BABI NA BIYU/SOS

278 34 9
                                    

*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪

*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*

Labarin Asiya Bamaina.
Season 2
BABI NA BIYU

Sai dai abu daya ma fahimta,matukar ina da wani abu a hannu na, toh magana ya kare zai ta bina luf luf, har sai mun gama da abin yana gamawa da shi zai dawo da halin shi.

  Dake yayi karatu kawai aikin ne Allah bai nufa ya samu ba, sai gashi cikin ikon Allah ya samu karatu zuwa kasar Turai. Nafi kowa murna, dan haka na gayawa Yan uwana, tare Allah sarki sai gashi sun hada kishi shatara na arziki sun turo min, bawan Allah nan ya amsa babu godiya, ban damu ba domin nasan matukar ya tafi karatun shin nan idan ya tashi dawowa zai dawo da abin arziki ne.

    Muna cikin wannan yanayin ne, wata juma'a sai ga mutane har cikin gidan,suna shigowa suka gama duba gidan nan suka fita, hmm mutumin nan bai gaya min gaskiyar zuwan mutanen ba. Sai da ya rage wata daya tafiyar su,. Kwatsam sai mutanen sun zo wai na bar musu gidan su mijina ya sayar da musu gidan, ban iya magana ba, haka nayi ta niman shi,babu shi babu labarin shi. Sai dare yazo da mota J5, aka kwashe min kayan zuwa cikin motar.

       Wani unguwa can ya kai ni state lowcost, anan ya kama mana haya, na san dai an kwaso kayana da idona, amma abin mamaki koda aka zo zuba kayan babu furnitures dina gado da kujeruna babu su babu labarin su, koda na mishi magana marairaice min yayi sannan yace min.
"Kiyi hakuri shekara biyu Insha ALLAH zan saya miki idan na dawo"

       Bawan Allah nan haka ya sani jin kamar bani da yancin, babu kuma yadda na iya haka na bashi ya tashi da shi,(Allah sarki Maman Khalifa, Ubangiji ya saka miki) ban kuma shan mamakin shi ba sai da ya gama abin da zai yi ya saya mana kayan abinci yayi tafiyar shi, a lokacin naji damuwa domin ya tafi ya barni babu wani gamshashen bayani. 

   A hankali muje gurgura rayuwar mu da Yarona,babu shiri na kama sana'a a cikin gidan, Allah da ikon shi dake bakin hanya muke matasa na taruwa, sai gashi nan ina cinikin taliya da miya da wake, zobo da Pure water. Alhamdulillahi Ubangiji ya dafa min domin nasan ya dubi halin da nake ciki ne ya bani damar hutawa. Ciwon kafana ne yake hanani kuzari da hanani barci tunda abu ne da ya tab'a kokon kafana.

  Haka na cigaba da tura rayuwata, babu laifi domin da zai tafi ya bar min layina. Bayan ya tafi banki yaso mai da alert dina nashi, ai kuwa bankin suka nuna mishi ko sata wayata yayi, ganin haka ya dawo min da layin babu waya a hannu na, adana layin nayi. Na cigaba da tura rayuwata da na Yarona,  haka kawai naji a raina ina son waya a hannuna, dan haka na sayi wata karamar techno, me torch ina sakawa naga sakon yan uwana da iyayena, ranar naci kuka gashi bani da katin bankin na, dakyar na samu na tafi bank nayi sabon mtn.

     Sannan na dawo gida na kira su, ina kuka rasa bakin magana domin na samu dubu kusan saba'in a cikin account ɗina,  a daddafe na shirya tare da bawa costomomina hakuri zan tafi ganin gida.

    Basu ji dadi ba, amma kuma babu yadda suka iya,domin ina zaune da mutanen kirki ne, duk da sun san mijina baya nan amma haka bai hana a kare min mutuncina ba. Kuma wani abin burgewa babu wanda ya tab'a min kallon mutuniyar banza.

    **
Lokacin da na tafi gida naga soyayya da kulawa, sannan muka tafi Kano, aka duba kafana. Wasa wasa sai da na kwashe wata uku a gida,  da zan dawo ne muka da da kanen shi domin ta can yana musu aikan kudi amma bai tab'a min koda sau daya ne.

              Da zan dawo aka min kayan abinci kamar wacce tayi sabon aure, gara sosai aka min. Duk da Kanen shi sun ga abin da na dawo dashi bai hanani guna guni ba. Ban damu da su ba, ina dawowa na cigaba da sana'a ta, duk da suna gaya mishi bai tab'a kirana ya tambaye ni ba, kawai tara ni wai yake,

GIDAN Aure Na..!!?Where stories live. Discover now