Suna zuwa asibitin a karbeta cikin hanzari a kaita emergency su kuma a barsu anan suna ta jimami da juyayi. An dan jima sannan likitan ya fito daga inda aka shiga da Rahima, ya fito nurses guda biyu suna biye dashi.

       Likita ya kalli Alhaji Inuwa, yace "Honorable muyi magana office dina" sai ya wuce Alhaji Inuwa da Alhaji Ahmed da Malam Buba su bi bayan sa, suje office su zazzauna.

       Likita ya kallesu yace "Honorable matar nan tana fama da bugun zuciya fiye da kima, kuma zai iya haifar mata da heart attack, kuma jininta ma na neman hawa nan da wani dan lokaci kankani"

        Alhaji Ahmed cikin damuwa yace "Likita ta yanzu ya za'ayi"

        Likita ya dauki takarda da biro yace "Zan rubuta mata wasu injections da wasu magunguna sai ku siyo su yanzu yanzu a pharmacy"

        Alhaji Ahmed ta jinjina kai da sauri yace "To shikenan a rubuta!"

        Likita ya rubuta musu a takarda ya mika musu, Alhaji Ahmed ya karba su fita gaba dayansu. Su fito waje sai Alhaji lnuwa yasa hannu ya dauko kudi ya riga dubu ashirin ya mikawa Alhaji Ahmed.

       Alhaji Inuwa yace "Alhaji ga wannan a saya mata maganin, ni zan koma gida amma zan dawo in an jima"

       Alhaji Ahmed ya karba yace "Mun gode Alhaji, Allah ya saka da alkhairi Allah ya kara arziki"

        Malam Buba ma ya kalleshi yace "Alhaji muna godiya Allah ya bar zumunci"

        Alhaji Inuwa yace "Haba wannan ai ba komai bane, mun riga mun zama daya, saboda Aisha ta riga ta hadamu, sai na dawo" sai ya wuce.

        Alhaji Ahmed ya daga masa hannu yace "To sai ka dawo"

        Malam Buba yace "Allah ya kiyaye a dawo lafiya"

         Alhaji Inuwa yaje ya hau motarsa ya tafi, su kuma su nufi wajen pharmacy.

  
     ***            ***             ***            ***

    Bayan Alhaji Inuwa ya koma gida yaje dakin Aisha shi da Hajiya Sailuba suka sameta suka fara mata nasiha da jawabi gaskiyar magana.

        Alhaji Inuwa yace "Ke a ganinki mu zamu iya cutar dake? Ko a tunaninki zamu yi miki karya ne? Ko kuma kina zaton mun daina sonki ne ko gajiya dake?"

        Aisha ta sharbar kuka tace "To amma daddy me yasa baku taba gaya min baku ku ka haifeni ba a lokacin da nake karama a lokacin da ko kun gaya min abin ba zai dameni kamar yanzu ba!?"

        Alhaji Inuwa yace "Gani muke kamar abu makamancin wannan ba zai faru ba saboda abubuwan da suka afku a baya"

         Hajiya Sailuba tace "Mun tsinceki kina karama kuma anyi cigiya an gaza masun iyayenki wannan yasa muka rike ki 'ya, ganin dadewa da shekarun da aka diba babu ko labarin iyayenki shi yasa muka boye wannan abu a garemu don kada idan kin girma kiji ba dadi ko kiji akwai wani gibi a rayuwarki ko kuma wani ya samu hanyar yi miki gori, duk don saboda wadannan abubuwa muka boye miki sirrin bamu gaya miki ba, ba wai don son ranmu ba"

        Aisha ta rungumeta tana kuka tace "Na gamsu da duk abubuwa da kuka fada, nasan ba zaku taba cutar dani ba, don Allah ku yafe min!"

        Alhaji Inuwa ya dafa kanta yace "Ba komai, Ki daina kuka!"

        Aisha tace "Ina so kuyi min jagora zuwa garesu don na nemi gafararsu a bisa bata musu da nayi!"

        "To shikenan ki kwantar da hankalinki yanzu zamu tafi gaba daya, ku tashi ku shirya" Alhaji Inuwa ya fada yana mai mikewa.

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now