page 45

258 36 10
                                    

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...45....

A bakin kofar gidan anty nafin hajiya Aisha ta sauke sumayyan.
Fitowa tayi daga motar ta nufi gidan,har zata shiga sai taga karamar yarinyar ta tafito daga dakin.
"Anty sumayyah mamata tacemin na fadamiki wai batan ki tafi kawai"
Jimm sumayyan tayi kafin ta tsugunna a gaban yarinyar,
"To shikenan babyn mama,kicewa maman ki ina gaisheta kinji,kuma zanyi kewarta sosai goda bamu hadu ba kinji"
Daga kai yarinyar tayi tareda wucewa cikin gidan,shuru sumayyah tayi tareda juyawa ta bar gidan.
Duk abinda yake faruwa anty nafi tana kallon su ta window,rife bakinta tayi ta hannunta saboda ta rike kukan dayake kokarin zubomata,allah yaga tana jin tausayim yar uwartata amma kuma bazata juri gainin a yanzu ba gaskiya.
Har sun kam hanya zasu tafi gidan hajiyan sumayyah tasake kallonta tareda cewa,
"Dan hajiyah ko zaki kaini gidammu kai"
"Kai sumayyah wai bazaki kulada halin da ake ciki bane,kowafah bazai kalleki ba a wannna lokacin,koda zasu dubeki badai yanxu ba gaskiya,anty nki ma dakika je gidan tana nan fah,kawai bataga damar ganinki bane,ina ga kuma babanki yanda nake jin labarin sa"
"Hajiyah hanlalina baxai kwanta ba idan na saba umarnin hajiya mama,tace duk rintsi karna bar gida,hakan zai karamata tashin hankali ne"
"To shikenan tunda kince,hakan muke fata dama"
Karkarta motarta tayi zuwa gidan su sumayyan,duk da yanda kirjinta yake bugawa amma hakan shine yafi,koda iyaelyenta zasu yankata bai kamata ta kaurace musu ba.
A bakin kofar gidan ta tsaya tareda buga get din gidan,mai gadi ne ya bude ya fito tareda kare mata kallo.
"Uhm abbah yana gidane,ko zan iya shiga"
"Ahah kiyi hakuri ranki ya dade,inna barki kika shiga gaskiya aikina zai samu tangarda,dan haka ki tsayah barina je nayimiki magana dashi,idan ya barki to ina bai barki ba wannan kuma bai shafeniba"
"Cikin magana kamar yanajin haushinta yake maganar"
Hhhh wannan masifa haka,gidan ubanka sai maigadi ya yarda ka shiga,tsayawa tayi ita da hajiyah Aisha wanda ita kuma ta koma mota ta zauna,dan bata shiryah haduwa da mahaifin sumayyah ba.
Kallonta abbah yafara sama da kasa cikin tsana da kuma haushi da kuma takaici.
"Me kikazo yi nan wajen,waye yabaki damar fitowa daga cell din danace a kulleki?"
"Abbah  ina hajiya mama?"
Me zaki mata,karisa kasheta zaikiyiyanzun saboda wancam bai miki ba abinda kikayi,karkiyi tunanin ma zaki shiga cikin gidannan"
"Abbah  bani ce na turet..........."
"Kiyi Shiru anan wajen,ban yarda ki sake cewa wani abu,bakinki baya furta alkhairi bare kuma aikinki,sannan kuma daga yau ki manta da gidannan dakuma abinda ya shafeshi,ban yadda nasake ganinki ba daga yau,kibar rayuwar kowa ya huta dake"
Yana gama fadar hakan yakoma cikin gidan tareda buga kofar da karfi.
.!....karki sake cewa komai daga yau......! ki manta da gidannan da abinda ya shafeshi ........! ki fita a rayuwar kowa ya huta.......!
Wannan sune kalmomin dasuke yawo a cikin kan sumayya suka cikin kanta,take jinsu ta ko ina daga inda sauti yake fitowa.
Dafe kunnuwanta tayi jiri jiri yana dibanta.
Hajiyah Aisha daga mota ta hango barin abbah a wajen da kuma abinda sumayyan take kaman zata fadi.
Dadai isowar hajiyah aisha wajen tasaki wata kara mai karfi ta fadi a wajen sumammiyah.

