Page .....26....

248 21 0
                                    

     🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵

           
    🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
    ..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Wattpad:SAKHNA03

🏵🏵🏵
...26....

Tunda sumayyah ta tashi tabar maryam a zaune bata tashiba,saima tagumi da tayi tareda tafiya wani zurfin tunani na daban.
Idonta kuwa yana tsaye kyam akan hanyar da sumayyan tabi,komai take tunani Allah masani.
Jin da tayi an dafa kafadunta ne yasata juyawa dan ganin waye,duk da daga kamshin turarensa tagane waye amma kuma hakan bai sa ta gagara juyawa ba.
"Yah Ahmad "
Shine abinda ta fada a hankali a kasan makoshinta,
"Uhm mekike a zaune ke kadai,naga mood dinki yah sanja dafatan lafiya koh"
"Lafiya kalau,kawai dai ......uhm babu komai "
"Babu komai kaman ya,tayimiki wani abune kafin ta tafi,fadamin mai tayi miki,dama nasan said tayi wani abun ai"
"Ahah babu abinda tayimin,kawai dan ina kikarin fada mata ba lafinta bane shine taji haushi ta tafi,fushi take dani wai dan naki jin haushinta akan abinda tayimin,shiyasa tace bazata nemi yafiyata ba harsai nagane tayimin laifi,amma taya ka gane cewa tare muke zaune da sumayyah dazu?"
"Hmm gaya bazan saniba,nazo nemanki saina ganku a zaune,shiyasa na koma domin ku gama tattaunawa,ni banason tarayyarki da ita yanzu,kwata Kwata ba abar yarda bace ita,zata iya yimi ki wani abun"
"Dan Allah kadaina fadin haka,babu abinda zatayimin da izinin Allah,hasalima ita bata cutar da mutane irin wadda kake nufi"
"Naji,yanzu dai tashi mutafi gida dare yayi,sai gobe kuma idan Allah ya kaimu"
Daga haka Ahmad yaja hannun maryam suka kama hanyar motarasu,duk abinda suke sumayyah tana kallonsu daga inda take zaune,duk da bata jin abinda suke fada amma daga yanayin fuskar Ahmad tasan fushin dayake ta dalilinta ne.
Bayan sun tashi sun tafine ta sauke ajiyar zuciya tareda sake goge hawayen fuskarta,tabbas ita kanta sheda ce kirkin maryam sai an tona,koba komai Ahmad yayi sa'ar mata a rayuwarsa.
Ita kuma haka Allah ya azurtata mutanen kirki a lokacin baya,amam ta kasa ganin hakan har saida lokaci ya kure mata tukunna.
Tana cikin tunanin ne Muhibba ta nufo wajenta tareda cewa,
"Sorry aunty sumayyah nasaka ki jirana,wlh mun hadu da friend dina ne da kuma uhm.....kaninki"
"Murmushi sumayyah tayi mai sauti jin abinda muhibban tace,
"Ban jiba sake fada naji,kika hadu dawa ye?"
"Kai anty karki saka naji kunya mana,yace ma muzo ya kaimu gida"
"Eh lallai mashaallah,muje mana kinga nasamu na gaisa dashi,naga shin zai iya rike min ke,idam ba haka ba hmmmm yasha masga"
Dariya Muhibba tayi lokacin suna tafiya wajen motar tasa jin furucin da sumayyah tayi na alamar kulawa a gareta.
Washagari ranar daurin aurece na Yah mu'azzam,wanda ya kama juma'a kenan.
Gidan su sumayyah a cike yake tam da baki,kasacewar yini daya za'ayi daga ranar taro yakare,dan a ranar ne za'ayi walimah shikenan shikenan.
Tun da asuba da sumayyah ta fito zuwa aiki bata samu lokaci ba,koh
Breakfast ma a tsaye tayishi.
Kowa idan ya shigo kallon mamaki yake yiwa sumayyah,ganin yanda ta zage tanata ayyuka.
