025

92 8 3
                                    

*KWANTAN ƁAUNA*
Fitattubiyar 2023

©️ *Nana Haleema.*

*Book 1*
*025.*

Yaya Ummi tayi shiru alamun tunani kafin ta sauke numfashi ta kalli Rauda tace, "Tabbas Anas ba abin yarwa bane ba, in muka watsar da Anas bamuyi adalci ba." Rauda rausayar da kai tace, "Abinda na gani nima kenan, zan iya auren Anas na zauna dashi duk da bana jin sonsa a zuciya ta har gobe, amma halayyar sa da yadda yake nuna tsantsar so a gare ni zata saka naso shi nan gaba."

Yaya Ummi tace, "Haka ne Rauda, ki cigaba da addu'a kedai kawai duk abinda ya zama alkhairi Allah ya zab'a maki."
"Ina yi sosai." Yaya Ummi zatayi magana kenan aka bud'e k'ofar aka shigo Baba ne da kuma maza guda biyu a bayan sa ganin su waye ya saka Yaya Ummi tashi tsaye tana fad'in, "Sannun ku da zuwa."

D'aya daga cikin su yace, "Yauwa Ummi, ya mai gidan naki?." Yaya Ummi tace, "Alhamdulillah." Gaisawa sukayi har Rauda kana d'aya daga cikin su yace, "Jiya nazo wucewa ta k'ofar gidan ku na tarar an baje gidan gabad'aya ya koma fili ana sabon gini na bulo, daman kuma ina ta ji a gari ban tabbatar ba sai dana gani da ido na; sai yanzu mahaifin ku yake shaida min abinda yake faruwa."

Kawu Badamasi yace, "Ke daman kin san shi ne tun a baya har ya furta yana sonki?." Rauda ta girgiza kai tace, "A'a Kawu bansan shi ba." Ya girgiza kai yace, "ikon Allah kenan, abinda baka tsammaci faruwar sa ba sai kaga ya faru." Kawu Lawan yace, "To ke meye a ranki kenan?." Rauda tayi shiru bata amsa ba Baba yace, "ita bata yanke hukunci ba har yanzu; akwai wani yaro Anas da yake sonta yana hidima da ita sosai ina tunanin shine a ranta."

Kawu lawan yace, "ba d'an gidan Alhaji Tasi'u mai farin gida ba?." Baba yace, "Shi." Kawu lawan yace, "to ai ni Alhaji Tasi'un ya aika min da mutane guda biyu na d'auka ma ko neman auren ta suka zo wajena sai suke shaida min shine ya turo su yace a sanar damu ya yiwa d'ansa mata kar a jishi shiru kwana biyu zai masa aure ne. Sun shaida min bazasu iya had'a ido da kai ba sabida kunya shiyasa suka je wajena kai tsaye." Baba yace, "ikon Allah! Amma baka sanar dani ba."
"Na d'auka shi yaron ai ya sanar dakai ko ya sanar da ita."

Baba ya girgiza kai ransa fari karr har hakan ya bayyana a kan fuskar sa yace, "basu zo inda nake bama shiyasa kwana biyu shiru babu motsin yaron, Allah sarki ni shaida ne yana son Rauda amma da alama iyayen sa basa son alaqar su tare shiyasa suka yanke wannan hukuncin, Allah ya zab'a mafi alkhairi." Kawu Badamasi yace, "Amin. Baza muyi saurin cewa iyayen ne basa son alaqar ba wataƙila alqawarin aure ne sukayi zasu had'a shi yaron bai san dashi ba shiyasa yake neman Rauds. Rauda karki yiwa kanki dole dan ganin kud'i ko dukiya ko kuma sarauta, yanzu maganar Anas ta k'are kinji duk abinda yake faruwa da kunnen ki, kar kice tunda babu batun Anas yanzu bara na amince da d'an sarkin kar kiyi haka kiyi addu'a ki kuma bi zab'in zuciyar ki."

Kai ta girgiza alamun gamsuwa Baba yace, "Ai ana ta addu'a duk inda na bayar ayi mana istikhara sai kaji ance auren sa da ita alkhairi ne ba kad'an ba. Daman Anas d'in nan nake ji tunda abin yazo da haka wallahi nafi kowa farin ciki ya auri zab'in iyayen sa itama ta auri Asad d'in shikenan an huta." Kawu Badamasi yace, "A'a, ka barta ta zab'i abinda take so dan Allah kar abin duniya ya rufe mana idanu mu kaita inda zamu zo muna dama mun sani bamu kaita ba, dan ni Allah ya sani wani lokacin bana yi mata sha'awar shi yaron mai martaba sabida abinda zata tarar ba abu kad'a bane. Na farko da ga babar sa, na biyu ga sauran jama'ar gidan, na uku har abada gidan sarauta bazasu tab'a girmama ta ba k'ask'ance zata rayu dan su gidan sarauta indai ba y'ar gidan sarauta ka d'auko ba talaka sunan ka balle kuma Rauda."

Umma da take zaune tace, "tun a yanzu ya fara bayyana kansa dan mahaifiyar yaron bata jima da fita daga gidan nan ba tayi b'adda kama ta shigo tana yi mata gargad'! akan auren d'anta, har da ikirarin in ta aure shi sai ta b'atar da ita daga duniya, ina dalili d'an sarki ai ba d'an wani annabin bane da za'a so a aure shi. Kuma shi yaron ita dashi bai ma ce yana son ta balle yace zai aure ta, haka zasuyi zaman auren?." Kawu Lawan yace, "sai a bar maganar in mai martaban ya nemi jin ra'ayin ta ace bata amince ba ai ba dukan mu za'ayi ba."

KWANTAN ƁAUNAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant