WUTA A MASAƘA 13_14

Start from the beginning
                                    

"Shikenan, zan san yadda za'ayi, zan tuntuɓeshi ki gaida Ihsan ɗin".

"To shikenan zataji, seda Safe"

Ihsan data shigo tun ɗazu ta tsaya tana jiran Mummy ta gama waya, ta kalleta tace "Mummy da Ammi kike waya ko?"

"Eh da ita ne har Imran ɗin ya tafi ne?"

"Eh ya tafi" ta samu Guri ta zauna Sannan ta kuma cewa "Mummy, naji kamar tana ce miki wai wannan ƙanwar tasa zata dawo gidansu ne ko?"

"Kai Ihsan, yanzu dama kasa kunne kikayi kina jin abunda nake faɗa?"

Ihsan ta girgiza kai tace "ba haka bane Mummy, Imran ya bani labarin yarinyar, sedai a duk lokacin da za'ay zancenta se inji gabana yana faɗuwa, sama bana ƙaunar maganarta, gashi Yanzu ana zancen zata dawo gidansu"

"To ke meye haɗinki da ita da zaki damu kanki akanta? Inma gidansu zata dawo da zama akanki zata zauna? Ina gidanki daban?"

"Mummy, Yarinyar cousin ɗinsa ce kuma kamar yana nuna damuwa akanta fa" tai maganar cike da karaya.

Mummy ta riƙo hannunta tace "haba Autan Mummy, tun kan ki shiga gidan Aure kin fara da karaya haka? Ki kwantar da hankalinki sekin so wata zata raɓi mijinki, kuma yarinyar da take yawon banza ina zatayi kima a idon Imran bayan gaki" tai maganar tana murmushi.

Ihsan tace "hakane Mummy, amma kin san mazan yanzu ba'a iya musu fa"

"Ke dallcan, don't put that in your mind Baby, ba ruwanki da wata kanki kawai zaki kafa, kuma Imran yana sonki sosai baze yi abunda ze saki damuwa ba"

Ihsan tai ajiyar zuciya tace "Shikenan Mummy, na dena damuwa insha Allah"

Shikuwa Imran kamar kullum sannu a hankali yake tu(insa harya shigo layinsu, wani matashine tsaye a jikin wata Mota yana danna waya, Imran ya ƙara gudun motar ya tafi yai kan matashin kamar ze bigeshi sannan yai wani wawan birki.

Matashin seda ya ja da baya, Imran ya fito daga motar yace "kai yaushe ka dira ba labari?".

Matashin yace "ban sani ba, takeni da mota dan ubanka, kayi jinyata a Asibiti, sedai kaci amarcin a nan Asibitin gurin jinyata"

Imran ya kwashe da dariya yace "kaifa ₦an iska ne wasu lokutan, to ya? Ya ake ciki ne ka diro ashe?"

"Ba dole in diro ba, tunda ka addabeni in dawo gani na dawo, ka bani uwar da zaka bani"

Imran yace "wace uwar zan baka kuwa? Kawai dama danka dawone ka tayani hidimar bikina'

"Ɗan rainin hankali, nima ina hanya na samo wata zazzafa, kuma insha Allah wuf zan da ita"

"Karma dai kayi, ka zauna kaita ruwan ido"

"Ai nayi mamakin lokacin da ka fara soyayya, har kake shirin Aure ka barni, dole in zuciya Yaseen, kamarni Khalid ace Imran ya rigani Aure, gaskiya wannan ci bayane a gareni".

Imran yai dariya yace "wai yaushe ka shigo ne?"

Khalid yace "da magaribar nan ne, nake gidanku Ammi tace min baka nan, shine naje nai Salla sekuma gaka ka dawo"

"Fatan ka dawo lafiya, ya hanya?"

"Alhamdilillah, mushiga cikin gidan se muci Abinci mucigaba da tattaunawa"

Daga nan suka shiga gidansu Khalid.

Hajiya Amira kuwa, tunda ta lalata musu ɗan wake tasa ƙafa ta bar gidan nan, ta tafi nata garari a gari da wannan magaribar, sedai duk inda ta wuce wasu na nunata, ana cewa itace wadda aka baiwa mota, wadda zata fito a videon raye raye, ita kam ko a jikinta hakan sam be dameta ba, sabgar gabanta kawai takeyi.

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now