Kawai sai Lakshmi ta fashe da kuka ta fada jikin babanta tana fadin "Baba na rantse matukar ya ki amincewa ta sai na kashe kaina!"

      Khodaram Moham cikin fushi yace "Ki kwantar da hankalinki dolen sa ma ya amince tunda ke kina sonsa, idan kwa ya ki har yasa na rasaki to fa shima ba zai kara ko 1 second  a duniyar nan ba!"

      Salman tsoro da al'ajabi su kamashi ya rasa ma abinda zai ce yayi tsuru tsuru, sai kawai Suhail ya tashi tsaye ya kalli Khodaram Moham, yace "Ranka ya dade! ina son na dan zaga bandaki"

      Sai Khodaram Moham yasa wani daga cikin bodyguard dinsa dake can gefe da ya nunawa Suhail toilet, Suhail ya shige cikin toilet din ya turo kofa ya rufe yasa sakata ya rufe sannan ya dauko wayarsa a aljihu ya kira wayar Priya, sai ta daga tana tambayarsa me yasa basu dawo ba? a ina suka tsaya? sai Suhail ya kwashe labarin duk abinda yake faruwa tunda farko har karshe bai boye mata komai ba, Priya tana jin haka sai hankalin ta ya tashi tace da Suhail ya turo mata da address din wajen, shi kuma ya tura mata sannan ya kashe wayar ya koma parlour ya zauna a inda yake tun farko wato kusa da Salman.

____________

NIGERIA

     Anan gida najeriya kuwa a yanzu Aisha ta koma kaduna gidan iyayenta na asali zatayi musu sati biyu kamar yadda Alhaji Ahmed ya bukata. Da yamma Rahima tana zaune a bisa tsofaffin kujerunta a falo sai Alhaji Ahmed ya shigo.

       "Salamu Alaikum"

       "Amin wa alaikas salam, sannu da  zuwa" ta mike tsaye ta karbi ledojin dake hannunsa.

        "Yauwa sannu ya gida?"

        "Lafiya kalau"

        "Ah ah ina kuma Aisha ta shiga ne?" ya fada yana dube dube.

        "Ina kuma zata? tana cikin daki"

        "Ya akai kuma ke kina falo ita tana cikin daki sai kace mara gaskiya?" yana magana ya bata rai.

       "To Alhaji nace mata ta fito falo tace in kyaleta a daki, to me zan ce mata, zan kamata da kokawa ne nace sai ta fito?"

        Alhaji Ahmed ya nufi dakin yana cewa "To bari inje in sameta in ma wani abun ne yake damunta" ya shige cikin dakin sai yaje ya sameta tana ta kuka tana zaune akan gado.

       Alhaji Ahmed ya karasa kusa da ita da sauri yana kiran sunanta "Aisha!"

       Aisha sai tayi firgigit ta goge hawayen fuskarta ta kalli sashin da yake tace "Abba sannu da zuwa"

       Alhaji Ahmed ya bata rai yana kallonta yace "Aisha me yake damunki kika zauna a daki kike kuka?"

        Aisha cikin sauri ta girgiza kai tace "Ba komai fa Abba"

        Alhaji Ahmed ya zazzaro ido yace "Ya zan zo in same ki kina kuka kuma in tambayeki kice wai babu komai, ai in gangami da labari domin ruwa baya tsami banza" ya zauna a gefen gadon ya fuskanceta yace "Aisha ki gaya min abinda yake damunki, kin san duk duniya baki da kamar mahaifa, to me yasa zaki dinga boye mana matsalar ki, bayan kin san duk duniya baki da wadanda suka fimu, ko akwai?"

       Aisha ta girgiza kai da saurinta tace "Babu!"

        Sai Rahima itama ta shigo ta tsaya a bakin gadon.

        Alhaji Ahmed ya rausayar da kai yana kallon Aisha yana magana cikin tattusan kalami yace "'Yata Aisha gaya min matsalarki!"

        Aisha hawaye su zubo mata, tana magana cikin kuka da sheshsheka tace "Tunda na gane cewa kune mahaifana hankalina yaki kwanciya sai yawan tunani ne yake damuna kuma nakasa gane tunanin me nake yi, hankalina yayi ta tashi, zuciyata tayi ta bugawa, gabana yayi ta faduwa, raina yana baci haka kawai" sai ta kara fashewa da kuka.

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon