BABI NA TALATIN DA HUƊU

413 125 15
                                    

KALLABI....!
A Tsakanin Rawuna

Mai_Dambu

*EWF*
BABI NA TALATIN DA HUDU
Sannan ya saka kai ya bar dakin, ta kuma fashewa da kuka. Shigowar Innayoh bai hanata kukan ta ba, sai da ta zauna a gefen ta tana faɗin.
"Karki illata idanun ki da kuka mana"
"Innayoh Lamido tsoro yake bani, kowani lokaci sauyawa yake, tsoron kar ya tambaye ni waye shi nake ji shi yasa bana son yana shigewa cikin gidan sarautar nan"
"Taya jini ba zai bayyana kan shi ba? Taya kike tunanin zai zauna shiru haka, matukar jinin Gobir ne, kiyi hakuri amma fa dole sai sun bayyana kan su." Ta gaya mata haka bayan ta bar mata dakin tana jin ta, haka kawai dan tana da taguwar zuciya sai ta hana yaro sakat.
Dan haka Innayoh ta dauki aniyar lallai sai Yaran sun dan asalin su sai tayi kuma,
Dan haka ta zuba ido ta ga yadda zaa boye asalin su, kwatsam ana cikin kokarin ganin ya daina shiga masarautan borno, sai ga shi ya fada fita da yan farauta, abin ya samo asali ne lokacin da suka fita sallah Jumma'a, ya ga shugaban yan farauta ya kai gaisuwa wurin sarki a lokacin, yaji suna bisa kukumo, da kirari kawai sai ganin shi aka yi a tsakiyar su tsugul, ayin juyin Duniyar nan ya dawo Yaron nan yaki fir karshe ma farautar aka fita da shi, Allah da ikon shi bai dawo gida ba, sai da yar barewar shi a kadadar shi, ranar bakin ciki kamar ya kashe Aminatu, kura Mishi ido tayi gashi bata iya duka ba, sam ta rasa ya zata yi da shi.
"Gaya min me kake son kayi? Ka gaya min zan Barka kayi"
"Ki bar ni a bani horon yaki toh" ya fada kan shi a sunkuye.
"Shi kenan Lamido na amince, amma ban da farauta" kallon ta yayi tare da cewa.
"Kiyi hakuri ko banje ba, zasu dauke ni" a matukar firgice ta ce.
"Su waye?"
Tashi yayi ya bar ta cikin tashin hankali, kawai tayi imani ne da Allah amma zuciyar ta, ta kusan bugawa baki daya Lamido sai jangwalo damuwa yake a kan shi..
A gefen Gidado kuwa, bai da aiki sai na idan ya zauna yayi ta rubutun da babu kai babu gindi, idan yaga abu yayi mishi zai dauki alakami da yar battar tawadar shi yana rubutu, Yana son mulki amma yasan ba zai tab'a zama sarki ba, shi yasa duk ranar juma'a idan ya tafi masallaci, bai da aiki sai na rubuta shigar da Sarkin Borno yayi kayan da dokin sa ya saka daban abubuwa dai gasu nan, Allah ya daura mishi shiririta, gason saka kowa farin ciki, baya magana amma duk abinda masu magana suke zaka samu yana yi.
Bayan shekara goma, cikin wani irin zafin nama ya kaiwa sarkin Yaki sara, ya tare, ya kuma kai mishi wani saran ya tare.
"A yayin da zaka fuskanci gaskiya dole kwakwalwar ka,.tafi zuciyar ka sauri dan haka idan jinin Gobirawa ne ke yawo a jinin ka gwada min kai sadauki ne"
Wani irin sara ya kai mishi sai da takobin Sarkin yaki ya rab'e gida biyu, sannan ya saka mishi takobin a wuyar shi.
"Tabbas zaka jagoranci rundunar da zata kasar Chadi domin taimakawa kana domin yakar Sahil" a hankali ya sake takobin yana me sunkuyar da kan shi. Ji yayi an danne bayan shi, fisgo shi yayi, kamar zai buga shi da kasa.
Yana kallon idanun shi. Da yake hango iyakar bashi hakuri da kuma farin cikin.
Zama suka yi Sarkin yaki ta kawo musu ruwa, zama shima yayi sannan ya ce musu.
"Mahaifin ku sarki ne, a masarautan Gobir,.mikewa Lamidi yayi ko ba a gaya mishi ba yasan shi din dan sarki ne a bakin Innayoh, amma ganin kukan da Ammyn take yasa shi jin tsanar masarautar su, kuma yasha jin haka a wurin mai martaba sarkin Borno idan yayi baki yana gabatar da shi,
Rike hannun shi Gidado yayi a kan ya zauna su ji labarin baban su, wani irin duba yayi mishi dan dole ya kyale shi. Sannan shi ya zauna yana kallon sarkin yaki, da yayi ta bashi labarin su, dauko littafi yayi ya fara rubuta labarin iyayen su,
A yanzun yaran aminatu suna neman shekaru goma sha takwas ne, domin suna cikin na sha bakwai ne, dan sun fara mallakar hankalin su, ba kamar Lamido wanda tsabar aikin yaki da horo, fita farauta da sauran su, ya saka shi ya bude har ya fi Gidado budewa. Shi kan Gidado cewa yake ba zai iya aikin wahala ba, dan Lamido ya saba da wahala sai yayi ta yi.
Bayan ya gama rubutawa, ya mike yana dariya sannan ya bar wurin yana godiya.
Allah cikin ikon shi ya raba musu halayyar su, yayin da shi Lamido ya gado jinin gidan su, sai gashi Gidado ya dauki halin baffa'm baya son rigima babu ruwan shi da hayaniya asalima dai idan har tafiya ta tafi ba mamaki baffa'm ne domin yana son abinda zai saka shi farin ciki, ko sau daya bai taba rike takobi ba, kai Gidado tsabar bai kaunar rike takobi ko kaza wannan bai saka kan shi ya yanka ba, domin kiri kiri ya ce musu da hannu shi ya auri alkalami,.kamar yadda Lamido ya auri takobi, haka Allah ya rabawa kowa abinda yake ganin shi ne ra'ayin shi.
*
Masarautar Sokkoto.
Inna Marwa wacce shekaru suka haura mata ce zaune tana kallon Baffa'm da yake ta rubutu yana ajiyewa.
"Bello jiya Galadima ya zo kana barci"
"Inna" ya fada yana sake alkalamin hannun shi.
"Eh yana nan shi da Sarkin Gida zasu zo an jima" a hankali yayi kamar zai tashi sai ya koma ya zauna sai ga hawaye sharrr.
Da wani ido zai kalli galadima? Me zai cewa galadima? Me zai ce musu, ya ce musu shima dan yana da sauran shan ruwa ne yake raye ko me? Bai san halin da Waziri Zakaria yake ciki ba, tunda shi yaro ne, ya so kwarai da ya gaya mishi ya bar masarautar domin zasu iya kashe shi.

