020

61 5 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*020.*

         Lokacin da Asad ya shiga falon Mama ya tarar da Hydar a zaune ya rame sosai yayi haske jikin sa babu k'arfi sai idanu da yake bin mutane dashi, a nutse ya tako ya zauna kusa dashi ya kalli Mama da take zaune itama a gefen sa sai Suhaima da take tsaye yace, "Sannu Hydar, ya kake ji?."
Maganar sa bata fita sosai yace, "da sauk'i."

"Asad ka taimaka masa yayi wanka ya sai yaci abinci." Asad ya kalli Hydar yace, "Zaka iya tashi?." Kai ya d'aga alamun eh ya rik'e shi suka tashi zuwa d'akin da yake kwance. A nan yayi wanka aka kawo masa kaya ya saka yayi sallah ya fara cin abinci. Suna zaune zagaye dashi ya gama cin abincin ya sha magani kana ya kalli Asad yace, "Akwai yarinyar dana buge deaf a tambaya min Dr Yasir tana ina."
Ran Mama ya b'aci jin da abinda ya fad'a tace, "na saka an sallame ta." Hydar ya kalli Mama ya dafe kansa yace, "meyasa Mama? Yarinyar tana buk'atar taimako sai an mata aiki fa."

Mama tace, "kuma indai nice na haife ka dole ka bar maganar ta ba, bana son sake jin zancen wata wacce ka buge a bakin ka ya wuce ka manta da babin ta." Zaiyi magana Asad ya d'an ja rigar sa sai yayi shiru ya saukar da kansa k'asa baice komai ba. Tsaki Mama tayi tace, "kana farkawa ka rasa da abinda zaka tashi sai maganar wata banza y'ar talakawa, kenan daman da ita ka kwanta a ranka da yake baka da hankali, na tsani yarinyar tsana mai muni." Babu wanda ya ce komai ba sukayi shiru zuwa lokacin magariba ta kawo kai.
Tare suka fita da Hydar sai a sannan jama'ar masarautar suka san da farkawar sa aka dinga gaishe shi zai amsa duk da ba wani k'arfi ne dashi ba.

Bayan an idar da sallah suka je wajan mai martaba daga nan suka dawo apartment d'insu. Aliyu baya nan Hydar ya zauna a falo jin jiri yana d'aukar sa yana sauke numfashi yace, "Deaf ban san inda zan ga yarinyar ba, basu da kud'in da za'a yi mata aiki in wani abun ya same ta Allah sai ya saka mata."
"Relax" abinda Asad yace kenan daga nan bai kuma cewa komai ba.
"Deaf ina cikin damuwa tunda na tashi itace tazo raina, ta yaya zan ganta ina so na ganta wallahi."
Wani irin kallo Asad yayi masa jin abinda yace nan take sai gaban sa yayi mugun fad'uwa amma bai nuna masa ba bai kuma yi masa magana ba.
Hydar ya yi shiru amma zuciyar sa gabad'aya tana ga tunanin inda zai ganta gabad'aya hankalin sa yana kanta gashi bai san inda zai nemo ta ba abin duk ya dame shi.

        Washe gari Asad tare da Hydar suka fita zuwa company dan ya samu k'arfin jikin sa suna tare har yamma, a yamman aka kawo masa passports d'insu Rauda an buga musu visa ticket ya rage a siya, bayan tafiyar wanda ya kawo passports Hydar ya kalle shi yace, "Passports d'in su waye?." Bai bashi amsa ba sai da ya gama abinda yake yi ya tashi suka shiga mota suka bar company.
Gidan su Rauda ya wuce Hydar bai san gidan ba yaga dai sun tsaya a k'ofar gidan ya kalli Asad yace, "Ina ne nan?."

Bai magana ba ya sauke glass d'in motar nan ya hango Khalil yana ta wasa ya yafito shi da hannu ba musu ya k'araso Asad ya kalle shi yace, "Abban ka yana nan?." Khalil yace, "Eh yana nan."
"Jeka kace ana sallama dashi" yana fad'a ya ja bakin sa yayi shiru Khalil ya shiga cikin gidan.

Hydar yace, "Asad ban gane ina muka zo ba fa." Kallon sa yayi baice masa komai ba a lokacin Baba ya fito ganin haka ya saka Asad ya fito daga motar shima Hydar ganin ya fita shima ya fito lokacin Baba ya k'araso, hango Asad sai ya washe baki ya k'araso da sauri yana zuwa yace, "Barka da zuwa ranka ya dad'e." Murmushin k'arfin hali Asad yayi suka gaisa da Baban Hydar ma ya gaishe shi kafin Asad yace, "Shine Hydar wanda ya buge ta jiya ya farka daga rashin lafiya" ya fad'a yana nuna masa Hydar.

Baba ya washe bakiyace, "Allahu Akbar! Naso na gane fuskar sa yadda ya rame ya saka ban gane shi ba, sannu Hydar ya jikin ka?." Fad'ar hakan nan take sai Hydar ya gane shi shima yace, "Alhamdulillah, ya jikin ta?."
"To jiki da sauk'i dai za'a ce."
"Zan iya ganin ta?" Hydar ya fad'a yana kallon Baba.

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now