"Asad me kake yi a nan?." Jin tambayar daga bayan sa ya saka shi ya juya yaga Hajiya a tsaye tana kallon sa. Mamaki ya kama shi uwar gidan sarki mai zai kawo ta wajan a wannan lokacin da ba kowa yake yin hanyar ba..?  amma bai nuna mata  mamakin sa ba sai ya goge idanun sa yace, "babu komai" yana fad'a ya wuce tabi bayan sa da kallo ta murmusa kafin ta bar wajan.

         D'aki Asad ya koma yana zagaye hankalin sa a tashe matuk'a, bai tab'a jin tashin hankali akan abubuwan da suke faruwa ba kamar yadda yake ji yau. Babban tashin hankalin sa sunan Hydar da yaji suna ambata kenan duk rashin lafiyar da yake yi sune suka jawo hakan?. Suna saune suke kwantar dashi dan rashin imani..? Su waye ma a tak'aice....?. Kama k'ugu yayi ya furzar da iska mai zafi yana sauke numfashi, "me ya kai Hajiya wajan a yanzu?" Ya tambayi kansa nan ma babu amsa ya had'd'iye  saliva a jikin sa yake jin lokaci yayi da kowa ya kamata yasan waye Asad.

*Bayan wasu kwanaki.*

"Malam dan Allah in ka fita ka biya ta wajan sarkin d'ori ku tawo da ko yaron sane yazo a duba k'afar Rauda. Gashi dai ta samu lafiya amma k'afar ta nakasa yazo ya gani in akwai abinda za'a yi" Umma ta fad'a tana kallon Baba. Baba da ya gama saka takalmi yace, "in aka d'auko sarki d'ori ke zaki biya shi?."
Umma ta buɗe baki tana kallon sa shima yana kallon ta yace, "Nidai bazan biya ba in zaki biya yanzu za'a tawo dashi."

Umma tace, "Shikenan azo dashi sai na biya d'in."
"Zab'i mai kyau, kuma kin san dai biyan da tsada tunda gida zai zo sai ki tanadi kud'i."
"Zan bayar ko nawa ne."
Ya k'are mata kallo yace, "Da uwar kud'in ki a k'ugu amma asahana in ta kare sai a turo min yaro" ya fad'a yana fita ta bishi da kallo kawai.

Ba jimawa ya shigo yace, "ku gyara gashi mun zo dashi" ya fad'a yana komawa suka shigo tare aka shiga d'akin Umma ya fara duba k'afar Rauda da take zaune.

Mai gyaran k'afar da yake kusa da Rauda yana duba k'afar ta ya kalli Umma da Baba da kuma Inna yace, "Akwai sauran gyara a k'afar nan tata dole sai dai ayi mata aiki." Baba yace, "Aiki kuma?."
"Eh aiki Baba, amma kuje asibiti ayi hoton k'afar a kaiwa likita shi kuma zaiga inda za'a gyara sai ya fad'i kud'in ku biya." Umma ta girgiza kai tace, "to kuma zata iya tafiya?."
"Eh zata iya amma sai dai a bata sandina guda biyu, inda dama yanzu kuje asibitin ayi gaggawar duba k'afar tata in ba haka ba zai zama silar da za'a ce zata nakasa gabad'aya."

Baba yace, "to mun gode." Fita yayi Baba ya kalli Umma yace, "ke kina da kud'in zuwa asibitin ne?." Umma ta girgiza kai a raunane tace, "bani dashi. Suke nan na hannuna kuma na bayar yanzu."  D'an k'aramin tsaki yaja ya kawar da fuska gefe yna jin haushin ciwon nata kawai za'a saka shi kashe kud'i kafin ya fita. Inna tace, "abu kad'an zai zama sanadi." Umma tace, "Allah ya yaye." Rauda dai tana jin su jikin ta yayi sanyi ta tabbatar ta rasa k'afar ta kenan sabida tasan kud'in aikin da za'a fad'a babu mai kud'in da zai iya biya.

Baba ya dawo yace, "ta tashi ta d'auki sandinan muje yanzun." Ba musu Umma da Inna suka kama ta ta tashi aka bata sandinan nata tana tafiya dasu a hankali har suka fita suka ga taxi Baba ya taro aka kwantar da ita a baya Umma ta rab'a ta zauna Baba ya shiga gaba suka tafi. Wajan hoton k'afar suka fara zuwa suka hau layi abin mamakin Baba baiyi k'yashi ba ya bada kud'in akayi hoton suka shiga asibiti wajan likita. Tun safe suke zaune har azahar layi bai zo kansu ba duk sun gaji da zama gata ita kuma a kwance tunda k'afar ba kwari tayi ba.

        Bayan azahar layi yazo kan su suka shiga duka su ukun aka bawa likitan hoton yana kalli hoton sosai ya gama Nazarin duk abinda yake jiki ya juyo ya kalle su bayan ya gama dubawa yace, "Akwai wani k'ashi da ya tsage a k'afar ta yanzu kuma nama ya shiga tsakiya jini ya shiga sosai dole sai anyi aiki zan cire an had'e wannan k'ashin." Baba yace, "to kuma aikin yana kaiwa nawa?." Likitan yace, da yake bani zanyi aikin ba amma dai gaskiya yana kaiwa miliyan d'aya da dubu d'ari biyu koma yaje miliyan biyu. Aikin babba ne gaskiya dan ba'a jima da fara yin sa Nigeria ba Egypt ne da Germany da India kawai suke yin sa." A tare gaban su ya fad'i suka kalli juna Rauda idanun ta tuni sun wanke da hawaye Umma tace, "Tabd'ijam."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now