"Kuka kuma? A'a ai ba naka bane, shi yasa muke addu'ar Allah ya haɗa mu da mutanen arziki. Gashi Allah ya haɗa ka da Nafi'u kuma yana tare da kai ba dare ba rana, duk abinda ya faru baka da laifi, haka Allah ya ƙaddara sai haka ya faru kafin ka iya gane dama can kai ma da laifin ka, ni da kaina na gaya maka soyayyar ka da Aminatu itace hanyar da za'a iya farraka ku amma ka yi kunnen uwar shegu, Allah na tuba gidan sarautar da tun daga haihuwar ka ake binka da Idanun balle kuma an san ta yadda za'a yake ka, fir kaki ji toh gashi nan dai kana ki kana gani sun shiga kyakkyawan alakar dake tsakanin ku" tana gama fadar haka ta mike tana me barin dakin, shafa gefen wurin kwanciyar shi yayi yana me dauko wani jakar fata, a hankali ya juye yayan jigidar ta, yana kallon hawaye na zuba mata. Ranar da ta fara shiga turakar shi ya tuna, da lokacin da ya kwashe jigidar ya ajiye yana kallon su da idanun basira, kafin ya cigaba da goge fuskar shi,
"Ina sonki Aminatu sai dai lokaci ya kure da zan kuma samun damar da na samu, duk inda kike Allah ya jibanci al'amarin ki" ya fada yana sake wani irin kuka me ban tausayi, shine gaskiyar abinda yake ji, shine gaskiyar abinda zai iya faɗa yana ji a kanta.
*
A can wajen masarautar kuwa, Galadima ne da Sarkin Gida, bayan sun gama gaisawa da Yaran Inna Marwa, suka nufi dakin da yake. Da sauri ya shiga tattara kayan shi, da ya ciwo.
"Assalamu alaikum!" Suka shiga mishi.
"Wa'alaikumunsalam!" Ya fada a raunane, suna shiga ya ga galadima wani sunkuyar da kai yayi, sam yaki d'ago kai ya kalli waziri.
"Sarkin gida yaushe na zama Surukin wannan bawan Allah?"
"Ba mamaki tunda akwai aure a tsakanin su da Maimunari" kallon juna suka yi kafin ya ce mishi.
"Kuma wallahi sai yanzun na tuna zan iya bashi auren Maimunari, toh ka zama shaida kafin Aminatu ta bayyana, na bashi auren Maimunari" da sauri ya d'ago kan shi. Murmushi Galadima ya sake mishi.
"A'a galadima, ita ɗaya na mallakawa kaina don Allah karka kawo min wani tashin hankali"
"Toh kunyar uwar me kake ji? Kunyar me kake ji a kaina? Sauke min rawanin da na gada tun iyaye da kakanni da kayi ban haushi ba, mara mutunci kawai"
"Kayi hakuri"
" Da ban yi hakuri ba, ba mamaki da takaicin ka ya tsiro a gadon bayana, Ina Zakaria?" Ya tambaye Baffa'm,
Girgiza mishi kai yayi yana kallon kasa.
"Ban san halin da yake ciki ba, nima Sarkin gida ne ya dauko Ni" kallon sarkin gida yayi sannan ya ce mishi.
"Ban gane ba, ya aka yi?"
Zama suka yi suna kallon sarkin gida.
"Allah ya baka nasara, galadima al'amarin da ban mamaki a ce matar da ta haifi d'a da kai ita take yunkurin ganin bayan ka."

