Ta jinjina kai, can ya ture kayan Abincin yace "ya ƙoshi"

Amira ta kwashe kayan Abincin, ta kai Kitchen, taje bedroom ta ɗakko masa bargo da fulo, ta fito tace "ga fulo ka kwanta kafin ta dawo daga gurin aikin"

Imran ya karɓa ya kwanta tare da lumshe idonsa.

Har ta miƙe zata tafi yace "Amira"

Seda tsigar jikinta ta tashi, ta waigo tace "Na'am"

"Ya jiki?"

"Naji sauƙi ai"

Ɗan ƙura mata ido yai, dan sabon salo ta saka uban hijjabi taƙi cirewa, amma duk da haka kana iya gane ta rame sosai, kamar wanda a kaiwa dole yace "Meya sameki ne?"

"Bakomai, kawai rashin lafiya ne" ta bashi amsa, Yai ajiyar zuciya be kuma cewa komai ba.

Ta koma ɗakinta, tana cigaba da hamdala, kasancewar Imran yana raye.

Anty kuwa tana ganin Alhaji Hashim shikaɗai tace "yaya, ina Amiran lafiya dai ko?"

"Lafiya ƙalau, Mun ɗakko Imran, ya dawo lafiya ƙalau"

"To ina Amiran"?

"Na baro ta a gidan mijinta"

Anty tace "Daddy why? Ya za'ai ka bar musu ita?"

"To Anty ya kike so ayi?"

"Gaskiya ban niyyar ba da Amira Yanzu ba, sena san meye matsayinta a gurin Imran"

"A'a matarsa mana"

"A'a fa Daddy, nifa ban gane kan wannan abun da kayi ba, nan na zauna na baka labarin irin abunda ke faruwa kuma seka bar masa ita"

"Calm down Madam, yarinya ba ta da lafiya, ita ta fara hango mijinta taje ta taro abunta tana murna, ga sirikanta kawai se in taho da ita, haba Antyn Yara"

"Gaskiya ni dai banji daɗin abunda kai ba Daddy"

"To Allah ya baki haƙuri, amma gara da na barota a can, dan Yarinya na kewar mijinta, ai tsakanin miji da mata se Allah, ki ƙyale sha'anin yaran nan kawai"

"A'a dole in dinga saka ido, saboda baza'a mayarmin da 'ya bora ba"

"Koma dai menene, kiyi haƙuri"

Anty tace "ba wani inyi haƙuri, ka yi min laifi kawai"

"Naji kuma ai na bada haƙuri, ai nima 'ya ta ce" yai maganar yana murmushi.

Ammi kuwa bayan sun koma gida, ta samu Abba a part ɗinsa, ya kalleta yace "ya dai sarkin ƙorafi?"

"Magana nazo muyi"

"Maganar me ne?"

"Wai dagaske kake da Yarinyar nan ze tafi Lagos?"

"Eh dagaske nake"

"Amma saboda me?"

Abba yace "ban gane saboda me ba, Saboda matarsa ce, wancan lokacin ya tafi da Ihsan, wannan karon ya tafi da Amira"

"Amma....

Abba yace "bana son Amma nan dan Allah, na gama Magana wannan karon da ita ze tafi"

Ammi ta harzuƙa, amma ta dake tace "naji da ita ze tafi, amma ina son kayi tunani a raba musu gida, dan gaskiya Yarinyar nan ba ta da cikakken tunani, kan Imran yai tafiyar nan ta kama Ihsan ta daketa, harta fitar mata da jini"

Abba ya kalleta yace "ban gane ta daketa ta fitar mata da jini ba?"

"Ai shine bayanin da nake maka, shiyasa ni tun farko da kai shawara dani ba zaka yanke Wannan hukuncin ba, yana zaman zamansa yana da wadda yake so ka ƙaƙaba masa Auren Wannan yarinyar mara kunya mara ta ido, gaskiya a raba musu gida, kar ta yiwa 'yar mutane lahani"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now