Baba ne ya kawo wuya, yace "ke wace irin yarinya ce mara albarka haka? Ke yanzu bakiji kunyar haɗa ido damu ba ma? Kin tafi gantali babu wanda yasan inda kike? Kwana biyar Amira ba wanda yasan inda kike?"

"Wai Baba sekai ta min iƙrarin abun Kunya, haryanzu fa ba cikin shege ba ɗan dakan kuka ba ƙanjamau, ba wanda na ajiye balle aji daɗin nunawa, amma kun isheni, nifa wannan abun da kukemin ne yasa na bar gidan nan naje na sarara na dawo"

Usman ya kai mata duka, yace "Amina, maza jeki ki rufe min ƙofar gidan nan, yau sena tattaka wannan ƙaramar mara mutuncin, yadda in akace gobe ta kuma fita bazata fita ba"

Be rufe baki ba, Amira ta dafe ƙeya tai waje, aikuwa Usman ya biyo ta, bata zame ko ina ba se inda Sadiya ke zance ita da saurayinta, tana ihu tana "na shiga uku, zasu kasheni, dan Allah yayanmu kasa baki"

Ta tattake daddumar da suke kai, taje bayan saurayin ta tsaya tana cigaba da ihu, miƙewa saurayin Sadiya yayi yana faɗin lafiya kuwa?

Usman ya ƙaraso yana "Wallahi yau zaki gane kurenki, tunda ke rashin mutunci shi kika saka a gaba, zaki yabawa aya zaƙinta"

Cikin marairaicewa da karairaya, Amira ta cewa Saurayin Sadiya "Yaya dan Allah kasa baki, dukana zeyi dan Allah ka hanashi"

Baba ne ya ƙaraso inda suke shima, wanda hakan yai daidai da shigowar Zailani, Zailani yana dubawa yaga Amira yaga su Usman a tsaye cirko cirko kamar zakaru.

Yace "Wannan almirar uwar gantalin ta dawo kenan, shine daga zuwanta zata fara ɗagawa mutane hankali, tun daga waje ake jin ihunta, gidan ubanwa kika tafi?"

Saurayin Sadiya yace "dan Allah kuyi haƙuri, macece kubita a hankali karku daketa, zaku iyayi mata illa kuyi haƙuri dan Allah"

Usman yace "baka san halin wannan sheɗaniyar bane, shiyasa kake kareta"

Sadiya kam gaba ɗaya takaici ya cikata, ta rasa mema zatayi ta huce, kawai tana zaune tana tsinkar furen soyayya, wannan mahaukaciyar ta watsa komai, kuma ta zubar Mata da mutunci a gaban saurayin.

Amira kuwa kan saurayin ta kalla, ya sha uwar zanna bukar ɗinsa, kawai a ranata taga kansa ma ɗan dakon kara, ga dogon wuya kamar raƙumin dawa, ga yadin jikinsa duk ya tashi saboda tsufa, ji tayi kamar ta ƙyaƙyace da dariya, amma ta haɗiye dariyarta, saboda tasan a jazabar da take.

Yace "koma me tayi ina nema mata afuwa dan Allah, ayi haƙuri a ƙyaleta"

Suna can suna maganarsu tai cikin gidan, da sauri ta shige ɗakinsu ta banko ƙofar ta saka sakata.

Suka koma cikin gida, suna tunanin meye mafita akan Amira, dan lamarin nata sam ba sauƙi kullum ƙara taɓarɓarwa lamarunta sukeyi.

Amina taje zata shiga ɗakinsu, amma ta tarara Amira ta garƙame ƙofa da sakata, tai bugun duniya amma Amira taƙi buɗewa, tun tana bugawa harta koma magiya amma Amira tayi burus da ita.

Zailani ne yace "wai bakyaji ne? Bazaki buɗe ƙofar ba?"

Amira daga ciki tace "bazan buɗe ba, yau ni kaɗai zan kwana a ɗakin nan, kowacce ta tafi ɗakin uwarta ta kwana"

Amina tace "Ai naga ba ubankine ya gina gidan ba, danme zaki kulle ƙofa wane irin wulaƙancine wannan, dalla malama ki buɗe mana ƙofa"

"Bazan buɗe ba, kuma wallahi aka cigaba da takuramin a gidan nan, sena gangamo abunda duk zesa a haɗamu a kullemu"

Zailani yace 'anya wannan yarinyar ƙwaƙwalwarta bata fara samun matsala ba kuwa?"

Maman Amina tace "zunzurutun iya shege ne, ba wani taɓin ƙwaƙwalwa"

Amina kam tasan tunda Amira ta furta baza su kwana a ɗakin ba tasan bazasu kwanan ba, ba yadda ba'ayi ba Amira tace bazata buɗe ba.

Can Amina ta gama zancenta, ta dawo gida tana masifa "Wallahi idan Amira ta kuma shiga sabgata, sedai ayi mutuwar kasako, koni ko ita wallahi, wanne wane irin rashin mutunci ne? Tazo har kan sallayar da nake zance tana kurma ihu, ta nemi ta tattake mana ƙafafuwa, sauran ƙiris ta take masa cinya, gaba ɗaya ta zubarmin da mutunci yau, ji nayi kamar ƙasa ta tsage in shige wallahi"

WUTA A MASAƘAWhere stories live. Discover now