Rahila tace "Eh haka ne sai su zo aje a bincike a gani ko Allah zai sa itace"

        Rahina tace "Haba yaya ai itace ma! ga kamanni Rahima nan da tsagun nan na fuskarmu"

       Rahila tace "To mu dai Allah yasa muji alheri"

       Rahina tace "Amin summa Amin"

       Rahila tace "Ai sai ki tashi ki koma, ko baza kiyi girki ba?"

       Rahina tace "Tazarce nayi na rana dana dare na hade da naga zamu fita gidan barkar nan"

        Rahila tace "Kin huta kuwa"

        Rahina tace "Magaji ba'a dawo daga kasuwa ba?"

        Rahila tace "Bai dawo ba amma nasan a gaf da shigowa yake"

        ***           ***           ***           ***

  
        Alhaji Inuwa ya dawo office Aisha taje wajensa tana shagwaba tana bashi labarin abinda ya faru dazu da ita da yadda aka yi.

        Alhaji Inuwa yace "Ummina kema duk da laifinki, nayi nayi dake a koya miki mota kinki saboda tsabar tsoronki, da kinga da kanki zaki dinga tukawa kina zuwa duk inda kike so kina dawowa, amma saboda tsabar tsoro kinki, yanzu ma gashi kinga mutane kin kama tsoronsu, wannan tsoro naki yayi yawa, ke fa likita ce ana so likita ya zama mai dakakkiyar zuciya ba matsoraci ba"

        Aisha cikin shagwaba tace "Ni dai gaskiya daddy na daina fita waje kawai!"

        Alhaji Inuwa cikin mamaki da zaro ido yace "Because of  what? saboda me zaki daina fita waje? aikin naki fa?"

         Aisha ta fashe da kuka tace "Daddy barayin mutane ne fa?"

        Alhaji Inuwa cikin tattausan kalami yana rarrashinta yace "Ba wai daina fita zakiyi ba Ummina, a kasa ne wajibi ki daina fita nima bana so, tunda ga motarki nan duk inda zaki driver ya ringa kaiki yana zuwa yana dauko ki, amma wataran sai ki taho kice kina sauri bai je da wuri ba, ai dole mutane su dinga biyoki kin san ke kyakkyawa ce beautiful girl mai red skin ba'a fiya samun irinku a Nigeria ba sai a India "

         Aisha kunya ta kamata ta kyalkyale da dariya ta tashi ta haye sama da gudu. Alhaji Inuwa ya girgiza kai yana murmushi ya dauki jaridarsa yana karantawa. Da haka ya cire mata tsoron dake ranta har ta samu tayi barci a daren ranar.

        Su kuwa Alhaji Inuwa da Hajiya Sailuba da suka je kwanciya a dakina.

       Alhaji Inuwa ya kalli Hajiya Sailuba, yace "Hajiya me kika fahimta akan wannan labari da Ummi tazo mana dashi a yau?"

        Hajiya Sailuba tace "Kawai abinda na fahimta ba komai bane, ina ganin kamar ta tsorata ne da mutanen kasan Ummi da tsoron tsiya kamar farar kura"

        Alhaji Inuwa ya girgiza kai yace "Ni kuma ba wannan na fahimta ba!"

        Hajiya Sailuba tace "Me ka fahimta game da hakan?"

        Alhaji Inuwa yace "Idan kika tsaya saurari labarin nata kika yi tunani a kanta zaki iya cewa iyayenta na gaskiya ne suka bayyana"

        Hajiya Sailuba cikin sauri tace "Haba Alhaji wannan wace irin magana ce haka?"

        Alhaji Inuwa yace "Ki tsaya kiyi tunani akan abinda tazo ta fada, 'wasu mata su biyu da farko kafin suyi mata magana suna ta kallonta kallo fa na sosai, kuma daya tana da tsagu irin nata' idan har kika yi tunani irin nawa to zaki gano wani abu"

ASHE NI 'YAR TSINTUWA CE Where stories live. Discover now