Abubuwan walimar take ta sakawa a cikin take away itada su ladidi da su Muhibba wanda za'ayi .
Wani yarone ya zo akan ana kiranta a cikin gida,mamaki abin yabata waye yake kiranta.
Tana shiga ta samu salma da maryam sai kuma wacce idonta yake kanta a kafe.
"Ummu salma"
Shine abinda ta fada a hankali cikin mamakin ganinta,
"Kina mamakine da kika ganni,ai ni nayi mutunci tunda na nemeki,ke inaga ko sunana ma kin manta a rayuwarki,maryam ce muka hadu da ita a wajen dinner take fadamin kina gida ni nayi zaton ma bakya garin"
"Ina nan name sake din salma,kawai yanayin rayuwane,amma ykk ya su Dadah"
"Uhmm dadah tana nan kalau,ya hidimar biki,naga ai sai zirga zirga kikeyi"
"Wlh kuwa kinsan abinne sai a hankali"
Kunya ce ta kama sumayyah ganin yadda kowaccensu tasha kaya,musamman ma maryam da take sanye da dakykyakyiyar shadda mai zubin aiki har kasa,duk saitaji ta raina kanta a kusada su.
Tashi daya abin ya juya daga sama zuwa kasa,da lokacin da suke makaranta itace mai shigar kaya tana kallonsu wani iri,amma yanzu sunyi mata nisan da saidai tagansu daga nesa.
Maganar ummin ceh tadawo da ita daga tunanin data keyi inda taji tana cewa,
"Bikinfah muma namune,da yayan baffanu muke nida amaryar,kukan su maryam ai kungama karatunku,nidayake nasamu matsalar haihuwar saleem dina danayi har yanxu bandawo saiti ba,ajiye shakarar ma fah nayi,gakuma carry over suma sun sakani yin missing IT"
Dukkansu jaje suke mata tareda kwantar mata hankali,itadai sumayyah batace komai ba,dannta cakwakiyar tafi nata ma"
Salma ce takalli salman tareda cewa,
"Uhm summy kinyi shiru bakya cewa komai,ko wani abune yake damunki,da dai ba haka kike ba,gabadaya kin sanja"
"Lallai salma,wani idan yace na sanja aike mai bashi bayanin mai yasa ne,kawai dai kinsan sha'aninne sai hankali"
Dukkansu daga hakan basu kara cewa komai ba har lokacin cin abincin rana.
Da la'asar aka fara shirye shiryen tafiya walimah,lokaci yanayi sumayyah taga suna sanja kayan walimah,itadai nata idone dan cewa tayi bazata jeba.
Salma da Muhibba nesuka farayin gaba,aka bar maryam tana saka kaya,dan itace takarshen yin wanka.
Wayartace tayi ringing wacce take gefen sumayyah,kallon gaban wayar tayi inda aka rubuta "habeebee"
Daukar wayar tayi ta mikawa maryam tareda cewa,
"Maryam habeebee yana kiranki."
Karbar wayar tayi tana sunkuyar dakai kaman mai kunyar sumayyah,ganin hakan datayine yasata yin murmushi tareda cewa,
"Barina Baki waje"
"Lah dummy ki zauna,ya za'ayi keda dakinki kuma ki tafi ki barni"
Ahah karki dama inason debo kayan wankina"
"Ohk"
Daga haka sumayyah tafita daga dakin zuwa harabar gidan.
Lokacin data dawo da kayan wankin maryam har ta gama saka kayan tana shirin fita,
"Maryam kiyi sauri fah zasu tafi si barki,"
"Ahah Ahmad ne zaizo mutafi,amma sumayyah wai dagaske bazaki je ba kowa tafi saidai a barki kedai a gida?"
"Karki damu kedai ki tafi kawai,Ahmad din ma na Ganshi a falo ai suna magana da hajiyah mama,inaga kuwa ke yake jira,nidakika ganni kwanciya ma zanyi,dan nagaji sosai"
Daga haka maryam tafita a dakin sumayyan ba tareda tasake cewa komaiba,dan ta kula duk kokarinta sumayyah bazata sake da ita ba kaman a baya,abinda yafaru ya riga yafaru,koda anyi kokarin mantawa hakan bazai yiyu ba.