Bangaren maryam kuwa tun safe a ranar ta uku ta farfado amma taki cewa komai sai kallon kowa take da ido.
Sai kusan yamma kafin tasaki kuka mai karfi.
Yayar tace a wajen lokacin da taji kukannata,wanda hakan yasa tatafi kiran kowa domin ta fadamusu halin da ake ciki.
Mahaifiyarta ya yayunta biyune suka zo wajen da kuma su inna ramma da iyah,sai Ahmad kuma yah mu'azzam,wanda suna tareda Ahmad lokacin da'aka fada masa halin da ake ciki.
Da sauri suka iso asibitin lokacin ta daina kukan sai bain mutane da take da ido kawai.
Yunkurin tashi take amma mamarta innna Rakeeyah tayi saurim dagatar da itah,dan ance kwakwkwaran motsi ma kar tayi.
Ta dan sha tea dai kadan amma magana kam babu abinda tace.
Yayarta ce wacce ita dama a gida take ta matso inda take tareda cewa,
"Ki kwantar da hankalin ai wlh dolema a karba miki hakkinki,yanda ta miki wannan danyen aiki itama sai hukunci ya hau kanta,haka kawai kishi haukane"
Kallonta maryam tayi da mamaki tareda cewa,
"Wacece tayi wani abu?"
"Sumayyah mama data tureki kika fadi,dan mugunta ko kin manta kai,inaga sai an miki scanning din kwakwalwa ma"
"Sumayyah kuma,mai hadin sumayyah da faduwar danayi,tabbas nasan muna fada kam,amma ita kinyin fadan tayi,hasalima tafiya tayi ta barni soboda gudun kar na sami matsalar.
Ba sumayyah ce ta tureni ba kujera ce ta sakali zanina na fadi,wannan wajen na jikin kujera dakake ta cewa zaka gyara shine ya ja zanina,kaima yasha kama kayanka ai idan zaka fita"
Zaro ido kowa yayi tareda kallon maryam din,da kuma sauraron abinda take cewa.
Ganin kallon da suke matane yasa ta cewa,
"Yana kanku haka,ina sumayyan ne banganta ba,ko wani abu ya sameta ne"
Ahmad ne ya sunkuyar dakai tareda cewa,
"Mai gadine yace mana ita ta tureki kika fadi,dan ya shiga yagamta ta shake miki wuyah,kuma ta fita daga gidan da sauri,shiyasa muka kaita police station tun ranar,yanxu haka tana can"
"Police station kuma"
Maryam tafada a raxane,tareda kokarin tashi,saurin dakatar da ita sukayi daga tashin,zuwa sannan har idonta yafara kawowa hawaye
"Sumayyah ki yafemin duk laifina ne wlh,kin iya kokarinki dan gujewa shiga lamarina,harkar gabanki kikeyi bata wani ba amma duk da hakan saida kika shiga zargi"
Nan maryam ta kwashe abinda ya faru ranar ta fadamusu.
Kowa sallalami ya fara,tareda jimamin lamarin,musamman ma Ahmad daya tuna abinda yafada mata lokacin daya je police station din,lokacin zuciya na dibanshi,sanann kuma ya tuna da abinda ta fada masa na nadamar da zayyi,gashi kuwa yana nadamar yanzu,saidai anya kuwa lokaci ya kure masan?.
Da sauri ya tashi shida yah mu'azzam suka nufi police station din,suna zuwa ko sallama basuyi ba suka fara tambayar sumayyan.
Wani police ne a gefe yace,
"Ogah Indai Wacce kuka kawo ce ai anyi belinta tunda safe"
"Tunda safe kuma waye yayi belinnata?"
"Wata hajiyah ce,kuma gaskiya bansan sunan ta ba,ogah dai yasanta,amma baya gari ya tafi wani aiki,sai jibi zai dawo"
"Bani number says yanxu nan nakirashi"
"Kayi hakuri inda ya tafi babu service koka kira ma ba lallai ka sameshi ba gaskiya,dole sai ya dawo dai"
Yarfe hannu Ahmad yayi tareda cire hular Kansa yana fifita da itah lokacin da suka fito daga cikin police station din. Kallon yah mu'azzam yayi wanda yakasa cewa komai,tabbas sun aikata abinda bai daceba sosai,sunyi abinda yanzu gashi suke nadama.
"Mu'azzam kaman yanda tafada zanyi nadama gashi ina nadamar kuwa,meyasa banyi bincikeba nabari haushinta danake ji yafi gane rashin laifinta a lamarin,ni kaina shaida ne cewa sumayyah tasanja amma kuma nakasa gasgata hakan lokacin daya kamata,kaico nah da wannan hukunci dana dauka.
Shin waye ma tayi belinta bamu saniba,idan mai mugun nufice tashiga wani halin wlh laifinmu ne,kuma har abada bazan iyah yafewa kaina ba mu'azzam,saboda itadim matatace tana karkashin ikona,amma ban kulada hakanba ,kaico nah da rikon danayi mata mu'azzam"
Kuka Ahmad ya rushe dashi tareda kifah kansa aka sitiyarin motar tasu,abin ba karamin girgiza mu'azzam din yayi ba,dan shima ba karamin nadama yayi ba,basu rike gurbinsu na yan uwa ba a gareta,gashi ta bacewa ganinsu a yanzu.
"Mu'azzam inason sumayyah fiyeda yanda nake sonta a baya,nakasa furta matane kawai,a tunanina sainbi abun a sannu,saidai yanzu ina nadamar abinda nayi,yanxu gashi nafi Koyaushe dokin ganinta lokacin da banida tabbacin sake ganinta"
"Karka ce haka,Ahmad ni kaina shedane sumayyah ra dabance a zuciyarka yanxu,amma ba abinda zaka tsaya yi kenan ba kuka,kamata yayi ka tashi mu san abinyi,shine abinda yafi dacewa"
Direct gidansu sumayyah suka wuce, daga wajen.

