WUTA A MASAƘA 27_28

739 50 5
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.







27_28

Imran kam seda ya ƙarewa wayar kallo, tare da jinjina kalmar Yayana da Amira ta kirashi da shi, yasan wani sabon iyayin ne yasa ta faɗi haka, wani gajeren tsaki yaja, ya ajiye wayar ya cigaba da aikinsa.

Amira kam tunda ta shige ɗakin nan bata sake fitowa ba, ta zauna ta dinga saƙawa tana warwarewa, tana tunanin irin zaman da za tai a gidan Imran, daga Imran har matarsa da danginsa babu me ƙaunarta.

Imran kam ya samu nutsuwa sosai, hankalinsa a kwance yake sosai, cin amarcinsu kawai suke da Ihsan.

Yana kwance yana kallo, Ihsan ta fito tana yamutsa fuska, ya kalleta yace "My beb, ya dai naga kina ɓata rai?"

Ƙarasowa tayi ta kwanta a jikinsa tace "yau bana jin daɗin jikina gaba ɗaya"

Murmushi yai ya shafa dogon gashinta yace "kodai kodai?"

Ihsan tace "kodai me?"

"Ko an gamune, kin sama mana Baby?"

Gaban Ihsan ne ya faɗi, a ranta tace ji wata Magana, daga yin Auren se maganar ciki.

"Ya naji kinyi shiru ne?"

"My, daga yin Aurenmu se ciki kuma, ko gama cin amarcin banba se ciki, kasan fa ciki yana bawa mata wahala sosai"

"To meye a ciki Ihsan? Ai Arziki ne da yawa suna nan suna nema basu samu ba, ina fatan Allah yasa ciki ne, ko biyu ki haifamin sekiyi planing ki huta"

"My D Service ɗina fa?"

"Bakomai, Allah baze hana mu yadda zamuyi ba, Allah ya bamu masu albarka"

Yai maganar yana kissing goshinta, murmushi kawai tayi ta rungumeshi sosai ta lula duniyar tunani.

Amira ta kai kwana biyu kafin ta sake sakin ranta, dan duk batun Imran ta dameta, Anty kuma tana ankare da ita, ta tausaya Amira matuƙa, ta fuskanci Amira nada kishin gaske sedai kuma ta iya siyasa sosai da sosai.

Amira tana cin Abincin Safe tana ta cakala, ba wani ci take sosai ba, Anty tace "Amira, anjima ki shirya zamuje kasuwar, idan yaso gyaran kan gobe in Allah ya kaimu se Fadila ta rakaki"

Amira tace "to Anty, bari in gama se in fara shiri" ta kammala cin Abincin, amma maimakon ta tashi seta ɗakko wayarta ta kira layin Yadikko, amma bata tafiya, seta kira ta Usman.

Seda ta kusa katsewa sannan ya ɗaga yai Sallama.

"Yaya Usaman manyan gari, ko nemana ma ba'ayi ko, wato Allah ya rabaku dani babu me neman inda nake, bakomai rayuwa ce"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now