Gida yayi tsitt anyi biki an kare,yayinda amarya kuma na kaita tamfatstsen gidanta aljannar duniya,saida muyi fatan Allah ya basu zaman lafiya mai dorewa.
(Angama biki an more,duk da bakuji bayanin bikin yanda ya kamata ba,kowa da kowa musamman yah KAICO NAH fans muna muku barka da gajiyah,sananm mun gode da amsa gayyata Allah ya bar zumunci 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤❤)

Kwanci tashi akace asarar mai rai,akwan a tashi ta ishi mai hankali wa'azi.
Watannin iddar sumayyah ya kare,wanda kuma yayi dadai da wa'adin da abbah yafada mata na yin aure ko kuma barin gidansa.
Tun ana sauran sati daya ta gama iddah Bayan biki hankalinta yayi matukar tashi sosai,batada aiki sai tunanin wa zata kaiwa abbah a matsayin Wanda zata aurah,ita yanzu babu kowa a ranta,hasalima duk maza sun fita a ranta,ko da tayi magana dasune bare kuma zaman aure da daya daga cikinsu.
Ga kuma uwa ubah alkawarin datayi wa hajiya mama na cewar duk yanda zatayi to zatayi dan karta bar gidan iyayenta,to ya zatayine da wannan al'amari,gaba jeji baya tsiyaki,rana zafi inuwa kuna.
Tana cikin zirga zirganne kaman an tsikareta ta danna kiran salma.
"Hello salma kina gidane,dan Allah idan babu abinda kike ki taimakamim kizo,taimakone na gaggawa yazo,nayi niyyar zuwa amma banida kwarin gwiwar hakan"
"Ayyah sumayyah kiyi hakuri,dan wlh bana gari na tafi kauyen su ummah babanta bashida lafiya nake duboshi,gashi sai wani satin zan dawo,idan wani abune ki fadamin summy"
"Ahah babu komai ba har haka bane,saikin dawo kawai,allah yabashi lafiya"
Katse kiran tayi tana share gumin kanta,zancen gaskiya bai kamata ta takurawa salma ba,yakamata ta koyi jure matsalarta da gyarata kafin kowa.
A ranar da sumayyah ta cika iddarta koh abincin rana dana dare bata shaba,tana kan sallaya(dadduma)tana ta addu'a,wani abin ma bata san mai take fada ba.
"Yah Allah Kasa Kar abbah ya tuna da zancen damukayi dashi,Allah yasa kar yah tuno da zancen na fito da miji yah.........."
Tun kafin ta karisa Muhibba ta bankado kofar dakinnata tareda cewa,
"Anty sumayyah wai kizo inji abbah yana kiranki"
Wai tashin hankali dankari makari,shuru tayi ta dade bata tashi ba can kuma ta yunkura ta tashi tareda yin hanyar dakin abban.
Gab anta yana faduwa tana takawa har taje bakin kofar dakin.
Dauke numfashi tayi tareda tura kofar ta shiga,a ranta tana addu'ar da duk tazo cikin zuciyarta.
A zaune tasameshi yana karatu da jarida a hannunsa yasaka glass da kuma irin deam light dinnan.
"Abbah barka da dare,Muhibba tace kana nemana"
"Eh ina nemanki,tunda ke kinki ziwa shiyasa na nemoki da kaina,gameda bayanin mu na kwanakin baya,wane hukunci kika yanke,wanne wanda kika fitar zan daura miki aure dashi"
"Abbah dama dama....."
"Dama me?amsar ki nake bukatar ji"
Amsar data bashine yasashi jefar jaridar hannunsa yana kallon ta,anya kuwa ya jita dadai kuwa?..............

🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵
  

KAICO NAHOnde histórias criam vida. Descubra agora