Bangaren hajiyah aisha kuwa da kyar ta samu tasakata a mota ta nufi asibiti.
Tundaga bakin kofar suka karbeta tareda shiga da itah,har sannan tana sume.
Ta kusa awa biyar a sibitin har wajen la'asar kafin likitan ya kirata,da sauri ta nufi office dinnasa tareda kaguwar jin mai yake damunta,dan jin sumayyan take kaman yar ta ta jini.
Kallon hajiya mama yayi cikin tausayawa kafin yace
"A gaskiya hajiya abun akwai abin dubawa a ciki,saboda abune gagarumi,da farko dana dubata naga kaman buguwa tayi shiyasa na turata neurologist su dubata,amma kuma da result ya fito yanxu sunce ba buguwa tayi ba.
Akwai wani reaction daya shiga kwakwalwarta wanda mu zai iyah daukarmu kusan wata biyu anan kafin mu mushawo kanta matsalar idan muka dorata akan magani,wamda kwanciyarta hakan kuma zai iya jawo ta samu mental problem"
To doctor yakake ganin za'ayi toh"
"Eh inaga idan kuka kaita Germany su sunada na'aurorin da zasu iya shawo kan matsalar a sati biyu,inaga idan zaku iya tafiya can to hakan yafi gaskiya"
"To shikenan doctor nagode ,"
Hajiyah Aisha na fitowa daga office din ta Kira shugabanta na abuja ta fada masa,dan dama akwai wata gasa ta kasa akan design da sukeso sumayyan tayi.
Fada masa halin da take ciki tayi da kuma abinda yake faruwa,inda yace shima zai fadawa shugabar mai daukan gasar,dayake macece,kuma tana kasar china.
Can kusan magriba yasake kiran hajiyah Aisha tareda cemata,
"Hajiyah kinsan abin ba nawa bane na dr.munawwarah ne,itace tace zanen sumayyan ya burgeta,yanzu nayi mata maganar halin da'ake shiki da kuma matsalar data samu,tace a cikin satinnan a samu jirgin dazai tafi da ita chinan tunda can ma zasu iya maganin,kedah ita kuje can din,zata dau nauyin aikin daza'ayi matan"
Wata kabbara hajiya aisha tayi tareda cewa,
"Ikon Allah mai yadda yaso,gani ga designer munawwarah ,wai tasan da zamana nikam naji dadi sosai,allah ya yanke miki wahalarki inshaallah sumayyah,dannasan zata koya miki abubuwa da dama,yanda batada da ko d'aya,sai tarin dukiya da kuma taimako.

Tun a ranar hajiyah aisha ta fara neman visa sannan kuma asibitin suka ce zasu kaita har cikin jirgin a matsayin patient dinsu,dan gobe take son ta tafi tunda an samu jirgin dazaije can din da yamma,gudun karma yan uwanta su sani,dan yanxu bakaramin haushinsu hajiyah Aisha takeji ba ,ita babu dama taje yanxu,saidai daga baya taje dubota.

Su yasriba za'a keta hazo gobe,dannasan ko a makalen tayar jirgi zaki makale...........

🏵*sadi-sakhna ce*🏵


Gashinnan but please help me in the next app

Arewabooks

KAICO NAHWhere stories live. Discover now