CHAPTER 1

610 27 0
                                    

It was a cool evening,Ina dawowa islamiyya da baby sister ta,Ranan na Fara ganinshi,dogo ne kyakkawa,kila Kuma nikadai nake ganin kyaun,Amma dai nasan yanada charisma(kwarjini) kowa zai iya ganin hakan.
   Ina kallon shi Sai Naga shima kallo na yakeyi,da sauri na dauke Ido na a kansa,Sai Kuma na Dan daga Ido na kalleshi,Naga dai still ni yake kallo bansan sanda nayi Masa murmushi ba,shima murmushin ne dauke a fuskan shi.
  From that day I met my first love,first love as they say It strikes at the most unexpected time,it introduces you to feelings you have never had before,I was Soo excited that day,naje gida cike da farin ciki a Raina Wanda Ni kaina bazan iya misaltawa ba.
  Na Isa gida na tarar da mama tana girki,munyi Mata sannu da gida,she replied sannunku da dawowa yarana ,ta tuna Mana muje muyi wanka kaman yanda kullum takeyi,aje ayi wanka wari kukeyi, kullum haka ta ke cewa in min dawo makaranta hakan yasa yin wanka in mun dawo makaranta ya zaman Mana jiki in bamuyi ba muma bamujin dadin jikin mu,mama nasan tsafta sosai Kuma tana kokarin koya Mana amfanin shi kullum.
    Sunana Asiya,shekara ta 17,duk da karancin shekara na baya Hana a ga kyaun surar da Allah yayi min,wato Kaya(wink),hakan yasa nake son sa dogon riga ko buba saboda in boye sura ta,Dan nakan ji kunyan or let's say I don't have that much confidence in my body saboda abin ne Sai dai ace tubarakallah,inada cute face ga Kuma murmushi na Wanda indai nayi nake siye zuciyar Mai kallon shi.
   Inada siblings guda 4,babban yayan mu sunan shi idris muna ce Masa Yaya khalifa ya Gama University ya karanta geography,yayi service Kuma saidai bashida aiki yanzu,ta biyun  Fatima muna ce Mata Yaya batool,tayi aure 2years ago batada yara,tana 500 level a KASU,tana karanta pharmacy,Sai siyama Yar auta tana jss 3 yanzu,shekaranta 14,Baba Kuma shi ba Mai Zama ba ne saboda yanayin aikin shi,ya kusa retire kila Zamu samu ya Dan samu lokaci sosai damu ,rayuwa na tafiya alhamdulillah,yau Dadi gobe da wuya,saidai Dadin yafi yawa.kuma munada rufin asiri alhamdulillah.
   Ina wanka Ina ganin shi a cikin Ido na,Saida na rankwashi kaina nace Asiya dawo hankalinki,Sai Kuma nayi murmushi Ni kadai,nayi alwalan magrib kafin nafito,ana Kiran sallah magrib nafito,na goge jiki na da brown towel dina sannan na sa doguwar Riga atampa,nayi sallar magrib a daki na sannan na fito parlor wurin su mama,abinci siyama ta jera plates da warmers,nan muka zauna aka zuba muka Fara ci,yawanci dinner tare muke ci da mama da siyama,watarana yaya khalifa shima Muna ci tare,yau ma taren muka ci ,baba yace cin abinci tare na Kara soyayya da shakuwa tsakanin Yan uwa.
   Ban cika magana ba,na gaji mama wurin yawan shiru shiru,Amma siyama akwai surutu ko parrot Sai haka,yanzu ma Ana cin abincin surutun takeyi,tana ba mama labarin makaranta,Yaya khalifa na tayata surutun shima,nidai na maida hankali wurin sa Loma Dan fa bana Wasa da abinci,mama da wasan ta tace madam ke yau ba wani labarin makarantar ne,dariya mukayi mu duka nace komai yatafi lafiya,mama saida  ta lura yau din duk da shiru na Amma Ina cikin farin ciki saidai bawanda yasan dalili Sai Ni kadai.mun gama cin abinci mun kwashe plates mun Kai kitchen,Sai muka dawo Muna kallo a TV anayi Ana fira,Yaya khalifa dai da laptop dinshi Yana kallon sa shima,a hakan baba ya Kira kamar yanda yasaba kullum bayan Isha,angaisa da kowa sannan na Kara tuna Mai wayata da yace zai siya,dariya yayi yace incigaba da hakuri inyadawo Zan samu,inata murna,mama na Mika ma wayan ta tafi daki sunata Hira da  baba,haka natafi daki inata murna sannan Kuma Ina tunanin shi a zuciya ta,inata murmushi nikadai,na kosa gobe tayi in Kara ganin sa kawai inji dadi ko sunan shi ma insani,a hakan dai har bacci ya kwasheni.

