BABI NA HAMSIN DA BIYAR

Start from the beginning
                                    

Wannan yanayin ba karamin dadi ya mata ba, domin bayan ta bar rafin kafin kace kwabo al'amari ya karade ko ina hatta rijiyiyyon da suke kewayen, tsuntsaye kuwa tuni suka yi cida wuta.
Abin da ya d'aga hankalin mutane kenan suka shiga niman agaji domin dai basu ba shan ruwa, ruwan da ta dauka gidan su Baffa'm ta kai tagaishe da Sarkin Gida wanda taki yarda su hada idanun su. Shima kamar wanda yake tsoronta yaki d'ago kai ya kalle ta.

Tana barin kofar gidan ya D'aga yana bin sawun ta da ido, da sauri ya shiga cikin gidan. Ya kira Baffa'm da Galadima.
Kallon wurin suka yi.
"Wayyo Allah na" inji Galadima.
"Ta zarce Aminatu ko?"
"Kowani lokaci zata iya daukar yanayi akan kowa" baffa'm ya tambaye shi a tsorace, domin shima ya gama razana da yanayin Anum, dan haka suka bi bayan ta.
Sanin babu wanda ya gane me take ciki tana shiga cikin gidan takada shanun ta suka bar gidan baki daya, har yankin ta bari, ba tare da ta juya ba, kawai tafiya take da shanu, ta kai ko mugan namun daji suka haɗu da ita sai dai suyi ta gudun ta. Yanayin ta ta'azzara da ko wucewa tsuntsun yayi akan dabobbin ta,ta Kalle shi faduwa yake a mace.

A can kuwa hankalin mutane ya tashi ga ruwa ya lalace dan haka masu maganin dan masu duba,bokaye da yan bori. Suka tawo aka saka ruwan a gaba da bincike, Galadima da Baffa'm sai dare suka samu damar zuwa ganin ruwan,bayan sun gama abinda ya kawo sune suka dawo gida, a hankali Galadima ya sauke ajiyar zuciya.
"Sarkin gida me yan borin suka fada?"
"Sunce tsinuwa ce da alwashi"
"Sun mata wani abu kenan da har ta yi alwashin"
Girgiza kai yayi, sannan suka ce.
"Babu ita babu alamar ta fa a wannan yankin?"
Kasa magana suka yi suna nazarin ta ina zasu dakatar da ita.
**
"Boka ka duba al'amarin yarinyar nan ta bayyana yanzun haka ta gabar din mu sun mata laifi ta musu alwashin ruwan su ya koma na jini" bincike yayi sosai sannan ya ce mishi.
"Sai dai ka nimawa Danka auren ta ba dai kai ba, a yanzu haka tana gab da samun me iya dakatar da ita. Domin ƙaddara ta ja ta izuwa takin da mutuwa ce xata iya shiga tsakanin rikicinda ya kono kai"

"Ban gane ba?" Ya kuma tambaya,
"Ina tabbatar maka ba zaka iya ba, ba zaka iya dakatar da ita ba, Danka da yake sonta bazai iya ba sai dai idan zaku aura mishi ita bata sani ba, shima ba wai karfi zata kara mishi ba,idan yayi wasa mutuwa zai yi domin yanayin ƙaddara ba zai barta haka."
Kamar wanda aka watsa mishi ruwa haka ya mike, ya bar bokan cikin nashi binciken.
--
Tsawon kwanaki uku,tafiya yake ba dare ba rana, fuskar ta yayi fayau kamar wacce ta rasa jini a jikin ta, kawai kada shanun take, gajiya tayi da tafiyar ya samu wani kasar bishiyar, domin yanayin ta ta fara dawowa daidai, shi yasa taji gajiya zama yayi a kasar bishiyar wata tsohuwar tsamiya, ta lumshe idanun ta, wani irin gud'a aka rangad'a daga jikin bishiyar tsamiyar, gyara kwanciyar ta tayi tana me jin kamar an lullube ta d bargo. A hankali ta kwanta barci yayi gaba da ita.

