BABI NA TAKWAS.

476 62 17
                                    

https://www.wattpad.com/1144631247?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
*EWF*
GIDAN AURE NA
🎪🎪

*Ƙarƙashin jagorancin Grps guda Huɗu! masarautan Mata 1/2. SBL TSK! EXQUISITE WRITERS FORUM.... Zai cigaba da zuwa muku kullum Insha Allah*

Labarin Sameerah.
Season 1
BABI NA TAKWAS.

Shiru tayi tana kallon Yaran tare da jin wani irin kunci a ranta musamman idan ta tuna inda yake cewa.
"Baba ke uwa ce, ya zaki ji idan Yarki tazo dangin mijinta sun mata abin da kuka yiwa Sameerah?kiyi nazari da kai idan har akwai wanda zai dauki yar shi guda ya bawa Naka toh ya gama maka soyayya, amma idan kuna ganin shiga hakkin wani shine mafita toh bismillah."

Share kwalla tayi sannan tace min.
"Sameerah ki gafarce ni" kallon mamaki ya kuma kashe ni a tsaye,
"Ki yafe min wallahi mun so kan mu da yawa"
"A'a babu kome wallahi ban rike ko ba dama Gwaggo."
"A'a yarinya mutuwa ake kullum kana ganin aya rayuwarka idan baka yi karatun ta nutsuwa yaushe ka shiryawa mutuwa? Babu lokaci domin daukar nauyin wasu da kake ba zai ficce ka ba, sai abin da ka shuka."

Shiru nayi ina mamakin yadda take bani hakuri, dan haka na mike tare da mata sai da safe, domin ba zan jure kallon ta tana bani hakuri ba, yarana suka biyo bayana, muka yi alola muka shiga sallah.

Wasa wasa muka daidaita da Gwaggo,.sosai ta cire kanta da shiga sabga na, sai ma kara bani kwarin gwiwa take akan D'anta.

A bakin Yahanasu nake jin abin da ya faru da Gwaggo na tausaya mata,. amma zai ban nuna na sani ba, gudun kar haka ta hanata sukuni, shi kuma ɗan muna raka shi da addu'a. Baki daya tausayin kaina nake ji domin ina son mijina amma ya nisance ni,kuma baya jin zai dawo gare ni, dan haka abu ya hadu min goma da Ashirin.

***
Yau Asabar ban da aiki ina daura abinci,.matan gidan suka shigo ina kallona tare da sake kananun habaici sun shirya tsaf zasu tafi Kaduna.

Kallon su Gwaggo tayi tare da sake dariya tana faɗin.
"Allah ya kai ku lafiya kuce ina gaishe ta." Sai da suka fita tace min.
"Bar su, su tafi Allah ya kiyayye hanya, hmm! Ko a lahira bana fatan komawa inda wancan munafukar take domin ina ganin da ke ce zaki rabani da D'ana sai gashi Allah ya kawo wacce zata kashe ni da raina kai wancan yarinyar munafuka ce."

"Allah ya kyautatta karshen mu" na fada ina kallon ta, wato abin da ya koro Bera daga rami ya fada wuta ba karamin abu bane, shi yasa na ke kallon sauyin da gwaggo tayi ba karamin abu bane zai sauya mata ra'ayi.

Wato inda ranka babu abin da ba zaka gani ba, gashi nan dai Allah ya kawo sauyi a tare da gwaggo kuma na gani, Allah ya kyauta. Na kuma fada domin baki daya rayuwar tsoro yake bani. Wunin ranar ina tare da ita. Domin ko na dawo d'akina zata zo ta kirani naje d'akinta baki daya wani ɗauki na take kamar wacce aka kawo ta sabuwa, Allah kenan gwanin hikima, dama shi din Alhakamu ne. Kuma ya wanzar da hikimar shi.
*
Yan Kaduna har da Zaliha tun a hanya suke shan alwashin idan suka dawo daga kaduna suka samo abin duniya sai sun kafta rashin mutunci ga Samirah domin su bawai Sameerah suke cewa ba, Samira suke cewa asalin sunan kwanon da akayi jeren shi da. Kowa ya kudiri mugun aniyar shi a ranshi dangane da Sameerah, nan suna da yakinin zasu koma su kafta mata shi yadda zata ji zafin basu yi da ita sai Amaryan ta.

Abin da yake faruwa kenan a cikin society din mu, tsakani da Allah mutane suke nuna sanka a fili. A da can dake suke yi, kuma suna matukar tare dake, a lokacin da aka miki amarya lokacin zaki gane waye masoyin ki, waye makiyin ki domin ido da ido zasu juya miki baya su koma wurin Amaryan ki, sai dai idan sun ga babu fuska a can zasu dawo da guntun gulmar su, idan kuma ta basu fuska wallahi kin kaɗe har ganyen ki, domin kome kika yi yana kunnen Amaryan ki.

Abun tausayi yana ga Yan matan mu masu tasowa, wallahi kune abin tausayi, kai ba yan mata ba hatta zawarawa suma abin tausayi ne, yaushe zaki yarda da dadin bakin namiji ya kwaso miki gulmar matar shi ya gaya miki? Ko an ce miki baya kaunar matar shi ce? Duk namijin da zai kwaso jiki ya gaya miki gulmar matar shi toh abu daya zaki tambaye shi wane da kazo ka gaya min halin matar ka me yasa kake zaune da ita?

GIDAN Aure Na..!!?Where stories live. Discover now