CHAPTER 8

90 10 0
                                    

Akwana a tashi yau Yaya khalifa zai dawo,mama Sai shirye shiryen walima takeyi,jiya mukaje POP din shi a NDA,Yan uwa na kusa duk sun hallara wurin taron jiya,munsha kallo kam ga manyan Baki harda su shugaban kasa da gwamnoni taron ya tsaro sosai,bayan haka munyi pictures ,Yaya khalifa yayi murnan ganin mu sosai siyama ceke kokarin Haye bayansa kamar Yar yarinyar,cewa yayi ke fa kin girma yanzu mun daina kalan wannan wasan,su din burge mu sukayi,ce Masa takeyi Yaya abubuwa da yawa sun faru na kosa kadawo gida in baka labari,dariya yayi yace Nima abubuwa dayawa sun faru siyama Zan Baki labari but am now a soldier in Kika Dameni da surutun nan naki Zan harbe ki,ihu tayi ta sauka a bayan sa da take kokarin Hawa,duk waigowa akayi ana kallon mu,cewa yayi mama yarinyar nan fa kiba Naga tayi,yawanci Yan uwa duk Basu San siyama harta je rehab tadawo ba saidai kawai kowa yaganta Yana cewa yaga tayi kiba,saidai muyi dariya.
  Gidan cike ya ke da Yan uwa da abokan arziki,ga Kuma abokan Yaya khalifa duk sunzo tayashi murnan Gama karatu gashi ya Zama sojan sama,anci ansha an tafi da souvenirs,mama kam murna baya misaltawa babban danta  yazama soja.
    yaya batool yanzu cikinta wata hudu kenan,munyi murna saboda an dan dade Ana jira,dama mama Tasha fada Mata lokaci ne,gashi kam yanzu Allah ya Bata,har yanzu Bata sakewa sosai da siyama ita haka Allah ya yota,wasu halayenta banaso Amma me Zan iya?ai Yaya ta ce,Kuma family is family.
  Muna ta shirye shiryen bikin hadiza ta bello,mu ne manyan kawayen amarya,yau ma anko mukaje siyo wa,min siyo atampa na yinin biki da Kuma material Wanda zamu sa ran dinner,gida muka dawo munata labari sannan muka tura ma sauran friends dinmu ankon,Muna zaune Muna fira da hadiza da hafsa naji wayata na ringing,gudun surutun su nakeyi shiyasa Ina kallo naki dauka,gashi Kuma fushi nakeyi dashi kwana biyu ko waya bamuyi ba,Saida ya Kira sau uku Ina kallo Ban daga ba Sai Kuma naga message,"am sorry my princess,nasan nayi laifi but please come outside I have a surprise for you"Ina karantawa Ina smiling,Ina Gama karantawa na mi ke da gudu,Sai lokacin na tuna Ashe su hafsa na dakin gaba daya hankalina ya dauke,dariya suka fara min da mamakin ko lafiya ta,ce musu nayi Ina zuwa dai,parlor na tadda mama a kunyace nace mama Zan duba Abu a waje,siyama da ke gefe ce tace Anya Abu ne kuwa zaa duba a wajennan,bige ta nayi sannan na sa Kai nayi kofa,gate na karasa da sauri na Ina zuwa naganshi tsaye,murna nakeyi sosai,ji nakeyi kaman in rungumeshi Amma bazan iya ba,shima na tabbata hakan yakeji,lumshe Ido yayi Kuma Sai ya bude kusa da Ni ya matso ya Kama hannu na,Sai kawai naji ni Ina hawaye,hawayen kewansa da nayi,girgiza min Kai yayi alaman in daina,yace ko so kikeyi Nima inyi kukan,gani nan ai nadawo,nasan kina kokari nidai fata na ki cigaba da hakuri da rashin Zama na,Kar wani yazo ya kwacemin ke,I have a long way to go,I am scared I might lose you,gashi Naga kin Kara kyau sosai princess nikadai nasan yanda nakeji yanzu,maganganun sa sunyi min Dadi,Sai Kuma Nima nasan tabbas akwai sauran tafiya a gabanmu,muna cikin wannan maganan Sai na hango siyama da hafsa ta gefen gate suna leko mu,dariya na kyalkyale dashi ce mashi nayi baby