Kallon rana yayi yaga yayi zafi burin shi ya samu wani wurin ya tsaya yayi sallah sannan ya cigaba tafiya. Hango shanu nata kiwo ne ya sa shi tunanin ai ya kusan gari, daga cikin yake hango wani katon mesa yana nad'e bishiyar da take kwance a jikin shi, kafin ya kuma sauka yana Niman hanyar da zai hàdiye ya baki daya, domin ya kwana biyu bai hàdiye dan adam ba, shi yasa da yazo wucewa ya hango ta kwance yaji ya samu kalacen shi na kwana da kwanaki kafin ta rube ya yarda kanta. Sai zaro harshe yake yana zagaye ya, amma zafin wutar da ke fita a jikin ta yasa shi kasa mata kome, sauka a dokin Lamido yayi ya zaro takobin shi, yana zuwa a hankali yadda mesa ba zai fusata ba.

Aikuwa yana isa ya samu dan bakin Naci ya fara na hàdiye kafarta zuwa gwiwar ta,. Dake mesan shima zalamamme ne da sauri ya zaro bakin shi daga kafarta ya nufi Lamido, a fusace shima cikin fushi da yi kan shi tare da sare kan shi da ya bude mishi. Aikuwa jinin ya ce watsu a fuskartar, abin ya firgitatta kenan ya fasa wata irin kara da ya haifar da kamawar bushiyar twamiyar nan, kafin ta kuma kara ihun ya maza ya toshe bakin ta, tare da fitar da ita kasar bishiyar tsamiyar, ya matse bakin ta da karfin tsiya wani irin tururi da zafi yake ratsa hannun shi, ta shiga kokarin kwace kanta, amma haka yayi nasarar matseta a jikin shi. Sai da ya tabbatar ta suma yanayin jikin ta da yake da zafi ya koma yayi sanyi, kamar wata matacciya, sauke ta yayi ya kwantar da ita sannan ya shiga kafa tanti a wurin ya gyara cikin ya saka ta, kafin ya cigaba da tattara mata shanun ta, kallon tafin hannun shi yayi yaga yayi jajjur. Kallon tantin yayi,
Sannan ya shiga niman tattara kome, ha kuma tsinko magani ya zo yayi ta dakawa da wani irin dutse ya matse ruwan a tafin hannun shi. Lumshe idanun shi yayi yana jin zafin na ratsa shi, sai da ya gama sannan yayi Sallah yana idarwa ya fita farauta. Haka ya samo fakara guda uku wato kajin daji, ya kawo ya gasa, sannan ya ciro bushashen naman da Innayoh ta hado mishi ya koma gefe ya ci sosai, har dare bata farka ba, dan haka ya cigaba da hada wuta yana karatun Alqur'ani.
Anan ya raba dare bai kuskura ya shiga dakin ba, wuraren asuba ya ɗan ajiye Kur'anin ya kwanta yana me lumshe idanun shi. Ai kuwa barci yayi gaba da shi.
Ruwa ne gaba da bayan ta, wanda yake cike da jini makil, kai hannu yayi zai riko ta. Amma ina tayi nisa domin ta nutse sosai, fadawa yayi shima ya hango ta kwance. Daukar ta yayi zai fito fa ita yaji ya kasa motsi daga wurin juyawa yayi zai duba yaga kafarta daure da igiya, gidado ne ya kai hannu zai amshi ta wani ya bangaje shi ya amshe ya,.shi.kuma ya kamo wanda ya dauke ta a hannun gidado bayan ya nuna mishi takobi, juyawa yayi ya zai mikawa gidado ita, aka wurge su da wani mashi... Bude idanu yayi sakamakon jin takobi a wuyar shi, Anum ne rike da takobi tana kallon shi.
"Waye kai? Kai barawo ne? Gaya min waye kai?" Buge takobin yayi daga ita har takobin suka fadi can, sake mikewa tayi, ranta a B'ace ta zata kowa kamar Barkindo yake. Kawai ta kuma tawowa kan shi da takobi tana cewa.
