Page .....9....

197 19 0
                                    

🏵 *(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*🏵


🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵🏵
..............*KAICO NAH*.............
Rubutawa.......sadi-sakhna.......

DEDICATED TO MY MOTHER & UNKNOWN OLD WRITER

Ga na dare,wanda basuyi bacci ba kawai😀😀😀

🏵🏵🏵
...9....

Kallonsa sumayyah take cikeda kosawar yafada mata abinda aka cemasa a waya,amma shiru baicemata komai ba har suka isa gida,parking din motar yayi tareda saurin fitowa ya je ta bangarenta,ganin yanda yake saurine yasakata yunkurawa ta fito daga motar itama.
A Falon ta Samu kujera ta zauna,har sannan batajin jikinta dadai kaman yanda ta saba,zama yayi a gefenta tareda fitowa da maganin da likita yace a bada,biyu ya balla maimakon guda daya ya mikamata a hannunta.
Karba tayi ta zuba a bakinta tareda karbar kofin ruwan dake hannunsa tabi maganin dashi.
Saida ya tabbatar tasha tukunna yarakata daki ta kwanta,har zai fita ta rike hannunsa da niyyar tambayar sa abinda yake faruwa,katseta yayi dason furta abinda yake bakinta.
"Kinga ki kwantar da hankalin ki ba wani abu bane sosai,Alhaji ne yayi hatsari a hanyarsa ta dawowa daga abuja jiya,yanzu haka yana asibiti shine Abdurrahim ya kirani,zanje na dubashi ne yanzu zan dawo,idan kinji wata matsala kisha maganinki dana ajiyemiki,sannan akwai abinci da muka dawo dashi ma"
Daga haka ya fita daga gidan ya barta a kwance.