Waiwaye adon tafiya.
Lokacin da Waziri Zakaria yayi aure toh gaskiya baya samun damar zuwa duba Baffa'm sai Bingel ta maye gurbin shi, tana saka Sarkin gida ya daga mata shi ta bashi abinci da magani, ana cikin haka ne ya fara gano jikin Baffa'm ya fara nauyi sama da ace kunyar ta fi haka, dan haka ya dauki abincin da take bashi ya kaiwa wani me magani anan ne yana samu har da gubar maciji ake saka wa kadan a cikin abincin, wanda yana ci a hankali yana shiga jikin shi, tare da kassara duk wani laka da wani kuzari a jikin shi, dan haka me maganin ya yi tsam da ran shi ya ce mishi.
" Ka ɗauke shi daga cikin gidan, ba iya gubar bace matsala idan ya fadi ya mutu kai ne abin zargi, ga shi wannan guru ne, wannan layya ne ka saka ka kudiri inda kake son kai shi, ku bar gidan"
Wannan dalilin yasa yana komawa gida, bai tsaya ba, ya je yayi sallama da matar shi, sannan ya shiga cikin gidan sarautar ya dauke mai martaba suka yi layyar zana. "Sannan ba iya yau ya fahimci Bingel tana bibiyar lamarin ka ba, na sha kamata tana makalewa tana jin abinda kuke da Aminatu, na sha kamata tana niman hanyar da za zo gare ka. Allah ya huci zuciyar ka, Bingel ita ce ta bawa Makiya damar cimma maka"

Lumshe Idanun yayi tare da bude shi akan galadima.
"Ku mai dani masarautar" wani kallon da suka mishi kafin suka kwashe da dariya, sannan suka ce mishi.
"Da kafarka zaka koma ba yau ba, ba gobe ba. Akwai lokacin da saka koma a yanzun ma balaiin da suke ciki ya ishe su, muna kai ka kuwa kwaɗo zasu yi da kai wallahi, ka bari dai ka jira lokacin sai mu koma ai ba damu koma ba, sau abinda Aminatu ta dauka ya dawo"
*Zan tafi amma ka zuba ido ka ga abinda zai hanaka gani*
Kalaman ta da alwashin ta, ke yawo a jinin ta, kura mishi ido suka yi.
"Yarima Yazidu ya girma"
"Dole zan koma, amma ba zan zauna a cikin masarautan ba, ina bukatar mahaifata"
"Duk mun sani amma dole mu jira ko, domin yakin da yake gaba yafi wanda ya tsallake, ina yawan bincike akan abinda Aminatu ta haifa, kamar yadda na gaya maka tun farko zakuna biyu ne zagaye da ita, ban san me haka yake nufi ba, ina fatar Allah ya gajarce mana wahalar jira"
Haka suka yi ta tattaunawa har dare yayi abinda ke fidda su sallah da cin abincin.
**
M. Gobir

Tsaye yake rike da takobi, ya juya ya ya kuma juyawa, kafin ya cillar da shi. Yana b'ata rai.
"Ni fa ba zan iya yaki ba, wallahi ba zai kashe kaina a banza ba"
Aikuwa da sauri sarkin yaki ya taso yana faɗin.
"Kai min rai Barkindo, wannan umarnin Fulani Bingel ne"
"Kai na ce ba zan iya dole ne sai na yi yaki ji min fa ba zan iya ba"

*ZAN YI AMFANI DA WANNAN DAMAR NA TALLATA MUKU SABON LABARI NA ZAYN MALIK PAID BOOK ONE♡300₦*
#Mai_Dambu
Na cika alkawari... Ku taya ni sharing🤣😂😂

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now