Page 06- From God We Are...

Start from the beginning
                                    

"Tashi mu je Khairi. Sai hakuri kin ji."
Tamkar tana magana da dutse, na dai ji ta, amma kwata-kwata hankalina bai kai ga abin da take nufi ba.
Sai da ta kama ni ta mikar sannan ma na gane ashe nufinta in tashi mu tafi.

"Allah Ya kara sauki UmmulKhairi. Please try your best ki yi kuka. Barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa."
Dakta Gumel ya fada cike da tausayi. Ban amsa masa ba muka bar office din, zuciyata na karyata batun mutuwar Ummu. In bancin kar in yi sabo da sai in ce ban shirya rabuwa da ita ba, bai kamata a ce ta tafi ta bar ni ba tare da dukkan burikanmu sun cika ba.

A kan hanya Anti Maryam ta yi ta kokarin kwantar mini da hankali amma ko uffan na kasa ce mata. Ta dai ci sa'a ina daga mata kai amma na gagara furta kalma guda ma.
Har muka isa gida ban ce komai ba, sai da muka shiga gida ta hau labarta wa Umma duk abin da ya faru, a lokacin ne kuma na rushe da kakkarfan kuka bayan na fada jikin Ummata.
"Umma...ashe Ummu ta rasu, ta tafi...ta bar ni..."
Na so in kara da wani abun amma kuka ya ci karfina, tunanin rayuwa da komai nake, tunanin yadda zan ci gaba da rayuwa ba tare da Ummu ba.

A hankali take dan bubbuga bayana,
"Sai hakuri Khairi, Ummu ta tafi inda ba a dawowa, inda da ni da ke duk sai mun tafi. Ki sanya wa zuciyarki salama, da sannu zai sanyaya miki komai AzzawaJalla. Ki yi addu'a, ki fada maSa komai, Shi ne mai maganin kowacce irin damuwa kuma zai magance miki. Duk wannan kukan ba zai amfana miki komai ba face wata cutar da zai janyo miki. Kina ganin ba lafiyar kirki kike da ita ba, ba na so ana tufka kina warwara."

Suka hadu ita da Anti Maryam suna ta ba ni maganganu amma ina! Na yi nisan da ba na jin kira. A yanzu dai babu wata magana da za ta kwantar mini hankali a kan mutuwar Ummu. Shakuwa da soyayyar da ke tsakaninmu ta fi karfin in manta da ita a dan lokaci kankani.

***
Kamar da wasa sai da na cinye wata biyar cif a cikin larurin depression, depression ciwo ne irin wanda damuwa ke haddada shi, sannan shi ba shi da kwayar magani ko allura. Mun yi zarya wajen Dakta Gumel fiye da sau bakwai amma babu wata nasara sai dai sauki daga wurin Allah. Tun abun ba ya tsorata su Umma sosai har ya fara.
Idan na zauna ni kadai ma magana nake yi ina ambatar sunan Ummu, ina tuna wadansu moments na rayuwarmu.
Rayuwa ta yi mini juyin waina a kasko, ko kuma dai juyewar gawayi zuwa danyar wuta.
Duk wanda ya san ni a baya idan ya dube ni a yanzu ya san an samu sauyi, irin mummunan sauyin nan wanda ba a so.
Ga wata irin rama da na yi jikina duk kashi, ni da ma ba wata kiba ce da ni ba, balle kuma a yanzu da komai ya karasa lalace min.

***
Zumbur na tashi zaune ina share kwallar da ta zame min tamkar ibada kullum sai ta zubo min ba dare ba rana. Zaman hijabin jikina na gyara, sannan cikin rashin kwarin guiwa na mike.
A tsakar gida na samu Umma tana wanki su Safra na makaranta.
Ta dago kanta ta dube ni ta ce
"Khairi sai ina?"
Na kara sharce kwallar da ke sake zubowa,
"Gidan su Ummu zan leka."

Ajiye rigar da take wankewa ta yi ta zo inda nake, ta dafe kafafa ta ce
"Idan kin san zuwa gidansu zai kara tayar da hankalinki ki yi hakuri kar ki je Khairi, kin ga muna dan murna jikin naki ya fara kyau kuma kar ki je angulu ta koma gidanta na tsamiya. Ba na fatan ki sake shiga irin wancan mummunan yanayin, duk da a yanzu din ma ba gama warkewa kika yi ba."

Na kirkiro murmushin da bai da alaka da nishadi na ce
"Tun da Ummu ta rasu ban leka gidansu ba, amana ba ta ce haka ba Umma. Ba na so Mama ta zaci don rashin Ummu ne ya sa ba na shiga gidan."

"Maman Ummu ta san larurin da yake addabarki tunda har ganin ki tana shigowa yi, ko jiyan nan dai ta zo. Ba za ta yi wani zaton na daban ba."
"Duk da haka dai Umma ina son zuwa in gaishe ta da kaina."

Ta saki ajiyar zuciya ta ce
"Shi kenan. In dai hakan zai faranta miki rai babu komai ki je. Ki ce ina gaishe ta."

"Za ta ji Umma."
Na furta cikin sassanyar murya, sannan na kama hanya na tafi gidansu. Ba wata tafiya mai nisa ba ce, duka-duka ba zai wuce gidaje uku ba ne a tsakaninmu, nan da nan na isa.
Na samu Baba zaune kan tabarma, Mama na dama masa fura.
Da annuri suka tarbe ni ni ma na kirkiri nawa annurin duk da bai kai ciki ba.

Har kasa na tsugunna na gaishe su kamar yadda na saba, Mama ta ce in je in dauko kujera in zauna amma Baba ya ce sai dai in zauna a kan tabarmarsa. Babu musu na zauna.
"Yaya karfin jikin naki? Jiya na leka Ummanku ke fada min bacci kike ai."
"Eh Mama, ta fada min. Jiki ya yi sauki."
"To alhamdulillahi ai haka ake so. Sai ke ma ki kara kokarin fitar da komai daga ranki kin ji? Allah shi ke bayarwa kuma Shi Yake kwacewa a duk sadda Ya so. Addu'a za mu yi Allah Ya toni asirin azzaluman, ita kuma UmmulKhairi Allah Ya haskaka makwancinta Ya kara mana hakurin rashinta."

Sai kawai na ji hawaye na bin kumatuna. Har yanzu na kasa sabawa da rashin Ummu, da zarar an min zancen mutuwarta sai na ji komai tamkar sabo. Na dukar da kaina kasa ina shawarar hawayen.

"Idan kin koma gida ki dauko mini kananan hotunanki, sannan ki rubuta sunanki a bayan kowanne hoto. In shaa Allahu gobe zan je in biya miki kudin jarabawa kamar yadda na yi alkawari. Da NECO ce da JAMB kadai, amma tunda babu Ummu, sai in yi amfani da kudin natan a biya miki duka biyun, WAEC da NECO din kenan."

'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!' Na hau maimaitawa a cikin zuciyata. Wannan maganar ta Baba ji na yi tamkar ya zuba mini narkakkiyar dalma a cikin kunne.

"Ki daina kuka diyata. Ko da ma can duk daya na dauke ku ke da ita, ballantana kuma a yanzu da babu ita. Ina rokon Allah Ya cika miki burikanki kamar yadda kuka fara ke da 'yar'uwarki..."
Shi kansa Baban cikin rauni yake maganar wanda har ya dakata ba tare da ya kai inda yake son tsayawa ba.


Amrah A Mashi❤️

DARE DUBUWhere stories live. Discover now