017

58 5 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*

             ©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*017.*

           Rauda ta jima tana bacci sanin ba sallah zatayi ba ya saka Umma bata tashe ta ba sai bayan azahar ta farka ta firgice, ganin ta a d'akin Umma ya saka ta raba idanu tana sauke ajiyar zuciya ganin mafarkin da tayi ba gaske bane ba. Mafarki tayi sun had'u da Aliyu ya kai ta wani waje tana ta bashi hak'uri yak'i ya hak'ura bai kai ga yi mata komai ba ta farka shiyasa hankalin ta gabad'aya yake a tashe.
Duk ta jike da gumi tana shafe fuskar ta Khairi ta shigo d'akin tana fad'in, "Umma ta tashi."

Kallon Khairi tayi kafin tace, "k'arfe nawa?." Khairi tace, "K'arfe biyu." K'aramin tsaki ta ja Umma ta lek'o d'akin tace, "To Rauda zan fita su Khairi zasu je makaranta ki kula da gidan."
"Ina zaki je Umma?."
"Zan koma yiwa matar nan gaisuwa, daga nan kuma zanje gidan Baba Malam mu gaisa."
"A dawo lafiya." Sakin labulen Umma tayi ta fita daga gida.

Rauda ta kalli Khairi da take shiryawa tace, "Khairi in zaki tafi makaranta ki biya gidan su Habiba kice dan Allah nace tazo ina neman ta Umma bata nan." Khairi ta amsa da to ta gama shiryawa ta fita. Gidan shiru hakan ya bata tabbacin d'akin su Rahma ma basa nan kenan ta fito daga d'akin ta zauna a kan kujerar ta a tsakar gida inda babu rana.

Yunwa take ji sosai amma baza ta iya cin abinci ba sai tayi maganin matsalar da ta d'aukowa kanta sannan zata samu abinci ya iya zama a cikinta, tana nan zaune taji sallamar Habiba ita da Walida sun shigo a tare. Amsawa tayi suka k'araso suka zauna a kan tabarma Habiba tace, "Naga fuskar ki a kumbure."
"Bacci nayi" ta bata amsa tana yatsine fuska.

Habiba tace, "y'ar hutu. Lafiya kike nema na?." Rauda tace, "Yan uwa ina cikin matsala ne." A tare suka had'a baki wajan fad'in, "Wacce irin matsala kuma?."
Shiru Rauda tayi tana kallon su kafin ta kwashe duk abinda ya faru tayi ta fad'a musu kafin ta d'ora da fad'in, "tunda kika ce min har fyad'e ya yiwa y'ar sarkin Zamfara na tsorata ku taimaka min dan Allah."

Girgiza kai suke yi cikin mamaki da tsoro Habiba tace, "Mahaukaci kika ce masa Rauda? Tabd'ijam na rantse da Allah bai k'yale ki ba kina nan a zuciyar sa sai ya d'auki mataki a kan ki, ya yiwa yar masu kud'i da mulki balle irin mu?." Sai ta fashe da kuka tana fad'in, "Dan girman Allah ku taimaka min ku nema min mafita wallahi tsoron sa nake ji, ni ko zuwa ne zanyi na bashi hak'uri indai zai yafe min."

Habiba tayi shiru tana tunanin m a fita kafintace, "mafita d'aya ce kawai abinda za'ayi zuwa zamuyi mu samu Asad ki fad'a masa duk abinda ya faru tunda a gaban sa akayi, ki sanar dashi tsoro kike ji kuma kinyi dana sanin yi masa rashin kunya dan Allah ya bashi hak'uri kar yayi maki komai, in anyi sa'a zai iya k'yalewa in Asad d'in ya saka baki."

Walida tace, "To kince sai ya kwana uku bai fito ba a ina zamu gan shi?." Habiba tace, "yana sadaka ai da kansa ranar juma'a bayan masallaci indai yana k'asar nan, ranar zamu je masa in ba ranar ba wallahi bamu da ikon ganin sa."
"Juma'a yayi nisa Habiba, kafin juma'ar zai iya sakawa ayi min wani abun, dan Allah a canja shawara. Ni tsoron abinda zai min nake yi bawai tsoron sa ba, ga Ummana bana so ta shiga wani yanayi mara dad'i a kaina shiyasa hankalina ya tashi sosai" Rauda ta fad'a cikin tashin hankali tana hawaye tana kallon su.

Cikin kwantar da murya Habiba tace, "Na rantse da Allah Rauda da ina da damar ganin Asad a yau zamu je wajan sa amma ban isa ba, Fulani ta saka an k'arawa b'angaren su tsaro sabida abinda ya faru dashi kwanaki kusa da wajan ma baki isa kaje ba sai da dalili. ki bari sai ranar jama'ar in Allah ya nuna mana sai muje ki same shi na tabbatar bazai bari a cutar dake ba, Kafin ranar ki ta addu'a Allah zai kawo miki sauk'i."

"Habiba in ya yi min wani abun na shiga uku dan Allah ku taimake ni. Ba kaina nake ji ba Ummana nake ji, abinda Baba zai yiwa Umma shi nake jin tsoro" ta fad'a cikin kuka sosai. Tausayi ta basu suka dinga rarrashin ta Habiba tace, "Allah yana tare dake wallahi bai isa ya cutar dake ba. Amma zan je yanzu in naga yana nan zan roƙe shi zance masa zan kawo ki ki masa bayanin komai in yaso sai naje na dawo muje wajan sa dake."

KWANTAN ƁAUNAWhere stories live. Discover now