WUTA A MASAƘA 17_18

738 55 4
                                    

🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

WUTA A MASAƘA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

The experience writer of

*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA)
*BAƘIN TABO (Labarin gasa)
*AƘIDATA (Paid Book)
* WUTA A MASAƘA

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

❌❌❌
Ƙirƙirarren labari ne, ban yadda ayi amfani da kowane sashi na labarin ba ba tare da izinina ba.

KAMAR YADDA NA FAƊA TUNDA FARI, BA LALLAI IN DINGA SAMUN YIN POSTING KULLUM BA, IDAN AN GA BAN POSTING BA AMIN HAƘURI




17_18


Imran ya kalleta a fusace yace "nan yai miki kama da gidan karuwai ne?" Murguɗa masa baki tayi ta ɗauke kai.

Khalid yace "Amira gidansu Imran ne fa, ki shiga bakomai, baki ga 'yan biki suna shiga suna fita ba"

Ta ƙarewa gidan kallo, sannan ta kalli Imran tace "muje"

Idan Imran ya biyewa Amira, ze iya yi mata dukan tsiya a gurin nan, kawai ya wuce yai gaba, Amira tabi bayansa.

Mata nata tsokanarsa suna ango ka sha ƙanshi.

Cikin gidan suka shiga, ya wuce Falo Amira na biye da shi.

Minal suna zazzaune a falo da ƙawayenta, da babbar Yayarsu Khadija wadda daga Ita se Imran, ita tayi Aure tuntuni.

Khadija ce ta fara ganin Imran da Amira, ta kallesu tai murmushi tace "Imran kai da wa nake ganinka haka kamar Amira?"

Amira dai tayi turus, tana kallon Anty Hadiza.

Jin ance Amira yasa Minal waigowa, duk yadda ake faɗar rashin jin Amira da yadda ta ganta a hoto, ba ta zaci zata ganta a haka a fili ba, tafi kyau da class Sosai a fili.

Imran yace "eh ita ce"

Hadiza tace "masha Allah, Nikam yaushe rabon da inga Amira tun tana ƙarama sosai, yanzu waze ce ita ce, ta zama hamshaƙiyar mace"

Wata a ƙawayen Minal tace "wannan ba ita ce wani mawaƙi yace zata fito a vidon waƙarsa ba?".

Minal ta kwaɓe baki tace "ita ce"

"Wow Gaskiya naji daɗi dana ganta, ashe 'yar uwakku ce, wallahi ni burgeni tayi"

Cikin isa Imran yace "ke minal, ki bar abun da kike kije ki kaita ɗakinki, ki nuna mata toilet tayi salla, Sannan ki bata babban hijjabi"

Amira kuwa kamewa tayi a gefe, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya.

Minal ta zumɓura baki, cikin ƙunƙuni tace "ɗakina, toilet ɗina, kuma kayana, taɓɗijan Allah ya kiyaye inyi sharing da wata"

Cikin muryarsa me razanarwa wasu lokutan yai mata tsawa "dan ubanki me kike cewa? Ni nake miki Magana kike min ƙunƙuni?"

A hargitse Minal tace "A'a Yaya, dan Allah kayi haƙuri, wallahi ba da kai nake ba"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now