Tun daga bakin asibitin mutum zai tabbatar lallai asibitine daya amsa Sunansa,shikansa wajen da'aka kwantar da alhajin kilacaccene,ba'a barin kowa ya shiga said iyalansa kadai.
A can gefen wajen yazeed ya ajiye motarsa tareda nufar wajen da kafarsa.
Kafin yakai ga isa wajen yaji an tareshi da bakin bindiga,kallon masu tsaron wajen yayi tareda cewa,
"Ya haka naga kun hanani shiga lafiya?"
"Eh lafiyarce ta kawo haka dan samari,daga cikin mutanen da hajiya ta bada umarnin su shiga babu kai a ciki,dan haka saika kirasu suzo ku shiga tare ko kuma ka koma inda ka fito kawai"
Juyawa yazeed yayi da baya yana cije lebe tareda yarfe hannu.
Hannu yasa a cikin aljihun wandonsa ya dauko wayarsa,dannawa Abdurrahim kira yayi domin shaida masa mai yake faruwa,daga daya bangaren ne yace,
"Am kayi hakuri abokina,wlh momy ce tayi haka,wai a cewarta babu wanda zai shiga wajensa harse ya farfado,amma karka damu idan yadawo hayyacinsa sai ka zo kawai"
Jijjiga kai kawai yazeed yayi alamar yaji,cikin bacin rai yq nufi motarsa ya tada ita ya bar wajen.
Gidansa ya koma inda yabar sumayyah gashi dama yasan bata da lafiya,badan yadamu da rashin lafiyarta ba saidan yaga shin cikin ya jube ko yana nan.
Bai sameta a faloba kai tsaye dakinta ya wuce,dan yadda yaga jikinta yasan fitarsa bayyi har ta fito falon ba.
Wayam dakin ya gani said karar nishinta a cikin bandaki,da sauri ya nufi wajen tareda bude bandakin.
A kwance yaganta a kasan tiles din gumi ya rufeta shirkif tana mayar da numfashi.
Kokarin daga yafara yi sai yaji tayi a yar kara tana rike cikinta,ana nanne ma yakula da jinin dayake bin kafarta,farincikine ya lullubeshi ganin sunyi nasara cikin ya zube.
Sharewa karar da take yayi tareda cire mata kayan jikinta daya bacin,ruwa ya hada mai dan yawa ya wanke mata jikinta tass.
Duk da halin da take ciki na ciwo amma a ranta tana mamakin yanda ya zage yana mata hidima.
Taimakon nasa bai tsaya iya bandakin ba dan suna fitowa daya zaunarta a kan gado ya fara kokarin hada mata tea mai kauri.
Cikin sauri sauri yahada tareda mika mata yana murmushi,karba tayi saikuma takasa kaiwa bakinta,kaman mai tunanin wani abu.
Tsugunnawa a gabanta yayi tareda tambayarta menene?
"Uhm ina tsoron kar na sha shima na amar dashine kaman na jiya"
"Ahah babu abinda zai miki,dama yanayin cikine toh yanzu babu shi ai,dan haka babu aman dazakiyi dankin sha"
"Ciki kuma yaushe ne cikin ya zauna a jikina?"
'Jiya yana nan amma yau baya nan ya fita"
"Taya zai fita haka kawai kaman wata hanya ya shiga ya fita"
"Nine na taimaka masa ya fita ta kwayar dana baki dazu,dakuma drip din da likita yasaka miki kina bacci,kinga na taimakeki babu ruwanki da wata wahala sai mu cigaba da zaman ..............."
Shiru yayi tareda saurin ja da baya jin radadin daya jiyarci fatar fuskarshi,shafa wajen yayi da sauri yana kallon empty din cup din cake hannunta,what? Tea din dayake hannunta mai zafi ta zuje masa a fuskar dayafi so a duk jikinsa.
Hakan bai mata ba ta kara da jefah masa kofin shima a fuskarsa,dafe hancinsa yayi inda kofin ya daga,cikim kankanin lokaci jini yafara zuba a hancinsa kaman dama neman hanya yake.
Nuna shi take da hannunta wanda yake rawa,dan takasa furta ko kalma daya ma da bakinta.
Ganin hakanne yasashi tashi da sauri ya bar dakin,dan tunda ya hadu da ita bai taba ganin bacin ranta ba irin na wannan ranar.
Tashi tayi ta saka doguwar riga a jikinta tareda daukar mayafin rigar,hanyar waje ta nufah ta wuce shi a falo ko kallonsa batayi ba.
Mai napep ta tsare tayi masa kwatancen anguwar dazai kaita,suna cikin tafiya tana kuka har suka isa kofar gidan.
Dari biyar din data dakko a kudin yazeed din ta bashi ko tambayar canji bata tsaya yiba.
Sallama tayi a hankali tashiga gidan.
Nafeesa ce datake shara tayi saurim zefar da tsintsiyar tana karewa sumayyah kallo,dan idan wani ne ya ce mata yaga sumayyah a haka to Zata Iya yin tsalle ta musa zancen.
Amma wai itace taga sumayyah a wannan halin,auren da koh shekara bayyiba(ke duniya)
Har tayi niyyar isa inda take saikuma ta tsaya tana kame kame,itama sumayyah lura da hakan datayi ne yasata tsyawa a inda take,dan maganar da abbansu yafada na ranar aurenta ne yadawo mata cikin dodon kunnenta.
"Sumayyah kiyi hakuri,wlh kekanki kinsan bazan so ganinki cikin haka naki taimaka miki ba,saidai dan ba yadda zanyi......."
