006

128 7 0
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
        FitattuBiyar 2023.

           ©️ *Nana Haleema.*

*Book1
*006.*

A guje Ummulkhairi ta tsallako a lokacin Hydar yayi inda take kwance hankalin sa a matuk'ar tashe ya d'auke ta cak ya saka a bayan mota bai ma kula da Ummulkhairi da take kuka ba ya shiga motar ya ja a guje. Kasancewar titin babu jama'a babu wanda ya lura da abinda ya faru Ummulkhairi ta kwasa a guje ko ta kan kwanikan abincin bata bi ba ta tafi gida.

Babban asibitin kud'i na garin ya wuce da ita jikin sa gabad'aya rawa yake fuskar ta ta tasa lokaci d'aya har lokacin bata motsin kirki, k'ara gudun motar yake yi har ya isa asibitin nan take yayi waya akayi sa'a likitan da yake nema yana nan aka fito a guje aka d'auke ta aka wuce ciki. Gabad'aya ya kasa nutsuwa yana zaune a office d'in Dr amma zuciyar sa bugawa take da sauri.
Sun jima matuk'a a kan ta kafin Dr ya shigo yana ganin sa ya kalle shi alamun k'arin bayani nake nema, Dr ya zauna yace, "Prince ta samu karaya a k'afar ta munyi x-ray na k'afar mun gano k'ashin da yake rik'e k'afar ta baya wanda ya kasance bashi da k'wari ya karye shima, k'afar ta d'aya lafiya take sai dai buguwa da tayi amma d'ayar gaskiya tana da matsala munyi iya abinda zamu iya a yanzu in abin baiyu ba gaskiya dole sai anje Egypt."

Hydar ya sauke numfashi ya lumshe idanun sa ya bud'e ya kalli likitan yace, "Yanzun jiran me za'a yi baza a tafi can ba?." Dr yace, "dole za'a jira ciwon ya warke in ka lura karaya ce mai jini ma'ana karaya ce mai had'e da ciwo, in ciwon ya warke in abinda muka yi  bai na shine za'a fitar da ita." Baice komai ba ya mik'e ya fita ya shiga d'akin da take yana kallon fuskar ta da ta kunbura amma kamannin ta basu gushe ba.

Kallon ta yake k'irjin sa na bugawa ga k'afar ta a d'aure haka goshin ta ma an manne shi sabids ciwon da ta samu, numfashi yake fesarwa dana sanin fitowar sa daga gida gabad'aya ta damalmale masa zuciya ya fito daga d'akin suka had'u da Dr d'in a k'ofar d'akin yace, "A nemo family nata but bana so a sanar dasu nine na kad'e ta, a tabbatar musu da za'a tsaya ta samu lafiya ko nawa ne za'a kashe" abinda ya fad'a kenan kawai ya fita daga wajan bai jira ma yaji mai likitan zai ce masa ba.

A can gida kuwa a guje Ummulkhairi ta shiga gida tana fad'in, "Umma! Umma!!" Umma da take tsakar gida ta kalle ta tace, "Khairi lafiya wannan wanne irin kira ne?." Jikin ta har rawa yake tace, "Anty Rauda! Umma Anty Rauda" abinda take maimaitawa kenan tana haki alamun ta sha gudu.

Hankalin Umma ya tashi ta k'araso kusa da ita tana fad'in, "me ya sami Rauda d'in? Tana ina?, me ya same ta?."
"Wani ne ya kad'e ta a mota tana kwance bata numfashi Umma, jini yana ta zuba daga jikin ta Umma" ta kuma fad'a har lokacin bata dawo dai-dai ba tana hakki.

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, wani ya kade ta fa kika ce Ummulkhairi?." "Eh Umma, ya d'auke ta a mota sun tafi."
"Hasbunallahu wani'imal wakil, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!" Abinda Umma take fad'a kenan jikin ta na rawa itama Anty Babar su Rahma kenan ta fito itama tana salati tace, "To banda shirme kuma irin naki sai ki bari su tafi baki bisu ba?."

"So nake nazo na fad'a muku, Umma Anty Rauda jikin ta duk jini" ta k'arasa fada tana fashewa da kuka ta zube a wajan. "Kukan me nake ji haka?" Baba ya fad'a yana shigowa yana kallon su. Ba wanda ya iya magana yace, "Ya naga kunyi cirko-cirko kamar wad'an da aka yiwa mutuwa?, ke ina Rauda?."

"Baba wani mai babbar mota ne ya kad'e ta ya d'auke ta suka tafi a mota." Baba yace, "Ya kad'e ta fa kika ce? A ina ya kad'e ta?, waye shi?."
"Baba ban san shi ba, ya dai kad'e kuma ya saka ta a mota sun tafi."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" abind Baba ya furta kenan ya fita daga gidan hankalin sa a tashe.

Dukka mutanen gidan Hankalin su a tashe yake sun kasa koda zama musamman Umma Khairi kuma har lokacin kuka take sosai hankalin ta ya kasa kwanciya tunda a gaban ta akayi, Baba ya jima da fita ya dawo Umma tace, "Malam an same ta?." Baba yace, "ban samu komai, inda aka buge ta d'in tabbas ga jini nan har yanzu yana wajan amma babu wanda yazo ya bada sanarwa koda y'an uwan ta zasu neme ta."

KWANTAN ƁAUNADove le storie prendono vita. Scoprilo ora