"Sai na kashe ka tunda ka sato Ni" juyawa yayi yana mamakin taurin kai irin nata, kafin ta matso gare shi ya samu damar tsayawa da kyau tana zuwa ya kauce mata, tare da damke keyarta ya D'aga ta cak da kasa. Kallon yadda take mutsu-mutsu yasa shi sake ta, aikuwa ta fadi a kan hannun ta.
"Kasssss" kashin hannun ya bada sauti. Wanda yayi sanadin sumarta.
Sai da yayi Sallah sannan ya koma wurin dokin shi ya dauko kayan aiki ya zo ya kama hannun ya rike addu'oi yayi sannan ya tofa a hannun ya daure mata shi. Sannan ya watsa mata ruwa, ba wai ayayyafa ba, a'a Juye mata yayi a firgice ta bude idanun ta sai lokacin ta ji idanun ta ya cika da kwalla ta ce mishi.
"Kai Azzalumi ne mugu mara imani, Allah sai ya saka min". Ta fada tana matsar kwalla, sunkuyawa yayi zai dauki kayan aikin shi a tunanin ta wani abu zai mata, aikuwa ta fashe da kuka, tana kame kirjin ta. Tabe baki yayi sannan ya dauki abinda zai dauka har tana jin kamshin turaren shi.
"Mugu" ta fada kasa kasa, nan ya juya baya kallon ta,.kafin ya mike abin shi bai kuma bin kanta ba.
"Hala bayan jin ne shima Mugu barawo me kama da yan fashi"
Ita a tunanin ta satotta yayi shi yasa ta rufe idanun ta,.tayi ta gaya mishi.magana abun haushi ko cikanki bai ce mata ba, har ya gama abinda zai yi gari na wayewa ta wuce ta dauki sauran ruwan shi tayi alola, sannan ta gabatar da sallah,.tan idarwa taga ya haɗa wuta yana dumama namar shi, hàdiye yawu tayi.tana kallon shi. Yana halkance da ita amma ko ta kanta bai bi ba, da gayya ya saka namar nan a gaba ya cinye,.aikuwa ya sha bambami.
"Allah ya isa min hàdiye yawun da nayi Mugu me kama da bishiyar kuka,.ka karya min hannu sannan ka cinye kazar jinyata, Allah sai ja gani a ƙwaryan cin tuwon ka, zaka sha mamaki. Idan ba tsoron ba ka bude fuskar ka mana! Yaji tsoron a bashi ruwan madaci ya sha, ragon maza Lusari" wani kallo ya watsa mata, tayi maza ta rufe bakin ta, tana hàdiye yawun tsoro, kafin ta fara kwalkwal da idanu.
"Idan na rashin imani ba, taya zaka cinye abu kaɗai baka ce min bismillah ba, ai ko na maida mugun yawu, Yanzun idan ka mutu wuta za a saka ka...." Wani irin fisgota yayi tare da zare takobin shi ya mai da ita jikin shi yana me buge kifiyar da aka dannota da shi, a hankali mayafin da yake kare a fuskar shi ta warware,aka kuma wurgo musu wani wanda ya dauke rawanin shi da hular baki daya. Tana jikinshi ya sakala hannun shi akan cikin ta, yayi ta kabe harin har sai da mutanen suka gaji dan kan su, suka bayyana sanye da bakaken kaya,juyo da ita yayi da tayi mutuwar tsaye, ya ce mata.
"Rufe idanun ki, ki rike ni sosai"
Kallon shi take sai da ya kuma.daka mata tsawa ta rungume shi tare da boye fuskarta a jikin shi kafin ya samu damar daure ta da rawanin shi ya tam, sannan ya shiga wani irin yakin kota kwana da mutanen da bai san Meye hujjar kawo musu hari ba....
🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️
*Let me waka kai da kazo ganin tsohon ka kaine da shiga yaki na gaya mishi gaskiya ne ko na bari Gobirawa su gaya mishi... Yau na hada muku na yau baki daya domin ba zan yi na dare ba kar ma ku saka rai 👋🔥😍*
#Mai_Dambu

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now