   Adam shekaran shi 20,he's from a rich family, Yana zuwa NDA,Yana  therma 1,yazo hutun first semester, kwana uku kenan yana lura da Asiya sanda ta ke tafiya makaranta da sanda ta ke dawowa,Amma ita Bata taba lura dashi ba Sai yau,ya ji Dadi sosai yau da ta ganshi Kuma har tayi Masa murmushi,dama plan dinshi shi ne ta lura dashi sannan Sai yayi mata magana,Ranan shima yayi bacci cike da farin ciki,ya kwanta Akan gobe zaiyi Mata magana ko number ta ya amsa kafin ya koma makaranta.
Wednesday,Asiya ta farka daga bacci me nauyin da tasha,gashi Kuma baccin yayi Mata dadi,kafin ta Mike a gado taji mama ta shigo dakin ta ta kunna wuta,Asiya lokacin sallah yayi mama tace,na amsa Mata sannan natashi nashiga toilet,nayo alwala nazo nayi sallah na,na idar nayi azkhar dina sannan na hau aikace aikace na,gyaran daki da wanke toilet,Sai Kuma wanke wanke,ita Kuma siyama aikinta shara ne,duk da rufin aisirin mu umma Bata daukan Mai aiki mu mukeyin Dan aikace aikace mu kafin mu shirya makaranta,mama dai tana hada Mana breakfast.ina Gama aikina na fada bathroom nayi wanka sannan na shirya cikin uniform Dina white shirt,da Kuma blue skirt and blue coat,Sai Kuma white baby hijab,nashirya komai tsaf nayi kyau Abu na,breakfast nafito nayi,ga pink jakata da na rataya hannu daya,na dauka water bottle Dina shima pink na zuba tea a ciki,I was looking elegant and sweet,mama ta Riga ta tashi Yaya khalifa a bacci Dan yanzu shi yake ajiye mu a makaranta da dai mama ce,Amma yanzu tunda Yaya khalifa yadawo daga NYSC shi yake kaimu,hakan ya na Yi Mana Dadi nida siyama,shidai yace Muna Hana shi bacci gashi Yan matan makarantan mu suncika kallo Baya so🤣,but why not yayan namu spec ne ai.
    Mun shiga school Ana morning assembly,Ana gamawa kowa yatafi ajinsa,kawayena biyu ne hafsa da hadiza,inaji dasu saboda mun Dade tare tun primary,da farko da ba kawayena bane,Sai da mukazo senior secondary muka Fara kawance da hafsa Sai Kuma hadiza itama muka Fara shiri,lokacin break muke samu muyi labarin mu da su,munje sch cafeteria da hadiza muka ga hafsa da saurayinta  Hassan ko a aji ma tare suke zama,suna fira suna cin abincin su,anan ne na tuna da na hanyar islamiyya,sunan Dana bashi kenan yanzu kam,murmushi nayi nikadai,coke na siya muka zauna da hadiza Ina Shan coke Dina ita Kuma tana cin abinci,Muna Yi muna labari a haka dai har break ya kare.yaya khalifa yazo ya dauke mu muka tafi gida,I was Soo eager mu Isa gida in shirya inje islamiyya,min tarar da mama ta dafa favorite Dina,fried rice da kaza,yau dai Naga alama komai na tafiya da dadi.Mama ta lura excitement Dina ya Karu,tace jiya da yau dai Naga alama garin na Miki Dadi,dariya nayi nace Mata kullum Ni haka nake mama,kallona tayi dai Bata ce komai ba,nayi Shirin makaranta cikin uniform Dina farare,komai whites,riga,hijab da wandon saidai fa yau harda powder na Dan shafa da lipgloss aikuwa Ina fitowa mama tace inje in goge shi,Ina Dan kumburo Baki naje na wanko fuskan,dariya mama tayi tace ko kefa ya ta tafi kyau a natural beauty dinta plus banso maza su kalle min ke a waje,daga zuwa islamiyya inji anata sallama a hakan ya aka Kare,mama tana nufin wani Ibrahim ne da wasu masu zuwa sallama Dani,nikuwa haushi nakeji in sukazo nema na,dariya tasani,siyama na gefe itama dariya tayi tace yes sis kinfi kyau natural dinki,hararanta nayi,a hakan dai muka Kama hanyan school.....

Please vote and comment this is my first book,let me know what you think if you have read this far.
 
 
  

NI DA YAN GIDAN MUTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon