37_38

570 14 0
                                    

Sake fashewa da kuka Amira tayi tace "ni dai ba na son ka tafi"

Ɗan shiru yai yana kallonta "meyasa ba kya so na tafi?"

"An kashe mutane, kuma bana so a kashe ka"

Jikin Imran yai sanyi sosai, ya kalli yadda ta riƙe hannunsa, ga idanunta na zubda hawaye.

Gyara tsayuwarsa yai, ya ɗago fuskarta, ta na kallonsa, fuskarta duk cizon sauro ga idanunta sunyi jawur"

A hankali yace "kin kwana a falo sauro ya cije ki, kinga zazzaɓi ya rufeki, kije ki kwanta zuwa anjima ki kira Anty a waya, a kawo miki magani, zan tafi abokan tafiya ta suna jirana, dan Allah ban da faɗa ko tashin hankali, ni na tafi"

Ya zame hannunsa a hankali, ya juya ya fara tafiya, bayansa ta bi da kallo, har ya fita daga falon.

Jiki a sanyaye ta koma ta Kitchen, ta leƙa window, ta ga sojoji a harabar gidan jikinsu da Uniform, suka hau mota suka fita.

Amira ta zauna a Kitchen ɗin ta haɗa kai da gwiwa tana maimaita 'Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

Sun yi nisa a tafiyar, Imran ya kira Anty, tana tsaka da aiki ta ga kiran nasa, amma tai ƙoƙari ta ɗaga wayar "Anty barka da safiya"

"Yawwa barka Imran, ya kake ya gida?"

"Lafiya ƙalau, ya aiki?"

"Aiki Alhamdilillah, mun fito tun ɗazu"

"Masha Allah, dama Anty nace dan Allah idan ban takura ki ba, kinga an turani aiki Zamfara ne, kuma na bar Amira ba lafiya, ban san lokacin da zan dawo ba, nace in ba damuwa ko zata zauna a gurinki, kan inga yadda Allah zeyi damu, tunda babu me kula da ita a gidan"

Anty tace "Ni da 'yata amma ka dinga cewa in ba zaka takuramin ba, ai gara da ka gayamin inje in ɗakko abata, yanzu Zamafaran aka turaku Imran?"

"Wallahi kuwa Anty, kin ganmu a hanya ma"

"Subhanallah, to Ubangiji Allah ya tsare mana ku, ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, Amirana kuma Allah yasa rabo muka samu"

Imran yace "Rabon me kuma Anty?'

"Rabon Baby mana, zan ɗau jika"

"Hmmm Anty kenan, ai mana addu'a dawowa lafiya"

"Insha Allah zamuyi, Allah ya tsare"

"Ameen Anty nagode"

Ya katse wayar.

Duk da yasan Ammi tana jin haushin sa amma ya kirata a waya, suka gaisa ta amsa masa sama sama, yace "Ammi ina buƙatar addu'rki, ina hanyar Zamfara ne"

Ba shiri ta ware murya tace "wace irin Zamfara kuma?"

"An turamu aiki ne, na so in biyo muyi Sallama, amma kiran na gaggawa ne, kuma abokan tafiya ta suka zo, shiyasa kawai na taho"

Ammi tace "Innalillahi wa innalillahi raji'un, To Imran Allah ya tsare mana ku, ya kiyaye ku, Allah ya dafa muku ya shiga lamarinku, Allah ya dawo mana daku lafiya" tana maganar se hawaye.

"Ammina ki kwantar da hankalinki, ba abinda ze faru insha Allah"

"Ai hankalina ba ze kwanta ba, se Allah ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare"

"Ameen Ammi nagode"

Ta ajiye wayar jikinta a sanyaye, Minal ta shigo ɗakin Ammi ta ganta wani iri, tace "Ammi meya sameki naga kamar kinyi kuka?"

"Bari kawai, Imran ya tafi Zamfara yanzu mu kai waya da shi"

"Zamfara kuma Ammi?"

"Eh Wai Zamfara, suna hanya ma"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now