Bayan mun gama komai muka dawo gida, sai da Baba ya ga na shiga gida sannan ya tafi.
Ina shiga na shaida wa Umma komai, cikin farinciki ta ce
"Wadannan mutane karamcinsu har ya yi yawa. Ni ban ma san ta inda zan fara yi musu godiya ba. Wallahi mutanen kirki ne."

Ni dai shiru kawai na yi a raina ina cewa daga gare su ne Ummu ta gaji halayen kwarai.

***
Ban jima da dawowa ba sai ga Anti Maryam ta zo sanye da fararen kaya, da alama daga wajen aikinta take. Da annuri a fuskarta ta shigo tana sallama. Na amsa sannan na shimfida mata tabarma ina gaishe ta.

"Ah lallai jiki ya yi kyau UmmulKhairi. Ji yadda kika fara murmurewa kamar ba ke ba."
Murmushi kawai na yi wanda iyakacinsa bisa lebena.

"Ina Umma ko ba ta nan?"
"Ga ni nan Maryama. Barka da zuwa."
"Yawwa Umma. Ya kwana biyu? Kun ji ni shiru wallahi ayyuka ne sun yi yawa. Ya mai jiki?"

Ta tambaya tana mayar da kallon ta gare ni. Ita ma Umma kallon nawa ta yi ta ce
"Jiki da sauki Sista. Kin gan ta nan yanzu haka daga makaranta take. Babansu ya yi mata rijistar komai lokaci kawai ake jira yanzu."

Cikin fadada annuri Anti Maryam ta ce
"Madalla madalla! Kai alhamdulillah! Wallahi na ji dadin wannan labari Umma. Ashe 'yar kanwata ta kusa cika burinta."
"Ga ta nan ki yi mata fada Sista. Wai ta fasa zama likitar. Yanzu haka fadan da na gama yi mata kenan ta tashi ta cike wai aikin jarida. Ba ma wannan ba, shi kansa jaridar wai ba shi take so ba, so take ta zama jami'ar tsaro."

Zaro ido Anti Maryam ta yi tana sake bi na da kallo.
"Wannan wane irin tunani ne kika yi Khairi? Shin da wa ma kika yi wannan shawarar?"
Na sunkuyar da kaina ina rasa amsar ba ta.

"Me ya sa ba ki kira kin ji daga gare ni ba? Ba har lambar wayata na ajiye a cikin wayar Umma na ce ki dinga nema na ba idan bukatar hakan ta taso? Wallahi ba ki kyauta min ba ni dai Khairi. Me mass com zai yi miki ke da nake son ki zama kwararriyar barrister?"

Na san abin da take so in yi kenan tunda ko kwanaki ta fada min, sai dai ko kadan ni ba ni da wannan burin.
Shi barrister sai jami'an tsaro sun kamo sun kai kotu sannan ne zai yi nashi aikin.
To idan kuma jami'an tsaron ba su kama ba fa?
Ni fa burina kenan, kuma ba na jin akwai wanda zai sauya mini shi.
Na dai yi shiru ina jin su ita da Umma sai aikin fada suke amma ba dauka nake yi ba.

"To ni dai yanzu ba zan fasa abin da na yi niyya ba, maganar scholarship din nan da na fara yi muku, yanzu haka abin da ya biyo da ni nan kenan daga asibiti. Jiya Abban su Rukayya ke ce min a yi kokari a ga dai ta samu O level mai kyau, shi da kansa zai tsaya ganin an samu scholarship din zuwa Sudan ko Egypt ta hanyar mai kudin nan Alhaji Kabiru Kaita. Don bana kam ana kyautata zaton zai tsaya sosai wajen bayar da admission din tunda siyasa ta kusa, kuma yana so ya ci."
Ta dube ni ta ce
"Law din nan dai shi za ki nema da yardar Allah kuma za a dace. Babu abin da ya dace da ke face shi."