wallahi wasu sun sa Mana ido suna leken mu,murmushi a dauke a fuskan sa yace Ina kallon su tuntuni kyalesu ga tsaraban ki nan Kuma Kar ki tsammusu inhar Basu fito min gaisa ba,ji nayi kawai an bude kofar gidan duk suna Jin mu Ashe,siyama tafara gaidashi Sai Kuma hafsa,yace princess ki tsammusu since they have greeted me,ansan ledar nayi a kunyace yace Bari inje gida,da mallam shehu mu ke,ko gida beje Dani ba nace Ni saina Fara ganinki,ga umma nan Sai Kira takeyi,she missed her boy,dariya nayi nace nagode,daidai kunne na yazo ya ce "I love you so much princess,will you be my wife?"Sai Kuma yace amsar kin fada min anjima,na rasa me zance maganar jinta nayi sosai cikin jikina,Ina kallo motan su ta wuce,nashiga gida na tarar dasu a tsakar gida Ana jira in shigo,kafin suyi magana nace toh gulmammu,yau dai kunga Adam,da hadiza da hafsa nakeyi,hadiza ce tace dama ita tasan shi Amma Bata San shi ne saurayin nawa ba,dama ita hadiza gidanmu da gidansu babu nisa,a tare suke fadin ya hadu,ce musu nayi ai Nima nasani Dan in biyesu da tsokanar su,ihu sukayi tare,siyama na Mika ma ledar nace nikam ki nuna ma mama bazan iya ba,hadiza ce tace Mara kunya da ki Kai da kanki Mana,ce Mata nayi ai kece Mara kunya,ke da ma aure zakiyi,dariya mukayita Yi tare sannan muka shige ciki Ina Shiga ciki na tadda siyama ta cika mama da surutu,Miko Mana ledar mama tayi tace kuyita Sha,ayi Bismillah shima ya iya Taya bera Bari,siyama tabiyo mu dashi daki kowa yayita dauka Yana sha,daga nan suka tashi suka wuce gida.
  Tunda Yaya khalifa yadawo gida mostly bacci yake sha,ko fira akeyi shidai inda zaisa kansa ya huta yake nema, maza fa anji jiki,gashi Kuma anriga anyi posting dinsu,hutun few days aka Basu an tura shi yobe,duk ya rame Amma ya yaiya,ai shi yace zaiyi🤣.
siyama kam ta dawo daidai da harkokinta,Kuma yanzu mama na iya kokarinta wajen kasancewa da ita sosai sannan duk sanda ta ganta ta chanza yanayi tana tambayan ta,makaranta ma an chanza Mata saboda ta manta da komai about wannan yaron,kullum mama na fada Mata how beautiful she is and duk Wanda ya rabu da ita yayi ma kansa,she's young and beautiful,mama na Mata kirari tace "babban kifi",Yaya khalifa kam be ma San abinda yafaru ba Sai da mama tafada Masa,yayi mamaki sosai Amma ya fahimce komai Dan haka shima Kara kula da ita yayi sosai,haka rayuwa ke ta tafiya Mana komai alhamdulillah.
Bayan naje daki tunanin maganar Adam naketa yi,Ina cikin tunanin naji kiransa na dauka naji yanayinsa ba walwala sosai,tambayar sa nayi ko meye Amma yace babu komai,a hakan Kuma Sai mukayita labari har muka manta da damuwar mu,sallama mukayi muka kwanta bacci.
   Abin mamaki tun Ranan Sai bamu Kara waya ba da Adam,ko na Kira Kuma baa dauka hakan yasa nafara damuwa kadan kadan,gashi ko nabi in zamuje islamiyya da siyama ban ganinsa,yau wurin kwana biyar kenan shiru,Sai nakasa hakuri mama nafada ma nace Ni yanzu bansan me ke damunsa ba,Naga damuwa a fuskanta Amma tayi kokarin boyemin,cemin tayi ki cigaba da addua,Allah zai Baki amsan duk damuwanki,Dadi naji sannan natashi nayi wanka,yau kam sati daya nafara tunanin ko inje gidan Sai nace Kuma zaa ce bakida hankali,nikadai nafada ma kaina,haka dai na hakura.

Please like and comment

NI DA YAN GIDAN MUWhere stories live. Discover now