"Ihsan, bana son duk wani dalili da ze ɗagamin hankali, ƙarewa Abincin nawa ma ita na barwa take ci, na ƙyaleta bana son abunda ze disturbing peace ɗina, kiyi haƙuri"

Kamar Ihsan za tayi kuka tace "Yanzu in dafa maka Abinci dan cin fuska ka bata ta cinye"

"No Baby, ni na isa inci fuskarki saboda ita, ina cikin mood na soyayya ne, ba na son ta ɓata mana shiri, ko tai sanadiyyar da zamu samu rashin jituwa, muje Kitchen ɗin in dafa miki wani abun da kaina in baki"

Ihsan ba ta son ya hasala, dan shi idan yai rarrashi ɗaya biyu baya na uku, tsaf ze ɓata rai ya fita harkarta, dan haka ta haƙura ta haɗa sauran Abincin suka koma falonta suka ci.

Wajen ƙarfe sha ɗaya da rabi, Suna falon Ihsan suna shan soyaya, aka ƙwanƙwasa ƙofar falon.

Imran yace "shigo"

Amira ce ta shigo, da kwanukan da tai breakfast ta wanke su tsaf, se wasu manyan plate da ta zuba snacks ta saka poil paper tai wrapping ɗin su.

Ihsan na jikin Imran yana wasa da gashin kanta, amma ganin Amira ya sa ta miƙe zaune, tana bankawa Amira uwar harara.

Amira kam murmushi ta saki ta ƙaraso inda suke, tace "Ihsan ga kwanukan ki, na wanke miki nagode Sosai, ta ajiye kwanukan a gaban su, sannan ta ɗau plate ɗaya ta ajiyewa Imran, tace
"Captain ga naka, Ihsan kema ga naki"

Ihsan tace "Me zanyi da wannan abun? Dalla ɗauke ki fita da shi ko mun ce miki muna jin yunwa ne?"

Amira tace "Haba Ihsan, meye na wani Maganar kalar yunwa a nan, ai kyauta ce ba wani abu ba fa"

"Eh na faɗa mu ba kalar yunwa bane, ba ma so ɗau abunki ki ƙara gaba, idan ma wani abun ki ka sa a ciki dan ki mallake shi to wallahi kinyi ƙarya, munfi ƙarfinki wallahi, sedai ki kalleshi daga nesa, dan ba kalarki bane"

Amira tai murmushi tace "naji shi mijin namu ba kalar yunwa bane, amma kefa, dan Allah idan ana Maganar yunwa ko makamancin yunwa, ki dena saka baki, dan ba ki da maraba da kalar yunwar"

"Amira!"

Imran ya kira sunanta da ƙarfi, "Matar tawa kike gayawa haka?"

"Bakaji ni me tace min bane, har tana wani Maganar zan zuba wani abu in mallake ka, ai idan har zanbi malamai dan mallakar miji ban kai karuwa ba, mu zuba mu gani ni da ke, na ɗaga miki ƙafa ne saboda be kamata daga zuwana ace mun fara samun saɓani ba, amma am ready for you"

Amira ta miƙe ta tafi, Imran ya dafe kai yace "Ihsan why? Na gaya miki duk yadda zaki kija girmanki kar yarinyar nan ta rainaki, amma kin kasa hakan, da ta kawo abu kika san ba kya so se ki karɓa ki bayar, amma abun da kike ze sa ta rainki, ni kuma bana son hakan, kuma ba zan iya haushi ba yau ba gobe ba, saboda gidana ba ba gurin aiki bane, ko filin daga da zan ta ɗaga maƙogwarona ba, shiyasa tun farko nake fargabar zama da mata biyu matsalolinku ba sa ƙarewa"

Ya miƙe ze fita saboda ransa ya gama ɓaci, Amma Ihsan ta riƙeshi ta marairaice fuska tace "am sorry dear, ba zan sake ba insha Allah"

Da ƙyar ta lallaɓashi ya haƙura, dan Imran akwai zuciya.

Amira kam tun da ta koma ɗaki, ranta yake a ɓace, bata sake fitowa ba har magariba, saboda yadda zuciyarta ke ƙuna, tun Abincin safen nan bata sake cin komai ba.

Bayan ta idar da sallalr magariba ne, sega kiran Anty ya shigo wayarta, cikin murna ta ɗaga tace "Antyna"

"Na'am, Amira na ya kike?"

"Lafiya ƙalau Amarya, au uwargida ya kike ya Gidan, ina fatan ba wata matsala?"

"Ba matsalar komai Anty, ya Anty Fadila"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now