BABI NA ARBA'IN CIF

395 116 14
                                    

BABI NA ARBA'IN CIF
https://youtu.be/UMtk8EpcIUI
Please subscribe

Shiru yayi na wani lokaci kafin ya dauke kan shi, cikin wani miskilin yanayi yana kallon kasa kafin ya ce mata.
"Don Allah ki bani aron shi."
"Ba zan ba da Yarona ba, kayi tafiyar ka Allah ya tsare" ta fada da Murya me nuna rashin amincewar ta.
Baki daya abin sai yazo mishi bakon yanayi bai tab'a magana da ita ba irin yau kuma a madadin tayi hakuri sai na kafewa da tayi.
Duk sai ya rasa inda zai sakata, kawai ya cigaba da zama a gaban ta, ai idan ta gaji zata hakura. Ita kanta so take suyi hira da ita, so take suyi farin ciki taji damuwar shi amma mutumin nan ko nace bishiyar kuka zama yayi yana kallon kasa, sai da Innayoh ta kawo mishi dafaffe madara ta mika mishi.
"Uwargijiya ta, ki mishi hakuri mana ki bashi Aron dan ki, dan zinari"

"Innayoh!" Ta kira sunan ta, tana kallon shi.
"Ko sau daya ba zai zauna da ni mu zanta irin na d'a da uwa ba?"
Da sauri ya d'ago kai yana kallon ta, abin da ya fahimta, halin shi na ko in kula yana tab'a zuciyar Ammyn su, kamar yaro karami ya kara zama a gaban ta. Bakin shi yana rawa, sai yayi kamar zai magana sai yayi shiru, kura mishi Idanu tayi kamar ta rufe shi da duka, shigowar Gidado yasa shi sauke boyayyen ajiyar zuciya, kan shi a kasa zama yayi kusa da shi yana cewa.
"Ya naga kunyi jugum jugum? Wani abu ne ya faru." Ya tambayi Ammyn su, bayan ya amshe kofin madaran Lamido ya sha rabi,
Kallon su take cikin so da kauna, yadda Allah ya haɗa mata mutane biyu ma bambanta hali.
"Wai zaku tafi karatu ne!" Ware idanu yayi akan ta yana kara tambayar ta.
"Inji waye? Da gaske kuma?"
Nuna mishi Lamido tayi.
"Don Allah ina zamu? Gobir?"
Rike hannun Gidado yayi yana girgiza mishi kai lamido yayi.
"Makaranta zamu na tsawon shekaru uku zuwa hudu, kafin nan ayi dacen samun maganin ka ko" murmushi suka sakarwa juna da hannu yayi mishi alamar ya amince..
"Yaushe xamu tafi?"
"Sai Ammyn ta amince"

