"Mun shiga uku Ammi, kashe sojoji ake sosai a gurin faɗan nan fa"

"Hmm, Nifa tuntuni bana son aikin sojan nan, Babanku ya goyi bayansa yaje ya nema masa, mutum yayi masters meye na wani aikin soja maimakon ya nemi aiki, duk wani abun tsiya babanku ke gayyato masa shi, ko taya shi aikatawa"

"To Ammi yanzu haka ya tafi ya barsu a gida ɗaya, Anty Ihsan da wannan 'yar damben"

Ammi tace "aikuwa, taɓ aikam baze yuwu ba, taje taiwa 'yar mutane lahani a banza"

"Wallahi kuwa dan kin san zata aikata"

"Aikuwa ta taɓa ta se ta bar gidan nan, bari kawai mayi Magana da Maman Ihsan ɗin ta koma gida kawai, ta bar mata gidan kafin ya dawo"

"Aikuwa dai da yafi, ni dama anjima zanje gurin Mummyn".

"Shikenan, bari inje gurin babanku inji meze ce, bana son inyi abu ya zo yanamin sababi, na ga kwanan nan tun da ya aurawa Imran Yarinyar nan yabi ya canza, amma canzawarsa ba ze canza ƙudurina akan Auren nan ba"

Minal tace "nima dai na gani Ammi, bari inje in fara shiryawa"

Anty se la'asar ta tashi daga gurin aiki, kai tsaye gidan Amira ta wuce, dan ta duba jikinta kamar yadda Imran ya buƙata.

Da sallama ta shiga falon, amma shiru ba'a amsa ba, ga mamakinta Ihsan na falon a kwance tana kaɗa ƙafa.

Anty tace "Barka da gida, ina sallama amma baki amsa ba"

Ɗagowa Ihsan tayi ta kalli Anty, ta ɗan yatsina fuska tace "banji bane"

"Allah sarki, ya gidan fatan kuna lafiya"?

"Lafiya ƙalau" Ihsan ta amsa da mata da ƙyar.

Anty tace "Nace Amira tana nan ne?"

"Bani da tabbas, tunda ba'a kaina take zaune ba"

Mamaki ne ya cika Anty, tace "to Allah ya baki haƙuri"

Ta wuce ɓangaren Amira, ta shiga da Sallama amma shiru ba kowa a falo, kiran sunan Amira tai, amma taji shiru, ta ciro wayarta ta kira Lambar Amira, amma bata ɗaga ba.

Kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Amira, tai Sallama sannan ta shiga, A duƙunƙune ta hango Amira akan gado, tana ta rawar sanyi ga sautin kukanta da yake tashi ƙasa ƙasa.

Da sauri ta ƙarasa bakin gadon tana kiran sunan Amira, Amira da ƙyar ta iya ɗaga idonta ta kalli Anty.

"Amira lafiya meya sameki haka?"

Tai maganar tana yaye bargon jikin Amira, Amira dai kasa magana tayi se kuka, Anty tace "yi shiru ya isa kukan, bari in haɗa miki ruwa kiyi wanka, kin ci Abinci makuwa?"

Amira ta girgiza kai.

Anty ta jona ruwa a heater, ta haɗawa Amira ruwa, ta rakata banɗaki, ta dawo ta gyara mata gado ta canza mata bedsheet.

Tayi mamakin yadda Amira ke Rashin lafiya har jikinta ya zama haka, kuma bata gaya mata ba, Amira ta rame sosai idanunta .

Ta shiga Kitchen ɗin Amira, amma babu kayan Abinci a ciki, ta dawo ɗakin ta tarar Amira ta fito daga wankan.

Ta kalli Amira tace "na duba Kitchen ɗinki, Banga komai na Abinci ba, se ɗan abunda ba'a rasa ba"

Cikin muryar marasa lafiya tace "suna Kitchen ɗin falo"

"Amma Amira ya akai kika bari jikinki yai haka bakije Asibiti ba, kuma baki gayamin ba? Ko dai ciki ne?"

Amira ta girgiza mata kai alamar A'a.

Anty tace "wani irin A'a, in ba ciki ba to wani rashin lafiya ne ze maida ke haka lokaci ɗaya duk kin rame, kamar bake ba, yanzun me kike son ki ci?"

"Bakomai"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now