Daga nan Dauda ya tashi ya tafi yana tafiya yana tunanin yadda Fatima da Imam zasu kalli wannan shawara ta Baba na kowa, a wani bangaren kuma tunanin hanyar da zai bi ya kubutar da Imam daga wannan tafiya mai hadarin gaske, har dai ya isa gida bai samu wata mafita ba kawai sai ya hakura.

     Yana shiga gida Fatima ta tarbeshi da farin ciki tana cewa "Sannu da zuwa Baba"

     Dauda yace "Yauwa Fatima yaya gidan?"

     Fatima tace "Lafiya kalau"

     Dauda ya nemi guri ya zauna sannan yace "Debo min ruwa Fatima"

      Fatima tace "To Baba" ta tashi ta tafi ta debo ruwan ta kawo masa.

      Dauda ya karba ya sha sannan yace "Kirawo min innar taki kice mata na dawo"

      Fatima tace "To Baba" ta tafi jim kadan sai gata ta dawo tace "Baba tace tana zuwa"

     Sai Dauda ya nuna mata waje a kusa dashi yace "To zauna anan"

    Fatima ta zauna dama abinda take so kenan don ta kagu taji yadda Baba na kowa yace ayi. Suna nan zaune sai Harira tazo ta nemi guri ta zauna sannan tace "Ashe ka dawo?"

    Dauda yace "Eh yanzu na shigo"

    Harira tace "Nima barci ne ya daukeni bayan na idar da sallar walha, sannu da zuwa"

     Dauda yace "Yauwa sannu, ku bude kunnenku kuji abinda zan gaya muku. Naje na samu Baba na kowa ya fada min abinda zanyi musu" ya dan numfasa sannan ya fada musu duk abinda ya faru tsakaninsa Baba na kowa da duk abinda ya fada masa yayi.

     Yana gama fada musu sai Fatima tayi farat tace "Yanzu Baba har da Imam za'ayi wannan tafiya? karfa ya halaka!"

     Dauda yace "Ki kwantar da hankalinki Fatima in Allah ya yarda babu abinda zai sameshi zai dawo lafiya" yana kallonta yaga yanayin ta ya sauya duk jikinta yayi sanyi, sai yace "To ai Fatima in har nace zasu tafi ba tare da Imam ba kuma daga baya na aurar dake gareshi, sai suyi zaton dama munafuntarsu nayi, kinga abinda ake gudu sai ya afku garin neman gira a rasa ido"

      Fatima tace "To shikenan Baba ba komai Allah ya kai shi lafiya Allah ya dawo dashi lafiya" tayi shiru tana kallon wani guri daban tana tunani.

      Sai Dauda yace "Nasan zaki shiga wani yanayi na daban, to ki yawaita addu'a kuma ki daina yin yawan tunani, Allah ya cika miki burinki na alkhairi"

       Cikin sanyi jiki tace "Amin Baba"

    A ranar Dauda yasa aka gayawa duk wani wanda yasan yana zuwa gurin Fatima cewa yana son kowa ya hallara a gobe goben nan.

   Kashegari kuwa da hantsi kowa ya hallara a kofar gidansu Fatima, suna nan tsattsaye sai ga Dauda dauke da shimfidu yasa aka shimfida sannan shima ya zauna, da aka yi addu'a sai Dauda ya fara bayani kamar haka "Abinda yasa na tara ku anan shine, fadace fadacen da kuke yi akan 'yata Fatima sun isheni dan haka naje gurin Baba na kowa ya bani shawara cewa duk wanda yake son Fatima da aure, to dama akwai wata gasa da kuyi duk mai sonta zai tafi birnin Sin yaje tsuburin mongoliya ya debo ruwan dake kan tsuburin, duk wanda ya dawo a cikin shekara biyar ba tare da ya kara ko kwana daya ba, to shi zan aurawa Fatima a ranar da ya dawo. Yanzu na baku kwana uku kuyi shawara domin nan da kwana biyar nake so ku tafi"

   Gama jawabin Dauda keda wuya sai gurin ya hargitse ya cakude da hayaniya da kuma bakaken maganganu, da kyar Dauda ya shawo kansu suka yi shiru sannan yace "Yanzu kawai kowa ya tashi ya tafi na sallame ku"

     Suka tashi suka tafi. Tun a ranar mutum goma sha shida daga cikin samarin Fatima suka aikowa Dauda cewa su fa sun hakura da auren Fatima, bayan kwana uku kuma mutum hudu suka zo suka ce suma sun janye ba zasu ba sune su rasa rayukansu a banza sai ya rage saura mutum uku  wato Imam da wasu  'ya'yan attajirai Jabiru da Jafaru su suka ce sunji sun gani zasuje ko zasu rasa ransu kuma babu gudu baja da baya har sai sun cika burinsu don haka sai Dauda yace musu jibi zasu tafi kuma yana so su hadu dashi a kofar gidan Baba na kowa, suka yi sallama suka kama gabansu. 

     A bangaren Fatima kuwa kwata kwata bata ji dadi ba da taji Jabiru da Jafaru sun amince zasu birnin Sin, taso ace Imam ne kawai ya rage a cikin su kawai da sai suyi aurensu ba sai ma yaje ba amma yanzu sun bata mata buri ta kudurce a ranta ko sunje sun dawo in dai har ba Imam bane ya samu nasara to babu wanda zata aura a cikinsu.

    Da Imam yaje gida sai ya fadawa Innarsu abinda yake faruwa da yadda aka yi, sai Innar tasu nemi hanawa ta fara yi masa maganganu masu kashe jiki.

      "Yanzu Dan nan tafiya zakayi ka barmu? kasan duk garin nan bani da wani gata da ya wuce ka, babu wani mai taimaka mana sai Allah sai kai tun bayan rasuwar mahaifinku, yanzu in ka tafi ina zamu kama?"

      "Kiyi hakuri Inna na riga na yiwa Fatima alkawarin aurenta kuma na rantse da ba don haka ba babu abinda zai sa nayi tafiyar nan na barki cikin kadaici ba, amma ai ga Aisha da Aminu nan kannena zasu iya kula dake kafin in dawo, kiyi hakuri Inna dole ce tasa haka kiyi fatan kawai Allah ya dawo dani lafiya kuma ki ringa yi min addu'ar Allah ya kaini lafiya ya dawo dani lafiya a duk sa'in da kika yi sallah"

      "To shikenan Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya kuma nayi maka alkawarin zan dinga yi maka addu'a"

      "Yauwa Inna, sannan Aminu zai dinga zuwa gurin sana'ata yana nemo muku abinda zaku ci ita kuma Aisha sai ta dinga taimakonki da aikace aikacen gida kamar yadda take yi da, Allah ya baku hakurin jure rashin ganina"

Kada ku manta da:

>Like
>Share
>Follow
>Comments

            
                         📖.............. ✍️
                      *Alkhamis KSA*

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 01, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

  IDON BAKAR MAGE A DUHU Where stories live. Discover now