Ya fada Mishi yana kokarin boye damuwar shi, haka Allah yayi shi. Ba zaka tab'a gane asalin damuwar shi ba, a gaban ta ma kokarin yake ya boye gajiyar da yayi da maganar da suke, dan haka ya koma gefe ya kame kan shi kamar ba shi ba, haka tayi ta jan su da hira, wanda baki daya nasiha ce, da nuna musu girman Allah da tsoron shi, kafin ta dire aya tana cewa.
"Ka saka min idanu akan shi, kusan shi amana ne a gare ka, don Allah kar ka bari wani abu ya same shi, bayi da baki kaji"
"INSHA ALLAH" ya fada tare da kokarin mikewa daga gabanta dama tasan za ayi haka domin baki daya kamar mara gaskiya, shi kan shi ba zai ce ga hujjar shi nakin sakewa da ita ba, amma yau ya zame musu rana me daraja, domin har sun yi hira, dan shi dai bai shiga maganar ba, idan tayi tsawo ne yace eh ko a'a. Da wannan yanayin ya bar su, ya fita wajen gari..tunda ya fita a masarautan ya nufi bayan gari, a nan ya zauna yana busa sarewa.
**
"Ba zaka tab'a zama sarki ba, amma tabbas idan har ka cika wandnan sharudar zaka cigaba da taka kowa ba tare da an fahimta ba, ka fahimci wani abu ba zaka zama sarki ba, sai dai ka nimawa Dan ka yarinyar da take da zubin halittar matar Bello an kuma haihuwar ta, idan kai ka ce zaka yi zaka iya mutuwa, domin nan da wasu lokuta wata guguwa me hade da dunkulen siffar Zaki zata kuma bayyana.."
Wani irin baki da farin hayaki ne suka hadu wurin guda suka fantsamo sama kamar zasu duke fuskar shi, kare fuskar yayi yana kallon bokan..
"Ba zan tab'a barin haka ya faru ba"
Dariya bokan yayi sannan shiga yiwa kan shi kirari.
*
Allah ya bashi sa'a ya fito daga masarautan ta kofar bai, duk da ya samu sama da shekaru yana zuwa dajin, kusan kullum idan ya fita niman ta baya samunta haka yau har ya cire rai zai same ta, ya jiyo sautin wakar ta, cikin sassanyar murya wacce ta karade sunkurun da take da shanun ta, yar kimanin shekaru goma sha huɗu, sandar kiwon da yake kafadar ta, sanye take da farin kayan saki ta asalin Fulanin usul, gashin ta da aka mata kitson doka ya sha wuri da wasu tsagiya, cikin harshen gurbataccen Hausar da zaka fahimci kamata ake tana kwacewa take rera wakokin hausa musamman wanda ake a dandali, wanda daga baya aka sabunta shi, K'ugunta cike yake da wurri, wanda aka ajera su kamar jigida, ba kasafai ake samun yan mata da shigar wurri ba, a rugaggen Fulani amma ita an makara mata wurrin ne sakamakon karfin yanayin ta, da idan aka mata abu wasu, ba zata iya kome ba sabida mugun ta, sannan masu taimaka mata ba zasu iya cutar da kowa ba..
_Charman duddu charman duduwa charmagade_
_Charman duddu charman duduwa charmagade_
_Akwai wani bako a gidan mai gari Charmagade_
_Baya sallah bayan lazimi_
_Charmagade_
_Baya nima 'Yan matan gari_
_Charmagade_
_Ko ya nima wai zai ba shima_
_Charmagade_
_Innata landiyo mana_
_Baba na Landiyo mana_
_Charmagade_
A hankali ta fashe da kuka, cikin shashekar kukan ta cigaba da wakar.
_Don Allah mai Tafiya ka jira ni sako zan baka daure ka kai ga masoya_
_Yarinya kyakyawa lamarin ki na ban mamaki_
_Don Allah mai Tafiya ka jira ni sako zan ba daure ka kai ga masoya_
Ita ke wakar ita ke amshin, baki daya jikin Barkindo ya mutu sabida tana wakar ne cikin Kadaici da tarin kewa.
Dan haka bai yi kokarin dakatar da ita ba, asalima sai ya lame a jikin itacce yana sauraron zazzakar Muryan ta.
_Don Allah mai Tafiya ka jira ni duba_

_Sakon nuna sauri ne don Allah ka karb'a! Zaki yi mamaki sakon da zan zaka kaii_
_Shi yayi alkhairi da na juya ban kuma cimma ba_
_Don Allah mai Tafiya ka jira ni sako zan baka daure ka kai ga masoyina_
_Akasi akan hanya...._
"Washhhhhhh" ta ji an fada da ƙarfi yasa ta juya da sauri itama, Barkindo ne ake dambe da shi wasu mutane,
"Auya maza kisa sake ta" ta fada cikin rashin tsoro,
"Jarmai ka amshe sandar hannunta ka kwala mata a kafa. Naga ma yar budurwa ce, maza yaga mana rigar mutuncin ta kafin mu kar wannan anan"
Wani juya sannan tayi tare da d'aga shi sama.
"Eeeyyuuuuu idan wani ya tako nan sai na sanya shi ya manta da nonon mamar shi maza ki zo"
Matsalar bata iya banbance mace da namiji, a waka zata banbance amma ban da a magana fatar baki.
Dake sakarai ne sun zata cika baki take, yana zuwa kuwa da Allah ya bata sa'a ta juya sandar ta muka mishi a hakarkari sai da ya fadi sumamme.

Bakar zuciya ne da ita, da shi ta kwaci kanta a cikin gidan su. Dan haka kiwo ya zama mata jiki ne, amma bata yarda wani yaci zalinta a ynzun duk da kuwa an dakatar da yanayin ta, da gudu wanda ya rike hannun Barkindo ya juya tare da barin wurin, cikin takaici ta kalli Barkindo. Sannan ta tab'e baki.
"Anum" ya kira sunan ta yana mikewa, riko damtsen hannun ta yayi, a fusace ta juya zata mishi magana yadda ya narka da fuska sai da ya kashe mata jiki baki daya.
"Ban iya ba, ba zan iya ba, asalima ba a haife ni domin yaki ko kare kai ba, amma qaddara ta samar da ni ta hanyar da kullum hango mutuwa nake" fauce hannunta tayi ta cigaba da wakar ta.
_Shi yayi banbanci wurin kyau da hali da nagarta da shi zaka mika turare na_
_Don Allah mai Tafiya ka jira ni sako zan baka daure ka kai ga masoyina_
"Don Allah ki saurare ni" ya sha gabanta.
"Na yarda ki koya min fadar kare kaina dogara sandar kiwon tayi ta daura hannu a kai tana kallon shi.
"Bani da wayo na rasa iyayena Mahaifiya ta da mahaifina, har yau ina fuskantar cin zarafi daga kakata. Abinda ma dauka a shekaru goma baya a yanzu babu wanda zai takani na kyale shi. Ni Marainiya ce, amma ba mara zuciya ba, idan ka ga an cutar dani nice naso haka bani hanya"

