CHAPTER 18

62 6 0
                                    

Laluben wayata daketa faman ringing nakeyi akan gadon da nake kwance Ido na a rufe naki na budewa, karar faduwar  wayar da naji a kan tiles din dakin yasa na bude Ido na da sauri tareda da tashi zaune,a kyuyace na dauka na dakko wayar naci saa ba abinda ya sameta saidai Kirar ya yanke,na duba missed calls Naga Ashe hafsa ce ta kirani,kafin inyi wani tunani wata kirar ta Kara shigowa.
  Cikin muryar bacci na dauka wayar,nace lafiya ake kirana da sassafen nan madam ?dariya hafsa tayi tace duba dai malama ba safiya bace yanzu gashi har karfe 11 na safe,zunbur na mi ke na kalla agogon dakin Ina zare Ido,Sam bansan lokaci ya Kai Haka ba,daga chan hafsa ta katse tunani na tana fadin Dan Allah so nakeyi mu hadu,wallahi inaso muyi magana Amma inajin kunya mama yanzu bazan iya zuwa ba.
Dariya tabani nace munafika bawani kunya ai,Sai ma nafada Mata yanda akayi kuka hadu zakiga kunya,yanzu kawai gulma kikeyi,hakuri hafsa tafara bani Wai Dan Allah Kar in Tona ta a wurin mama ai Dan nata ne ya cika kyau da kyawawan halaye,eh lallai yarinya kin girma Zan fada ma mama,hakurin dai ta cigaba da bani,tace ya zaayi mu hadu dinne nace in mama tabarni zanzo gidansu,da Haka mukayi sallama.
  Yau kwana uku kenan da komawan ya khalifa wurin aiki,which makes it three days da tanimu yafada min ciwon da ke damunsa,cikin kwanakin damuwa ta ya Dan ragu saboda kullum muna waya Kuma sannan maganganun da ya khalifa yayi min sun taimaka wurin kwantar da hankalina,na San ba abinda yafi bukata yanzu kamar addua da kulawan loved ones.
   Falo na fito wurin mama gaisheta nayi,ta dago ta kalleni tare dacewa lafiya kalau ai yanzu nake Shirin inzo dakin naki Inga ko lafiya,tunda mama taji labarin ciwon tanimu Sai ta Zama kamar tana Jin tausayina badan haka ba nasan da tuntuni ta tasheni a wannan baccin.
   Siyama na gefe tana mopping,amsa nayi nace Zan cigaba tunda dama aiki na ne,amsa kayanki dama mama tasani Nima in tayaki,harararta nayi dai na cigaba da aikin,Ina Gama mopping parlor na koma na gyara dakin mama da toilet na wanke,sannan na dawo dakina shima na gyara ko Ina tsaf na baza turare a burner kamshi Nanda nan ko Ina ya dauka,wanka nashiga nayi kafin in fito Ana Kiran azahar,duk da inajin yunwa nace Sai nayi sallah zanci abincin.
  Tea nasha na hada Mana spaghetti with meatballs stew for lunch,Ina cin abinci tanimu ya kirani,mun gaisa cike da kulawa yake fadamin yanzu yadawo daga asibiti yanzu gobe zaa Fara chemotherapy din in sashi addua,karfafa Masa guiwa nayi nace insha Allah zaa samu nasara.mun Dade muna firan soyayyan mu sannan mukayi sallama.
   Yaya batool najiyo muryarta tana kwada sallama,chan na jiyo annur shima Yana sallama da sauri natashi Ina musu oyoyo,annur ya rungumeni yayi Yana fadin mama oyoyo duk da maganar nasa Bata fita da kyau,daukan shi nayi na rungume shi sosai jikina,itama Yaya batool rungumeta nayi.
  Chan wurin mama na Mika shi har wani kunyanta yakeji,yaki sauka a jikina dariya mama tayi tace lallai wannan mijin kunya gareshi,Yaya Asiya ta shigo ta zauna sunata fira da mama,Ina gefe nida shi a jikina yaki sauka ai kawai Yana ganin siyama ta fito da gudu ya tafi wurinta,dariya muka hau Yi nace eh lallai Ashe ita siyama kanaji da ita mama na gefe tana kallon mu tace ai nasan me Zan bashi yanzu zakuga ya dawo wuri,aikam mama na dakko Jakarta ya tafi wurinta Dan yasan chocolate din da ta Saba bashi zata dakko,Haka dai akayita fira.
   Mama na samu nace Mata inaso zanje gidansu hafsah,cewa tayi in dawo lafiya Amma Kar in Dade,Kampala Mai multicolor anyi min buba da ita na saka,sannan na yafa gele nayi kyau abuna Kuma very simple,Yaya batool tace Yan Mata kunsha kyau Allah ya kawo miji na gari musha biki,zumburo Baki nayi dai na wuce a kasan Raina nace ameen.
  Na Isa gidansu hafsa na tadda maman su a falo,gaisheta nayi tana fadin yau ke ce a gidan namu,sannu da zuwa kawar Taki tana ciki,da toh mama Na amsa na Mike na shige ciki,nayi sallama Bata amsa ba Sai naji gyaran murya,nashiga na tadda Ashe sallah takeyi,ban ko zauna ba Nima nashiga bathroom nayo alwala domin inyi sallah laasar din nima,tana idarwa Nima na kabbara nawa ban tsaya sauraron shirmen ko ince gulman da takeyi min ba na Wai kunya na takeji.
   Fira muka hau Yi kaman yanda muka Saba abinmu,yau ma munyi firar kawar mu hadiza inda muke jajantawa yanda ko an kirata Bata daukan wayan kwana biyu ma wayan nata a kashe take a Haka dai muka ce zamu sa Rana muje har gida muga ko lafiya.
  Munyi fira da hafsa sosai,har ta Kira ya khalifa ta fada Mai nazo,Ina gefe in jinsu suna soyayyar su,cewa nayi lallai abin naku ya kankama biki kawai zamu sha,dariya dai hafsa tayi Bata iya cewa komai ba,Naga alama har wani kunya na take ji yanzu dan gulma.
  Naci samosa da hafsa ta soya min,Ina tsokanarta nace lallai Yaya na zaici Dadi,dama inata rokon Allah Kar hafsa ta tambayeni tanimu Dan yace shi baya so ayita Masa sannu,nikuma nabari Akan inta tambayeni shi Zan fada mata dan ko ba komai tayi Mai addua,dawowa tayi dani daga tunanin da nakeyi tayi tana fadin malama lafiya me kike nazari Haka,ce Mata nayi ba komai,ce wa tayi ban yarda ba Amma nasan ko meye Zaki fadamin in kin shirya,gyada Kai nayi alaman gaskiya yafada.
Nadawo gida gab sallar magriba na tadda Yaya batool ta tafi Amma ta bar Mana annur,Yana hannun siyama su nata Wasa,Yana Jin muryata nayi sallama yatashi yazo ya kamani sosai.munci dinner ta re nabashi laptop dina yana kallon cartoon munata fira har kowa ya shige daki.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now