Tai maganar hawaye wani na bin wani, tai ficewarta da ga ɗakin, ta tafi ɗakinta ta faɗa akan katifa ta sake fashewa da kuka.

Imran kuwa kasa motsi yai, Lallai an Cutar da Amira da kalma me munin gaske, amma koma da maraici wani abun ita ta janyowa kanta, dan babu yadda Za'ayi mutum yana aikata abunda takeyi ace ba Iskanci take ba, ga raye raye, ga shigar banza da gantali ga tsantsan fitsara da rashin kunya, ba wanda ze yadda ba karuwa ba ce.

Haka Imran yaje yai wanka, duk jikin sa a saluɓe, ya gyara gadon ya nemi guri ya kwanta, tunani duk ya cika masa zuciya tare da matsanancin tausayin Amira.

Da gari ya waye, da kansa yai gyare-gyaren gidan nan gaba ɗaya, ya dafa tea da yake ba wani iya girki yai ba yavfita ya siyo bredi.

Sedai har ƙarfe goma Amira ba ta fito ba, wanda ƙa'idar ta bata wuce ƙarfe takwas duk baccin da za tai, ɗakinta ya nufa ya shiga da sallama, ya hangota kwance akan katifar dake ɗakin a cikin bargo.

Ya ƙarasa ya ɗan janye bargon, ya daddaki filon da ta ke kai yace "Amira ki tashi ki karya, rana ta fara yi, idan yaso in kin karya se muje ko Asibiti ne"

Ƙare masa kallo tayi tace 'meye naka a ciki, da in karya ko kar in karya? Ina ruwanka dani Karuwa ka ƙyaleni mana"

"Naji amma kiyi haƙuri ki tashi, se muje ko Asibitin Barrack ne a duba ki"

"Muje Asibiti kace musu me, You rape your wife because you thought she's not virgin? Haka zaka gaya musu? To ni ba haka nake ba, ko da nake karuwa na san daidai, ba zan taɓa fallasa Asirin Aurena ba"

Imran yace "Amira rape kuma?"

Cikin hawaye tace "akwai maraba da rape da abunda kaimin jiya ne? Babu maraba ai, kuma ka dena wani pretending kana lallaɓani, dan ka samu wani abu daga gareni, seka sakeni daga Garin nan Kano zan koma na gama Aurenka"

Haɗe rai yai yace "dan kinga ina lallaɓaki shine zaki dinga gayamin Magana?"

Tashi zaune tayi tace "An gaya maka ɗin, na faɗa kaji haushi ka rabu dani"

"Naji, amma muje ki karya"

"Ba zanci ba"

Tai maganar tana Share hawaye, Ƙarshe Imran se tashi yai ya bar mata ɗakin, abun duniya ya ishi Imran, tabbas anwa Amira ba daidai ba, mussaman yadda ya dinga dizgaya da kalamai marasa daɗi.

Wunin ranar haka dinga koke koke, kuna taƙi saurarar Imran.

Imran yana ɗakinsa ya kira Khalid a waya.

"Kai lafiya kake kirana a daren nan? Ya kake ya Lagos?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, Amma fa akwai matsala ina cikin damuwa"

"Sarkin matsala, meke faruwa Kuma?"

"Khalid, Amira ce, naiwa Yarinyar nan ba daidai ba, Amira ba Karuwa bace, abun ya bani mamaki, how could this be possible, and worse part of it is that, ta dage wai sena saketa ta koma Kano, ni wannan be dameni ba, ina jin kunya akan abunda nai mata"

Khalid yace "kaga abunda na dinga gaya naka kenan a baya, amma kai kunnen uwar shegu dani Imran, na gaya maka ka sassauta ƙiyayya akan Yarinyar nan, duk da dama can kan son ta, son zuciya ne ya rufe maka ido, kawai seka haƙura ku rabu tunda haka take so, da ka cigaba da gallaza mata"

"Wane irin in saketa kuma? Kaifa ka fiye abun haushi wallahi, wane irin in saketa?"

"To in baka saketa ba me zaka mata? Ace ka Auri yarinya over 4_5 month, amma baka taɓa sauke hakkinta na Aure ba, da lafiyar ka da Komai ka tare a gurin mace ɗaya, gaskiya ba kayi adalci ba, kuma wallahi na goyi bayan ka sawwaƙe mata, tunda ba ka da adalci"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now