Umma ta saki murmushi ta ce
"Na ji dadin wannan bayani Maryama. Da ma ni dai wallahi sam ba na son wannan aikin jaridar. Allah Ya sa a dace."
"To amin Umma. Sai mu kara dagewa da addu'a, da yardar Allah nasara na nan tare da mu."
"To Allah Ya amince."
Umma ta furta tana mikewa ganin Anti Maryam din ma ta mike.

"Ni zan wuce Khairi. Allah Ya kara sauki."

Kasa-kasa na amsa da amin, domin ni dai ina nan kan bakana, zan kuma ci gaba da binciken yadda za a yi in samu aikin jami'ar tsaro ko da karami ne, har sai lokacin da na dace.

***
Bayan fitar Anti Maryam na koma daki na kwanta kawai na hau tariyar rayuwar duniya, silar kawancenmu da Ummu, kawancen da ya rikide ya zama 'yan'uwantaka...

TUNA BAYA

Ranar da aka haifi Sadiya, a lokacin Abbanmu yana raye, na hada kai da guiwa kurum saboda Umma ta ce sai na je islamiyya, ni kuwa irin abun nan na an haihu a gidanmu, sai cewa na yi babu inda za ni ai kuwa Umma ta hau duka na ta ce dole sai na je.
Cikin rarrashi Abbana ya kira sunana, na dago kan nawa sai gani na yi yana yi min murmushi.

"Maza tashi mu je in raka ki islamiyya tun kafin Ummanki ta kara miki wani dukan. In ban da abin ki Khairi, wa ya fada miki ana fashin makaranta babu dalili? Ko kina so malaminku ya zane ki?"

Na gyada kai.
"To idan dai ba kya son duka da dorina tashi mu tafi yau da kaina ma zan raka ki, sannan har da kudin shan alewa ma ga su nan."

Na kuwa saki murmushi har da tsalle na bi bayansa muka kama hanyar makaranta.
Ta gaban gidan su Ummu muka gitta, a lokacin sabon gida ne wanda ko kammala shi ba a yi ba don ko shafen simintin waje ma ba a yi ba.

Sai ga Baba ya fito hannunsa rike da Ummu, ganin za mu gitta ta gaban gidan ya sanya shi mika wa Abbana hannu suka gaisa.

"Barka da dawowa unguwarmu Mallam. Na ji labarin dawowar taku ai mako daya da ya wuce."
Abba ya furta da fara'a yana duban Baba.

"Eh wallahi. Ni kuma kullum uzuri. Ina ta son yin sallama ga makwabta a gaisa dai har yanzu Allah bai nufa ba."
"To ai da ma komai sai Allah Ya bayar da iko ake yi."

Baba ya dube ni da busasshen hawayena ya ce
"Yanmata ya aka yi ake kuka?"
"Makaranta ce wai ba za ta ba tunda Ummanta ta haihu yau. Shi ne ta sha duka. Ni kuma na ce yau da kaina ma zan raka ta."

Baba ya dafa kaina yana murmushi ya ce
"Ma shaa Allah! Watakila ma makaranta guda ce za mu je. Ni ma waccan islamiyar ta can kasa zan kai ta. Tun jiya na je na mata komai shi ne aka ce yau ta fara zuwa."
"Ka ga faduwa ta zo daidai da zama kenan. Bismillah sai mu tafi ai ko? Khairi, kama hannunta mu je."

Jin Abba ya kira ni da Khairi ya sa Baba tambayar sa sunana ya fada masa.
"Wannan fa shi ne babban katari. Ka ga ita ma wannan sunanta kenan UmmulKhairi. Amma ita Ummu ake kiran ta."

Hirar su suke ta sha yayin da ni da Ummu muka rike hannun juna ina ba ta labarin jaririyar da aka haifa mana fara kyakkyawa.

Wannan ranar ita ce mafarin komai, ita ce silar kawancenmu, ita ce silar amincin da ya kulla tsakanin iyayenmu, wanda kuma mu ne silar bunkasuwarsa.


Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now