WUTA A MASAƘA 17_18

Start from the beginning
                                    

"Kai Sarkin masifa, tun daga ciki ake jiyo hargowarka, lafiya kake wa 'yata shouting haka?" Ammi ce ke maganar lokacin da ta fito daga wani ɗaki.

Ba tsammani ta kalli inda Amira take, sukai ido huɗu da juna, ko za'a naɗe ƙasa a dawo, Amira ba zata manta fuskar Ammi ba, da wasu abubuwa da suka shuɗe shekarun da suka gabata ba.

A wulaƙance ta ƙarewa Amira kallo ta kalli Imran tace "lafiya wannan fa?"

"Abba ne yace inje in taho da ita yau, a fara biki da ita"

"Saboda bikin nata ne, kokuma na ƙanwar uwatta?"

Amira ta ɗago ta kalli Ammi, ta maida kanta ta sunkunyar.

Anty Hadiza tace "Ammi, Amira ce fa ko baki ganeta bane?"

"Ke zam cewa baki ganeta ba, baki da labarin rashin jin da yawon ta zubar ɗin da takeyi, babu inda hotonunata da rashin kunyarta basu shiga ba, kawai se a ɗebo jiki a kawomin ita cikin gida, saboda me to baze yuwu ba, ba a gidan nan ba sedai wani gurin"

Hadiza tace "Haba Ammi, koma menene dalili ne ya kawota, kuma na ɗan lokacine, ana gama biki fa zata tafi"

Gaba ɗaya hankalin mutane ya dawo kansu, aka dinga bawa Ammi rashin gaskiya da nuna mata illar abunda tayi, jin mutane nata surutu ba yadda ta iya, haka ta ƙyale Amira, saboda gudun surutan mutane.

Imran ya kuma kallon Minal yace "bakiji me nace bane?"

Miƙewa Minal tayi, Imran ya kalli Amira yace "ki bita kije ta baki masauki, a baki hijjabi ki rife jikinki"

Duk da sanyi da jikin Amira yayi, hakan be hanata zumɓura baki ba, dan da ta san gidansu Imran ze kawota, da duk tunballen tsiyar da za'ayi sedai ayi ba zata yadda taje gidansu ba.

Minal tai gaba Amira tabi bayanta, suna shiga ɗakin Minal ta juyo ta gallawa Amira harara tace "ga toilet nan ki shiga, kuma ki kula karki sake kimin taɓe taɓen abunda ba shikenan ba, kuma karki min fitsari a ƙasa, kinji na gaya miki"

Amira ba tace uffan ba, dan ta san kome akayi mata Imran ne ya janyo da ya kawota gidan, dan da tana gidansu babu me mata wannan rashin mutunci haka.

A masallaci Imran ya sake haɗuwa da Khalid, suka wuce gidansu Khalid, a hanya Imran ya bashi labarin irin karɓar da Ammi tayiwa Amira.

Khalid yace "ai nasam za'ai haka, ni babbar fargabata ma suzo su san wannan maganar, akwai fa sauran rikici"

Imran yace "bari kawai, aini na zubawa sarautar Allah ido kawai, dan ban san abunyi ba"

"Ka kwantar da hankalinka, Allah ze baka mafita insha Allah"

Seda suka raba dare suna hira, Sannan Imran ya tafi gida, lokacin duk an rurrufe ko ina, kuma be haɗu da Abba ba sam balle ya gayamasa ya ɗakko Amira, dan haka kai tsaye ɗakinsa ya wuce yaje ya kwanta.

Amira kam duk a takure take, ba wanda ya kulata balle ya bata Abinci, ga gajiyar hanya data ɗebo, gashi bata san ko ina ba, Minal da ƙawayenta se wulaƙanci sukewa Amira, Minal tana gaya musu ai Amira karuwace, se wannan guda ɗayar ta farko da tace Amira tana burgeta itace bata biye musu ba.

Da daddare akazo gurin kwanciya, Minal ta kalli Amira tace "kinga, me aiki zata shigo yanzu ta kai ki inda zaki kwana, nan ɗakin zamu kwana ne nida ƙawayena, bama son takura ina fatan kin gane?"

Amira ba tace komai ba, ga kaya tana son canzawa, bata ɗakko komai nata ba, kawai Imran ya kawota ya ajiye yai tafiyarsa, taji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan takaici.

Me aikin ta shigo ɗakin ta kalli minal tace "Anty gani"

"Yawwa, dama zaki wanke min banɗakina ne bana son sharing da jagwalgwalo, kin sanni da ƙyama, kuma an shiga banɗakin But before that, ki kaita inda na gayamiki za ta kwana"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now