02|Divorce

63 3 0
                                    


CAPTAIN RIDWAN

Meesty✍️

02|Divorce

بسم الله الرحمن الرحيم

The next day aka tashi da mutuwan Malam.Zuwa 11am,an mishi wanka aka wuce dashi Gwallaga Jumu'at mosque.Anan akayi sallah kafin aka kaishi maqabarta.Yayi jama'a sosai,saboda shi na kowa ne.

Haka su Bahijja suka tattara suka dawo gidansu Abdul zaman makoki.Ahaka har akayi kwana bakwai.A kwana bakwai dinnan kuwa kullum sai Yasmin ta nema ta da fada amma ita bata kulata saboda gidan mutuwa ne.

Acikin friends inta Sady,wata course mate inta kuma bunkynta ne kawai tazo mata ta'aziyyah.

From that day onwards kuma ta koma hostel in ta,saboda yafi kusa da inda take IT in ta.Ba ita ta sake komawa gidan Abdul ba,sai ranan da Zaynab ta Kira ta wai Mama tace ta dawo gida saboda za'a shiga satin bikin Abdul.

Shiryawa kawai tayi ta tafi batare da ta dauki kaya bah,saboda dama tayi niyyah idan ta koma zata tattaro sauran kayanta.

Tana isa ta samu ba kowa agidan,saboda haka ta jira abakin gate.Sai after like 2 hours Abdul ya dawo ya bude mata.

Shiga tayi batareda ta mishi magana bah,shima bai ce mata komai bah.Itadai wannan qaddararren aure ya isheta kuma tasha alwashin cewa bayan bikin nan sai tace ya sake ta.

Arayuwanta itadai abu daya takeso,ta auri romantic man wanda zae sota kuma bazaiyi shakkan nuna hakan wa kowa bah.

Haka nan dai ta kwashe sauran belongings inta tasaka awani trolleynta,wanda aciki dama Uncle inta yayi mata tsaraba lokacin da yaje Dubai.Hayaniya taji,amma sanin bai wuce Zaynab da Yasmin bane yasa ta share.

Zaynab ne tazo sanarda ita Abdul na kiranta.Hakuri ya bata tareda bata takardan saki wai Yasmin tayi rantsuwan bazata auri mai mata bah.Wani sanyi taji a zuciyanta kafin taje ta jawo trolleynta.Fita tai tana murmushi,tana kuma ji Zaynab nacewa Allah tura keya.

Tana fita daga gate ta samu napep ta tsara ya maidata school.

______________________________

Sa'adu Zungur road,
Old GRA,Bauchi.
_14:09pm_

Wasu 'yan mata ne biyu,identical twins farare kyawawa suke guje guje a tsakar gida.

Wacce take bayan ne take cewa,"Hida,Allah idan na kamaki sai kinyi bayani.Dan rainin wayau ni zaki fauce min phone ina call."

Shahida da ita ake kira Hida kuma itake rike da phone din tace,"Wlhy gwanda ki bini asannu,inba haka bah Yah Rid na isowa na bashi wayan sai inga tafadi.Har wani saurayi kikayi Amante❤🔐 koh?zakiyi bayani wa Yah Rid."
[Amante - Lover(Spanish)]

Zuciya tayi ta juya ta koma cikin gidan da gudu tana fashewa da kuka.Nan da nan hankalin Hida ya tashi ta bita da gudu tana kwala mata kira.

Tana shiga falo ta taradda Ammi.Tsareta tayi tana tambayanta Meya samu Shuhuda.

"Wlhy Ammi ina mata wasa ne kawai naga tana kuka.Allah ban dauka zatayi fishi bah.Barin je biko."

Wuce Ammi tayi tashiga wani katon bedroom.Ammi tabisu da ido tana cewa Allah ya shirya.

Acikin bedroom in kuwa Hida na shiga taga Huda kwance a gadonta,irin gadon boarding school dinnan mai sama da kasa amma nasu na katako.Yanda taga ta kwanta a gadonta maimakon 6 by 7 din da suke kwanciya akai yasa jikinta yay sanyi.Isa wurinta tayi,ta zauna a bakin gadon tareda ajiye mata wayan a gefen kanta.Juyarda kanta dayan side in Hudah tayi.

'Hudah kiyi hakuri idan na bata miki rai.Amma naga inata tambayanki da wa kike waya but you just ignored me.And I thought kince no secrets between us sisters,amma kinada saurayi baki fada min bah.I'm sorry'

Tana tashi zata bar wajen,Hudah tayi saurin rike hannnunta.

'I'm sorry too,habibty.But nifa banda saurayi,just someone I'm crushing on.'

Hida sarkin gurmi da sauri ta zauna a gefen Hudah wacce itama tana zaune zuwa yanzu.

'Shafa min.Waye crush in?'

'Sai kin min alkawari bazaki fadawa kowa bah'

'Ohk,kasam se'
Ta fada tana kama wuyanta da thumb and index fingers in ta,daidai wurin Adam's apple.
[Kasam se - I promise (Hindi)]

'Yah Zayn'

'Oh my gosh,MTN abokin Yah Rid?Ba laifi dai guy in ya hadu.Kin iya kamu'
Hida tafada dan ita haka take kiranshi.

