Alhaji Ahmed yace "Malam Buba, yaya Rahila, anti Rahina, mu zamu wuce sai kuma Allah ya sake hada fuskokinmu"

        Malam Buba yace "To Allah ya kiyaye hanya"

        "Allah ya kaiku gida lafiya" inji Rahina.

        "Allah ya tsare, Allah ya kaiku gida lafiya"

        Su kama hanya su nufi hanya, su kuma Rahina da Malam Buba suyi sallama da Rahila su tafi gida, itama Rahila ta wuce ta koma cikin gida.

        ***           ***            ***           ***

     Alhaji Inuwa da Hajiya Sailuba suna zaune a falo suna hira.

        Alhaji Inuwa cikin yanayin tausayawa yace "Kinga abu kamar wasa karamar magana ta zama babba inji masu iya magana, anyi neman anyi cigiyar iyayen yarinyar nan an rasa!"

       Hajiya Sailuba tace "Sai mu cigaba da riketa a matsayin diyarmu, wannan ba wani abu bane face kyauta daga Allah, kuma mun godewa Allah. Ni zan bata duk wani hakki na 'ya akan uwarta"

       Alhaji Inuwa yace "Nima zan riketa tamkar 'yar cikina dana haifa, duk wani hakki nata daya rayata akan mahaifinta zanyi mata shi"

        Hajiya Sailuba tayi murmushin jin dadi tace "Ai gara dai mu kama da kyau"

        Alhaji Inuwa yana dokin murna yace "Bari ma ki gani gobe idan Allah ya kaimu da rai da lafiya makaranta zan kaita private school tunda tace a primary two take sai ta cigaba, zan siyo mata mota na nemo mata driver ya ringa kaita makarantar yana komawa yana daukota idan an tashi, makarantar islamiyya kuma sai ta dinga zuwa tana bayanmu"

        Hajiya Sailuba cikin murna tace "Alhamdulillahi mun gode Allah, ai gara haka duk abinda kai ba Laifin bane"

        Nan suka cigaba da hirarsu tsakanin mata da miji har zuwa wajen karfe goma na daren sannan suka tashi suka tafi dakinsu suka kwanta kowanne zuciyarsa fal da farin ciki.

      ***            ***            ***            ***

      A can Kaduna kuwa karfe goma sha daya da rabi na dare, Alhaji Ahmed da Rahima suna zaune a daki sunyi jigum, Rahima sai kuka take.

         Alhaji Ahmed yace "Haba Rahima me yasa kike neman jefa kanki a wahala? kiyi hakuri ki dangana!"

         Rahima cikin muryar kuka tace "Ai dama tun a can kano na hakura na dangana na fauwalawa Allah!"

         Alhaji Ahmed yace "To amma kin hakura me yasa kike yawan tunani, bakya barci, bakya cin abinci wadatacce, sai kuka kullum kamar matar mamaci?"

          Rahima tace "Haba Alhaji kai kamar baka san irin soyayyar dake tsakanin da da mahaifi ba, ai Aisha ko bani na haifeta ba bazan manta da ita ba koda minti daya ne, ko duniya ta tashi ba zan manta da ita ba, saboda irin shakuwar da mukayi da ita, gashi a kullum bata cin abinci sai tare dani, bata barci sai a kusa dani, amma rana daya na rasata kasan duk abinda nayi ba'a ga laifina ba!"

          Alhaji Ahmed hawaye su zubo masa yace "Haka ne, duk maganar da kika fada gaskiya ne raba da da mahaifi sai Allah, amma don Allah ki rage tunani da kuka ki dinga yin barci yana isarki, kina cin abinci kina koshi"

         Rahima tayi wani dan gajeren murmushi mai kama da yake, tace "To mijina in Allah ya yarda zanyi duk yadda kace"

         Alhaji Ahmed yayi mata murmushi yace "Yauwa matata gara ki gyara zamanta kewarmu, domin wallahi kullum bani da kwanciyar hankali, yanzu addu'a kawai zamu dinga yi a duk lokacin da mukayi sallolin farillar nan guda biyar, muyi ta addu'ar Allah ya bayyanata"

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now