Chapter 23

79 9 2
                                    

Yau monday na tashi tun 4am ,sallah nayi na roki Allah ya biya min bukatu na sannan ya bamu aljanna na hada da roka ma tanimu karin lafiya,bayan haka na zauna nayi assignment dina.
Bayan na idar da sallah wanka nayi na shirya,tea na hada kadan nasha,ina cikin shan tea sai mama ta taso,ina kwana mama lafiya kalau tace,naga har kin shirya ?aikuwa mama yau ajin 8 nakeda shi gashi in lecturer ya shiga baya bari a shiga,kuma har assignment ya bamu,maxa tashi kitafi toh ai gwara serious lectures haka dan ku yanzu yan zamani in baa muku haka you will not be serious,kai mama nidai kinsan ba ruwana ,wice dai kitafi dai,toh mama sai na dawo.
Nayi saa na isa da wuri kwana biyu makarantar nayimin dadi saboda nayi kawaye gashi kuma suma suna son karatu ,duk da sabbin kawayen nawa haka ba ya hana mu hadu da hafsah kullum innaje makarantar.
Munyi submitting assignment dinmu dai mun huta,next lecture sai karfe 2-4 haka yasa natafi wirin hafsa amma na tsaya na siya abinci a restaurant din hostel saboda yunwa nakeji,nayi saa naje batada lecture hakan yasa muka zauna fira,saida muka ci abinci a hostel sannan na koma lectures din karfe 2 na.
  Ina zaune daga chan baya a cikin ajin muna surutu lecturer ya shigo,ragewar muryar surutun da naji yasa na daga kaina na kalla gaban ajin aikuwa dai sai mukayi ido biyu da zarkadeden saurayi a gaskiya sai da zuciya ta ya buga,saboda shi din ma kallo na yakeyi  da sauri na tabo su faith ta kasan table alaman suyi shiru,duk ajin kowa ya natsu kuwa.
   Yafara bayani yace ni sunana Ibrahim mai shanu sannan yake fada mana lecturer dinmu ya je karo karatu,shi assistant dinshi ne zai karasa da mu session din,munyi mai sannu da zuwa,tsakani da Allah guy din nada kyau,ko kuma ni kadai ce na ke ganin haka?.
   Well har aka gama class din gaskiya idonsa na kaina ni kuma duk nakasa zama comfortable,haka dai har aka gama ajin.
    Yau kam nadawo gida a gajiye sosai,sai da nayi sallar laasar sannan na baro school din,sannu da zuwa mama tayi min sannan tace abinci na kitchen ajiye naji dadi sosai,yau kam naga amfanin zuwa makaranta daga gida dan ko da a hostel nake haka zanje yanzu ina neman mai zanci,dariya nayi ni kadai sannan nace na gode mama.
   Siyama ce ta shigo da agwaluma tana nuna min nace toh sannu iyayen kwadayi,cewa tayi ba dai baki zanyi ba malama ahto,fizgewa nayi a hannun ta aikuwa tazo ta danne ni yanzu kam rokonta nakeyi akan ta daga ni,mama yarinyar nan fa kiba takeyi wallahi,mama cewa tayi wallahi nima dazu nake fada mata toh ci takeyi sosai yanzu,amma dai ni ban hanata ba gwara a ganku tubarkallah ai,ahto mama gaya mata dai a barni inyi kiba ta,jefo min agwalumar tayi tace gashi je ki sha,ya na iya amsa nayi tunda nima inaso.
   Wanka naje nayi,ina cikin toilet din naji siyama na kirana wai inzo ga hadiza tazo,hadiza kuma haka na fada da karfi sai naji hadizan ta amsa tace ehh ni ce yar rainin wayo ayi a fito harda wani wankan yamma ko zaizo ne.shiru nayi kawai dai na karasa wankan sannan na fito.
   Da mamaki nake kallon ta ganin yanda naga ta kara kyau kuma ta zama babba,sannan kuma mamakin me ya kawota gidanmu after all this while da ko an kira wayanta baya yi.
  Aunty zaki zauna ko kin hangame baki kina kallo na ne,cewa nayi sannu da zuwa kinzo lafiya yaushe rabon duniya da ayyaraye fatan kina lafiya,lafiya lau kawata nazo cikin layinku ne gidan wasu yan uwan miji na chan kasa shi ne nace ina fa da kawa yar boko anan bari inzo in gaishe ki,kundai ki aure kunsa boko a gaba ke da hafsa,yanzu kam murmushi kawai na iya yi nace Allah sarki yar uwa komai lokaci ne duka duka nawa muke in miji yazo kuma muma duk zamuyi auren.
  To na gaishe ki kinga ni na wuce,in yazo anjima kigaida shi ,mamaki nakeyi yanda hadiza duk ta chanza da kam ba haka ta ke ba,ban hakura ba nace naga all this while inmunkira ki bayayi da munce zamu zo da hafsa dai sai mukace ai kema baki neme mu ba,cewa tayi ni duk na yakice kawayen nan da kaina wasu kawai so suke su kwacema miji,yanzu kam baki na bude mamaki nakeyi  cewa kawai nayi Allah ya rufa mana asiri,amin tace a haka muka iso falo  ta na fada ma mama sai anjima.mama kuwa harda bata kyautan turare yanda kasan ince ma mama ta ajiye abinta 😒,kofa na rakata ta wuce a motar ta.
     Nadawo parlor mamaki duk a fuskata mama tace yau hadiza ce a gidan namu,aikuwa mama kema kinyi mamaki  gashi nasha bakaken maganganu,kamar ya bakake kawai dai ta raina mu wai harda bataso mu kwace mata miji kuma sannan mu munsa boko a gaba munki muyi aure,to ke sai kika ce mata mene,shiru nayi mama,lallai mama kawai ta iya cewa.
    Da kin bata amsa amma gwara da kikayi shirun,gaskiya naga tana rawan kai da ba haka take ba kuma,in anyi aure so akeyi aga mutum ya kara kamun kai ita kam wannan naga sai a hankali,karki bari abinda tafada ya dameki aure lokaci ne kuma shi ma bokon da kuka kama ba banza bane,watarana zakuga amfanin abin,Ina mata fatan Allah ya shiryeta kuma ya kara mata zaman lafiya da mijin nata.Ameen mama karar kiran sallah magriba ya tada ni nashiga daki yin alwala.
  Hafsa na kira dan in bata wannan labari,sai na jita call waiting,komawa nayi na kira yaya khalifa shima naji shi call waiting,nace tohm wainnan ana chan ana soyayya kenan,karatun Quran na dakko dan naga alama in ba haka ba zan shiga tunani da banso inayi akan rashin lafiyar masoyi na tanimu,gashi kwana biyu ko magana bamuyi ko da yan gidansu.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now