Haka dai suka cigaba da hirarsu,suna shiri saboda sunada class 4-6.Sukayi wa Ammi sallama akan zasu tafi school,take fada musu saidai su shiga napep amma babu mota ko daya agidan.Motan da suke zuwa school dashi kuma driver yaje dauko su Haly a Sa'adu Zungur University of Gadau, formerly known as Bauchi State University of Gadau (BASUG)Yuli Campus,kuma ba'asan yaushe zasu dawo bah.
Tsuka Hida tayi tana kunkuni ita bata taba shiga napep bah ta yaya zata shiga salon ayi kidnapping inta.

'Ai Wallahi saidai a fasa zuwa school in.Kuma Ammi ni karki kara basu car key inmu.Ai suma sunada motoci  a part insu.'
Huda tafada tareda cire hijab inta.Neman wuri sukayi suka zauna suna mayarda face mask da sunshade insu cikin backpack insu.Atare sukeyin komai,kuma shigansu iri daya sai suka zama kamar mutum daya ne da reflection insa,saboda identical twins ne wanda babu abinda ya banbanta su sai halin su saboda hatta murya da sanyin jikinsu duk iri daya ne.Babu me iya banbanta su sai Yah Rid,Ammi dakuma Abbu.Sai kuma abin mamaki Zayn ma yana banbanta su.

Suna haka sukaji horn in mota.Tashi sukayi suka saka hijabinsu akan koma waye ya dawo ya sauke su.Sunyi sallama wa Ammi kafin suka fito compound in gidan.Motoci uku ne suka shigo.Suna ganin motocin sun san Yah Rid ne ya dawo nan suka fara murna.Motan dayake ciki na tsayuwa suka karasa jikin motan.

'Oyoyo Yah Rid,sannu da hanya'Suka fada atare.

Matashin saurayi mai kimanin 26-27 years,fari kyakkyawa mai mutukar kama da twins in ne ya dago kansa yana sauke eyes dinsa
akansu.Captain Ridwan Muhammad El Bahrain kenan.
'Uhmm,thanks.Ina zakuje haka?'

'School.Yah,me doctor yace?'
Hida ta tambaya.

'Same as always.Ku shiga mu kaiku.'

Shiga sukayi,motocin sukayi reverse suka kama hanya.Suna tafe,suna tadi da yayan nasu wanda a da basu da daman yin hakan saboda kunsan sojoji da seniority and baya zama sosai.Dalilin ciwo da yaji a kafafunsa awani mission da sukaje har China,wanda shine sanadin dayasa baya iya ko tsayuwa ne yasa yayi sanyi har yake iya zama hira da kannen nasa.

Sun isa katafaren makarantan nan da aka santa a gaba dayan Nigeria harda kasashen waje ma wato Abubakar Tafawa Balewa University Bauchi (ATBU) Yelwa Campus.A dai dai Kofar Botanical Garden dake tsallaken FOS,wato Faculty of Science aka ajiye su.Dayake a New Building Upper Lecture Room (NBULR) dake cikin FOS in zasuyi lectures,akwai course mates insu da kuma 'yan facultyn wanda dayawansu freshers ne sunzo duba Test timetable da aka manna a notice board,wasu kuma physics practical registration suka zo yi, yayinda wasu kuma sun fito ne daga lectures.Kowa dai amma hankalinsa na kan motoci ukun nan kirar 2022 Mercedes-AMG GT bakake.
Ahankali Huda ta bude car doorn ta fito,Hida ma ta biyo bayanta,sannan suka juya suna waving at him.Shima waving musu yayi yace su kirashi idan sun gama.

'Wa'ennan babes in kuma daga ina?'Wani saurayi ya tambayi na gefensa.

'El Bahrain twins mana.Ai daga ganin wadannan Mercedes Benz kasan sai su.'

'Kai amma sun hadu.Ai ina following Instagram page nasu amma dake sunsa face mask ban gane su bah.'

'Mtssww,shine zunzurutun iyeyi saida convoy zasu zo school,saura securities mah'

'Daga gani Captain ne ya kawosu saboda wannan motocinsa neh'

'Nifa basa wani burgeni saboda girman kansu.Dan kawai sunga sunada kudi da kyau sai shegen fadin rai'

'Kai,suna da shine sai sa sukeyi.Ko nine haka zanyi'

Ire-iren surutun da akeyi kenan amma sukam ko ajikinsu dan sun rigada sun saba.Directly lecture room suka nufa,wasu mazan dake zaune a front seat middle row suka tashi suka basu wurin.Godiya sukayi musu kafin suka zauna.Hira suka fara tsakaninsu suna jiran zuwan Lecturer,dayake dukansu suna period.4:17pm lecturer ya shigo,dayake musulmi ne ya tsaya Asr prayer.

Vote,Comment and Follow.
Love,
_Meesty✍️

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 02 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Captain Ridwan | Very slow updateWhere stories live. Discover now