Ta rab'a gefen shi, garin yabi bayan ta, aikuwa ya taka mugun naya,
"Wayyo Allah na!" Ya fada da karfi, juyawa tayi ta kalle shi, takaici ya kuma turnike ta. K'aya ce fa.
Wani dauke kai tayi, ta tawo kan shi. Ba tare da ta ce mishi kalla ba, ta durkusa tare da kai hannun ta kan takalmin shi me zubin kayan jikin shi, wanda ya nuna daga inda ya fito.
Ta kama kafar, ta zare da karfin tsiya. Wani bincikota yayi, cikin jin haushi ta fallawa fuskar shi mari, ji kake.
"Tassss" wanda yayi daidai da zuwan Mandiya da wasu bayin Bingel. Da sauri ta fara kokarin mikewa amma ya rike ta da karfi.
"Anum me yasa?"
"Har abada tsakanin mu akwai babban iyaka" sannan ta mike tana me daukar sandarta, baki daya wani mugun kunya ce take dawainiya da ita, yadda take fa bakin jini a rugar su, bata san me yasa Barkindo yake mata haka ba, Asalima dayawan mazan rugar su, hanyar da tabi basu bi, domin suna kiranta da annoba, wasu kuma mayya suke kiranta. Sakamakon yanayin ta da idan ranta ya ɓaci zuma suna iya kusan hallaka mutum akan ta, a wannan bangaren ita kanta Inono ta razana shi yasa tayi kokarin dakatar da ita kafin ta zame musu annobar, ta ci wahala a hannun su shekarun baya amma a yanzu babu me ko lakatar ta, daga manya har yara kowa shakkar ta yake, duk ranar da suka dake ta Insha Allah, basu ba barci cikin salama, daga baya kuma duka da azaba yasa ta koyi wani mugun zuciya. Tun tana da shekaru goma sha daya ta fara dambe domin kwatar kanta, sosai take cikin uban Yara, haka yasa kowa ya kama dan shi, domin sunce kashi guda gare ta, idan ta damfara yaro ko yarinya da kasa sai kashin sa ta karye, idan kuma kaifi karfin ta idan ta kama ka sai ka sha mugun wahala domin ji zaka yi kaman ana dukan ka da danyen itacce.

Wannan halin nata yasa aka kyale, suka shafawa kan su lafiya, ta bangaren tallar kindirmo, idan ta dauka da izinin Ubangiji sai na ta ya kare na sauran yaran bai kare ba, shima duk ranar da take jin nishadi take daukar na Inono, idan kuwa aka sata dole ta dauka Insha Allah haka zata dawo da shi ya lalace har na sauran Yara, wannan yasa tafi son tafiya kiwo, domin idan ta shiga cikin gari talla maza kamar zasu kamata su boye ta, musamman da Allah yayi mata diri tun bata cika budurwa ba, akwai diri, gata kana ganin ta kaga bakar labarabiya, wacce take da sirki da kabilu biyu,wanda ya hadu da fatar ta ya haifar mata da wani irin dubun fata me kyau(dark brown) idan ta samu wasu shekaru zata fi haka tsawo da cikar halittar jikin, kugun ta kamar wanda aka zana mata shi domin duk wanda ya san kalangu haka Anum take, a yanzu da yan kananun nonuwarta da suka fara tasowa idan suka fi haka tabbas za ayi kerarriyar budurwa ce da babu irin ta a cikin rugar su, idan tana tafiya kuwa zaka ratse da Allah tana yanga ce nan kuwa haka tafiya yake, shi kan sa Barkindo a da can tausayi ne yake kawo shi wurin ta, tun bingel tana hana shi zuwa har ta fahimci duk lokacin da bai zo ba, kamar zai mutu yayi ta mata abin kunya kenan ko yayi ta tsinkata a gaban bayin ta, sai dai wani harin da aka taba kawo mishi yasa ta haramta mishi fita daga masarautan....
#Mai_Dambu

KALLABI..! A tsakanin Rawuna...Where stories live. Discover now