"Ahah karki ce komai Anty Nafee ninasan abinda zaki iya min,ki daina da damuwa da abinda laifina ne ba laifinki ba,ba taimako nazo nemaba kawai nazo na fadawa wani halin danake cikine koda kuwa bazai sauraraba,sannan kuma inaso nafadamiki sako wamda nake so kitaimak yaje kunnen abbah:
Ina so ki fada masa cewa nagode matuka da soyayyar daya nunamin,na rainata da yayi bai kasheni ba tun ina ciki,ya bani karatu da tarbiyya har na kai na mallaki hankalina.
Saidai babu abinda na saka masa dashi sai abin Allah wadai da tirr a rayuwata.
Hakika anty nafee ina cikin kunci ,wai mijin dana aura shine ya zubarmin da cikin jikina batareda sanina ba,wai mijina shine yake karban hakkin aurensa a cikin bacci batareda sanina ba kaman baiwa.
Kuma duk da hakan nasan banga komai ba,dan nasa iyayena zubar da hawaye yafi a kirga,dan haka dole nima na zubar da nawa hawayen.
Kice musu na gode da kukawarsu anty nafee,sannan kice sukara mantawa dani kar bakincikina yasa nazawo muku ku rasasu"
Haka ta juya tana rusa kuka tabar gidan,itama anty nafee a nata bangaren kukan take rusawa kaman amyi mutuwa hadda kwanciya a kasa.
Lokacin data koma gidan babu kowa a gidan da alama ya fita.
Maganin daya bata lokacin dasuka dawo daga asibiti tagani a kan kujera,dauka tayi tana dubawa inda daga ansaka a sha guda daya,idan yayi yawa yana iya yiwa mace illah.
Zare ido tayi tareda sake rushewa da wani kukan data tuna yanda yazeed ya bata kuda bibbiyu tana sha.
Motsinsa taji a bayanta yashigo gidan kaman mai sanda,juyawa tayi tareda nuna masa maganin dadai wajen inda aka ja guda daya da biro.
Sunkuyar dakai yayi yana mutstsuka yatsun hannunsa,
"Yanzu kiyayyar dakake min yazeed har ta kai haka,ina zaune dakai ashe kasheni kake sonyi bansani ba?"
"Ba haka bane baby,kawai inason cikin ya zubene,saboda banason mufara haihuwa yanzu ,kigane mana baby wlh ina sonki sosai"
"Rufemin Baki banason sakejin wannan kalamannaka masu cike da dafi haka"
Dakinta ta shige ta rufo tareda saka key,dan a yanda takeji ko kallonsa bata sonyi.
Shima dayaga hakan komawa yayi yasake ficewa daga gidan,dan yasan ko giyar wake yasha bai isa tankwasa ta a lokacinba,amma yasan soon zata sakko tunda tana sonsa.
Gaban mirror ta taje ta baje su a kasa tasak ihu,amma hakan ma bai saka ta taji zogin dayake cikin zuciyarta yana alamar fita ba.
Zubewa tayi akan gadonta tana maida numfashi,hannunta ta dora akan cikinta wai dan ta ne yakwanta a wajen amma yazeed yasaka magani da karfin gaske ya fito dashi daga cikin cikinta,wannan wace irin rayuwace haka tasaka kanta a ciki.
Daga haka tana cikin tunanin har bacci barawo ya saceta bata sani ba.
Tunda la'asar sakaliya datayi bacci ba ita ta tashi ba sai wajen karfe hudu na dare,zabura tayi tareda kallon window,jin yadda garin yayi tsitt.
Share tantamarta tayi ganin garin bakikkirin babu alamar haske ta window n.
Saurin nufar bandaki tayi data tuna da ko magriba batayi ba bare isha,gashi ana shirin kiran asuba.
Da farko fara duba jikinta tayi domin taga shin jinin da take zubarwa yana nan ko kuma ya tafi.
Hamdala tayi a ranta ganin babu wata matsala sosai kaman yanda take ta tunani,batasani ba ko nan gaba kuma.
Gyara jikinta tayi ta dauro alwala domin komawa ga mai duka,dan tasan a yanzu batada wani gatan daya wiceshi a cikin wannan halin da take ciki.
Bayan tagama idarwa da sallolin da ake binta saikuma tafara dayin nafilifili,ganin lokacin sallah har yanzu baiyiba da saura tukunna.

(To su sumayyah ba anga ba sarki sai Allah an koma gamai duka.
Allah yakawo mana dauki a cikin rayuwarmu dakuma ayyukanmu.
Allah yakara dada karemu dakuma bamu jarabawa wacce bazata fi karfimmu ba,mata wanda suke cikin kunci a gidan mazajensu Allah yakawo musu dauki yagyara zantakewarsu.
Wanda sule cikin wadata da kuma kwanciyar hankali Allah ya dawwar dasu a ciki,yakara hada kansu dakuma basu zuri'ah dayyab.
Muda bamuyi aure ba yan mata Allah ya azurtamu da mazaje nagari wanda zasu ji kanmu su kuma faranta mana daidai iyawarsu.
Mukuma matan Allah kasa mukasance mata na gari ta yanda zamuyi dadai da addu'ar miji na garin.

Allahumma yassir wala ta assir.
Lahaula wala kuwwata illah bika ya arhamarrahimin.🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼.





🏵 *sadi-sakhna ceh* 🏵

KAICO NAHWhere stories live. Discover now