Chapter 21

47 6 0
                                    

Yaya khalifa ya fada ma mama labarin soyayyan shi da hafsa,yazo yayi yayi in fada mata nace sai dai shi yafada mata saboda ai shi ya kai kansa😂, ya fara fada mata na tashi na shige daki na bar shi wayata na dauka na kira Hafsa,cikin tsokana nace aunty hafsa ina wuni ke banson iskanci tace waye auntyn ki dariya na fashe da shi nace yanzu dai ya tabbata kin kusa zama matar yayah khalifa to wai aunty zan dinga kiran ki ko yayah hafsa zandinga ce miki?
Aunty zaki dinga ce min,nace laa ji ko kunya to baki isa ba malama, dama gulma na kawo miki ga gogan naki chan naji yana fada ma mama maganarki ne nace bari inzo in fada miki ki fara shirye shirye dan nasan mama bazata ja abin ba in har taji ke ce amaryar dama ta kosa ta aurar da yaya khalifa,to kawai ki fara shiri ahto,wayyo asiya nabani natsu ki gaya min maganan nan da kyau me mama zatace shikenan yanzu ya zanyi in dinga zuwa gidan ku,duk wannan tambayan ban amsa taba na kashe wayar inaji tana kara kira naki dauka tashi nayi ina goge gogen daki.
    Siyama ce ta shigo daki da gudu tana fadin yayah asiya ke ma kin manta ko wai yau birthday din Annur,munyi abin kunya mun manta da birthday din yaron mu,hannu nasa na rufe baki na alaman na manta  kwana biyun nan daga school sai maganan ciwon tanimu su ne ban mantawa,cewa nayi me zamu shirya mai kafin  yaya batool tajimu shiru yanzu inta taso mu mun bani.
    Siyama tace wallahi kuwa yanzu ma kinsan ya akayi na tuna mijin ta ne naga yasa status shi ne na tuna,nace ni banma gani ba yanzu ma ba wannan ba me zamuyi mai ,siyama ta kawo idea mu siya cake,da drink sai muje gidansu a dan hada small party if its ok ma muje park,gyada kai nayi alaman yayi nace mayya yanzu har kin nemo idea haka zamuyi bari mu fada ma mama da yaya khalifa kinga kila ya rakamu yazo mana da matarsa hafsa,dariya muka kyalkyale da shi ni da siyama sannan muka nufi wurin mama a parlor.Mama go ahead ta bamu muka ce ta miko nata gifts din cewa tayi zata bashi da kanta in yazo,yaya khalifa yace kunga ku kyalemin mama na ta huta zan siya komai da komai mu tafi cewa nayi muma dai maman mu ce,bige bayan kaina yaya khalifa yayi nace mama kinga zai karasa ni saboda ya saba ture mutane a wurin yaki yasha nan ma battlefield ne,dariya mama tayi tace ka rufamin asiri khalifa,daki kowa ya nufa yaje ya shirya.
Munyi kyau abinmu kowa ya fito mama tace yara na kowa ya fito tas Allah ya muku albarka a tare mukace amin muna nufan kofa.mun isa gidan yaya batool munata knocking gate shiru dai amma dai motan ta da namijin yana ciki hakan ya tabbatar mana da su na nan,chan sai ga mijin nan yazo ya bude gate din,dama duk wannan knocking din da mukeyi ya khalifa be fito ba a cikin motan,yana bude kofan mukaga alaman bacci yatashi duk sai mukaji kunya laa yaya mansoor bacci muka tashe ku,kai haba ba komai ku shigo muma kawai baccin rana ya kama mu yau saturday.
Yayi gaba muna biye dashi sai na koma mota nace yaya khalifa ya shigo cewa yayi bazai shigo ba anyi abin kunya kar ma muce tare muke yana jiran mu muzo mu wuce in kuma a gidan zaayi shi ya yafe,dariya na kyalkyale dashi nayi gaba na barshi.
Annur na bacci a kujera a parlor sallamar mu ya tashe shi a baccin yafara dariya da mamakin ganin mu,birthday boy ya haka kake ta bacci where is your mom ya zata bar mana yaro ranan birthday yanata bacci ba wani fun,muna fadin hakan sai gata nan tafito auu ashe baku manta ba ai na zuba muku ido ne inga ko kun manta nace bari ingani zuwa laasar inna jiku shiru zankira in muku gori Allah ya so ku,dariya mukayi nida siyama nace yau Allah ya so mu siyama toh yanzu munzo ne zamu fita park ko kuma muyi anan gida mun siyo komai da komai yaya khalifa ma na waje a mota,wai bazai shigo ba dan yaga alaman bacci muka tashe ku ba da shi ba wannan abin kunyan,lallai beda aiki dan Allah je ki ce yashigo ko kuma bari ni inje hijab dinta ta sa ta fita wirinsa chan sai gasu sun shigo tare.yanzu dai fitan zamuyi ko dan ni yafi min ma dan harna gaya ma matata,da alama shima be san yafadi hakan ba saboda kulle bakinsa yayi bayan ya fada,dariya muke yaya batool tace kahlifa me naji kace?matarka wacece kuma wannan cewa yayi in tazo kya gani,siyama tace yayah batool akwai gist fa bari dai jeki shirya.
   Ni na nemo ma annur kaya na shirya sa as per celebrant yayi kyau wata shirt light blue mai short sleeve harda bow tie nasa mai, sai dark trouser yayi kyau harda glass da agogo abinku da big boy,maman shi ma tayi kyau baban ma haka.sai da su yaya khalifa sukaje sukayi sallar laasar muma mukayi sallah a gida sannan muka wice.
   Park din katafare ne asalin defination of peaceful sai kukan tsintsaye da iska me dadi,ga horses ga swimmming pool,ga lilo kala kala wurin yahadu,excitement a wurin annur baa magana i was like oh yeah have fun my son its your day,dariya yayi yace thank you mama asiya.
Carpet muka shimfida kowa ya zauna anyi setting abin like picnic 🧺 party,ana cikin haka mukaga yaya Khalipha na amsa waya yana fara waya nace tohm zaa je taro ta steady steady dai ka kwace min kawa, kallon mu yaya batool tayi da mamaki tace wace kawar nace bari dai zaki gani muna zaune ya wuce chan sai gashi tareda hafsa sai makale makale takeyi a bayan sa,kafin su iso nace fito malama daina wani boye boye ,kinyi kyau fa kuma hafsatuwa well u get explanations to do for yaya batool,ji nayi kawai yaya khalifa yace aah ba ruwanta ni zan fada mata.
Sun gaisa normal,daga nan aka yanka cake kowa ya bashi gifts,siyama tayita rawa itada annur nidai dama ba gwanar rawa bace,munyi games kala kala da pictures it was a memorable day, na samu nayi ma yaya na da kawata hotuna tare sai yau naga ashe dai duk sun dace sosai.Na tuno da saurayi na tanimu ko hoto tare bamu taba yi ba kwalla naji yana kokarin zubo min na shanye sannan nayi masa adduua a raina.
Motar yaya mansoor muka shiga akan mu koma gidansu sai yaya khalifa ya kai hafsa gida sai ya zo mu wuce gida,mun isa gida yaya batool na tambaya na wai ya akayi in mata bayani ce mata nayi biki zaayi a gidanmu,hafsatu ta zama ta yaya khalifa cewa tayi yanzu dai ta daina kula mazan ko cewa nayi kai yaya batool yanzu fa ba ruwanta da samari yaya khalifa ne shi kadai ,tohm Allah yasa amin nace kawai.

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now