Mai unguwa ya jinjina kai yace "Hakan yana da kyau Honorable, Allah ya bada abinda ake nema, ai ka kyauta ba kowanne dan takara ne zaiyi irin wannan abu ba" ya kalli Aisha yayi mata tambayoyi kamar yadda Alhaji Inuwa yayi mata, kuma ta bashi amsa irin yadda ta cewa Alhaji Inuwa.

Mai unguwa ya kalli Alhaji Inuwa, yace "Honorable ina neman wata alfarma guda a gurinka"

Alhaji Inuwa yace "Ba matsala, fadi ai ba komai"

Mai unguwa yayi gyaran murya yace "Ina so ka tafi da yarinyar nan gidanka, ka kaiwa matarka ta riketa amana kafin Allah yasa a ga iyayenta sai in sa a rako su karbi abarsu, idan kuma ba'a samu iyayenta ba sai ku riketa a matsayin diyarku har lokacin da zai sa tayi aure"

Alhaji Inuwa cikin mamaki yace "Yallabai haka tana yiwuwa kuwa?"

Mai unguwa yace "Eh mana, nawa akai!"

Alhaji Inuwa yace "To in dai haka ne wannan ai ba komai babu matsala zamu riketa da amana"

Mai unguwa yace "Nima abinda yasa nayi wannan tunanin, naga yarinyar daga ganin kasan daga gidan masu hali take, kaga idan aka ce zata zauna a gida irin namu na wani lokaci zata takura tunda bata saba ba, amma kai idan gidanka ne zata sakata ta wala a cikin jin dadi da kwanciyar hankali da samun kulawa"

Alhaji Inuwa yayi murmushi yace "Ah ai shikenan ba komai mu zamu wuce" yasa hannu a aljihu ya zaro kudi ya mikawa mai unguwa, yace "Ga dan wannan a sayi ko gishiri ne ayi miya"

Mai unguwa ya karba cikin farin ciki yace "Allah ya saka da alkhairi kuma Allah ya bada abinda ake nema sannan Allah ya baka ikon yarinyar nan da gaskiya da amana"

Alhaji Inuwa shima yana farin ciki yace "Amin summa Amin"

Ya dauki Aisha su karasa gidansu su gaisa da iyayensa sannan ya basu labarin yadda aka yi ya hadu da Aisha da yadda mai unguwa yace, suyi masa fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya bayyana iyayenta, daga nan yaje yayi sallama dasu ya dauki Aisha a motarsa tare da jama'arsa su nufi gidansa, suna tafiya yana farin cikin samun 'ya a gefe daya kuma yana tunanin yadda Sailuba zata kalli hakan.

*** *** *** ***

Rahima da Rahina suna ta tafiya suna dube dube sun saka Magaji da Salisu a gaba su shiga lungun nan su fita su filla wancan lungun, Rahima tana ta sharbar hawaye.

Rahina tace da ita "Ki daina kuka Rahima in Allah ya yarda za'a ganta ki kwantar da hankali!"

Rahima cikin kuka tace "Wallahi har ma na rasa abinda zance, da a ce Abbanta ya sani idan yazo bala'in da zai yi sai yayi kamar ya dakeni, Allah dai yasa a ganta kafin yazo daurin aure gobe"

Rahina tace "Amin Allah ya bayyana ta, amma dai ki daina daga hankalinki"

Rahima tana kallon Rahina cikin mamaki, tace "Dole ne na daga hankalina! da a ce Aisha mutuwa tayi dole ne na hakura da ita saboda nasan ta koma ga mahaliccinta, wanda ya bani ita ya fini sonta, to amma yanzu fa bata tayi ban kuma san hannun wanda zata fada ba kuma ban san halin da take ciki ba, kinga kuwa ai dole na daga hankalina!"

Rahina cikin tausayawa tace "Kaddara ta riga fata kuma yarda da kaddara babban imani ne, shi kuma hakuri haske ne"

Rahima ta girgiza tace "Ke uwa ce kuma kin san raba da da mahaifi sai Allah, shekara nawa muna tare da 'yar amma yanzu rana daya tsaka na nemeta na rasa!"

Rahina tace "Hakurin dai shine, muje idan muka yayyawata bamu ganta ba sai muje gidan unguwarmu ko an ganta an kaita"

Suyi ta tafiya lungu da sako suna yawo kuma suna tambayar duk wanda suka gani ko ya ganta, amma basu ganta ba basu ga wanda ya ganta ba, don haka sai juya suka koma suka nufi gidan mai unguwar kofar mazugal.

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now